Shishak Ya Kai wa Yahuza Yaƙi
1 Da mulkin Rehobowam ya kahu, ya kuma yi ƙarfi, sai Rehobowam da dukan Isra’ilawa tare da shi suka bar bin shari’ar Ubangiji.
2 A shekara ta biyar ta mulkin sarki Rehobowam, Isra’ilawa ba su bi Ubangiji da aminci ba, saboda haka Shishak, Sarkin Masar, ya hauro don ya yi yaƙi da Urushalima.
3 Aka faɗo masa da karusai dubu da ɗari biyu (1,200), da mahayan dawakai mutum dubu sittin (60,000). Mutanen da suka taho tare da sarki Shishak daga Masar, ba a san adadinsu ba, akwai Libiyawa, da Sukkimiyawa, da kuma Habashawa.
4 Ya ci birane masu kagara na Yahuza, har ya dangana da Urushalima.
5 Sai annabi Shemaiya ya zo wurin Rehobowam da sarakunan Yahuza waɗanda suka tattaru a Urushalima saboda Shishak, ya ce musu, “Ubangiji ya ce kun yashe shi, don haka shi ma ya bashe ku a hannun Shishak.”
6 Sai sarakunan Isra’ila tare da sarki Rehobowam, suka ƙasƙantar da kansu, suka ce, “Ubangiji mai adalci ne.”
7 Da Ubangiji ya ga sun ƙasƙantar da kansu, sai ya yi magana da Shemaiya cewa, “Tun da yake sun ƙasƙantar da kansu, to, ba zan hallaka su ba, amma zan cece su, ba zan kwararo fushina ta hannun Shishak a kan Urushalima ba.
8 Duk da haka fa, za su zama bayin Shishak don su san bautata dabam take da wadda ake yi wa mulkokin ƙasashe.”
9 Sai Shishak Sarkin Masar ya zo ya fāɗa wa Urushalima da yaƙi, ya kuwa kwashe dukiyoyin da suke cikin Haikalin Ubangiji, da na fādar sarki, ya yi musu ƙaƙaf. Ya kuma kwashe garkuwoyi na zinariya, waɗanda Sulemanu ya yi.
10 Sai sarki Rehobowam ya ƙera garkuwoyin tagulla a madadin na zinariya, ya sa su a hannun shugabannin matsara, masu tsaron gidan sarki.
11 A duk lokacin da sarki ya shiga Haikalin Ubangiji, sai matsara su kawo su, daga baya kuma su maishe su a ɗakin matsaran.
12 Da sarki Rehobowam ya ƙasƙantar da kansa, sai fushin Ubangiji ya huce, don haka bai sa aka hallaka shi ƙaƙaf ba, har ma halin zama a ƙasar Yahuza ya yi kyau.
Mulkin Rehobowam a Taƙaice
13 Sarki Rehobowam kuwa ya kafa mulkinsa sosai a Urushalima, yana da shekara arba’in da ɗaya da haihuwa ya ci sarauta, ya yi mulki shekara goma sha bakwai a Urushalima, birnin da Ubangiji ya zaɓa daga dukan kabilan Isra’ila domin ya sa sunansa a wurin. Sunan tsohuwar Rehobowam Na’ama, Ba’ammoniya.
14 Amma ya aikata mugunta domin bai nemi Ubangiji a zuciyarsa ba.
15 Ayyukan Rehobowam, daga farko har zuwa ƙarshe an rubuta su a littafin tarihin annabi Shemaiya, da na Iddo maigani. Kullum yaƙi ne tsakanin Rehobowam da Yerobowam.
16 Rehobowam fa ya rasu, aka binne shi a birnin Dawuda. Abaija ɗansa ya gāji gadon sarautarsa.