Annabcin Shemaiya
1 Sa’ad da Rehobowam ya kai Urushalima, sai ya tattara zaɓaɓɓun mayaƙa, mutum dubu ɗari da dubu tamanin (180,000) daga cikin jama’ar Yahuza da ta Biliyaminu don su yi yaƙi da Isra’ila, su komo wa Rehobowam da mulki.
2 Sai Ubangiji ya yi magana da Shemaiya, mutumin Allah, ya ce,
3 “Ka faɗa wa Rehobowam ɗan Sulemanu, Sarkin Yahuza, da dukan Isra’ilawa da suke a Yahuza da Biliyaminu, ka ce,
4 ‘Ga abin da Ubangiji ya faɗa, kada ku yi yaƙi da ‘yan’uwanku, kowa ya komo alfarwarsa, gama wannan al’amari daga gare ni yake.’ ” Suka kuwa ji maganar Ubangiji, suka koma, ba su tafi yaƙi da Yerobowam ba.
Rehobowam Ya Arzuta
5 Rehobowam ya zauna a Urushalima, ya kuwa gina birane masu kagara a Yehuza.
6 Ya gina Baitalami, da Itam, da Tekowa,
7 da Bet-zur, da Soko, da Adullam,
8 da Gat, da Maresha, da Zif,
9 da Adorayim, da Lakish, da Azeka,
10 da Zora, da Ayalon, da Hebron. Waɗannan su ne birane masu kagara a Yahuza da Biliyaminu.
11 Ya kuma ƙara ƙarfin kagaran, ya sa sarakunan yaƙi a cikinsu. Ya tara abinci, da mai, da ruwan inabi a cikinsu.
12 Ya sa garkuwoyi da māsu a cikin dukan biranen nan, ya ƙara musu ƙarfi ƙwarai. Haka ya riƙe Yahuza da Biliyaminu.
Firistoci da Lawiyawa sun Zo Yahuza
13 Firistoci da Lawiyawa da suke a dukan Isra’ila kuwa suka komo gare shi daga dukan wuraren da suke.
14 Sai Lawiyawa suka bar makiyayarsu da dukiyarsu, suka koma Yahuza da Urushalima, saboda Yerobowam da ‘ya’yansa maza sun hana su yi hidimarsu ta firistocin Ubangiji.
15 Sai Yerobowam ya naɗa firistoci don masujadansa, saboda siffofin bunsurai, da na maruƙa, waɗanda ya yi.
16 Amma su waɗanda zuciyarsu take ga Ubangiji, Allah na Isra’ila, daga kowace kabilar Isra’ila, sukan bi Lawiyawa zuwa Urushalima domin su miƙa hadaya ga Ubangiji, Allah na kakanninsu.
17 Sai suka ƙarfafa mulkin Yahuza, suka tsare mutuncin Rehobowam ɗan Sulemanu har shekara uku. Suka yi shekara uku suna tafiya a tafarkin Sulemanu.
Iyalin Rehobowam
18 Rehobowam kuwa ya auri Mahalat ‘yar Yeremot ɗan Dawuda, wadda Abihail ‘yar Eliyab ɗan Yesse ta haifa.
19 Mahalat ta haifa masa ‘ya’ya maza, su ne Yewush, da Shemariya, da Zaham.
20 Banda Mahalat kuma, sai ya auri Ma’aka ‘yar Absalom, wadda ta haifa masa Abaija, da Attai, da Ziza, da kuma Shelomit.
21 Rehobowam ya fi ƙaunar Ma’aka, ‘yar Absalom, fiye da dukan matansa, da ƙwaraƙwaransa. Yana kuwa da matan aure goma sha takwas, da ƙwaraƙwarai sittin. ‘Ya’yan da ya haifa maza ashirin da takwas ne, ‘ya’ya mata kuwa sittin.
22 Sai Rehobowam ya zaɓi Abaija ɗan Ma’aka, ya zama shugaban ‘yan’uwansa, gama nufinsa ya zama sarki.
23 Sai ya yi hikima ya rarraba waɗansu ‘ya’yansa maza ko’ina cikin gundumomin ƙasar Yahuza da ta Biliyaminu, a dukan birane masu kagara, ya tanada musu abinci a yalwace. Ya kuma samo musu mata masu yawan gaske.