Waɗansu Ayyukan Sulemanu
1 A ƙarshen shekara ashirin waɗanda Sulemanu ya yi yana gina Haikalin Ubangiji da fādarsa,
2 sa’an nan ya sāke giggina biranen da Hiram ya ba shi, ya zaunar da Isra’ilawa a cikinsu.
3 Sai Sulemanu ya tafi ya ci Hamat-zoba da yaƙi.
4 Sa’an nan ya gina Tadmor a jeji, a Hamat kuwa ya gina biranen ajiya.
5 Ya kuma gina Bet-horon ta kan tudu da Bet-horon ta kwari, birane masu kagara kuwa ya gina musu garu, da ƙofofi, da ƙyamare,
6 da kuma Ba’alat da dukan biranen ajiya waɗanda yake da su, da birane don karusansa, da birane don mahayan dawakansa, ya gina dukan abin da yake bukata a Urushalima, da Lebanon, da a dukan ƙasashen da suke cikin mulkinsa.
7 Dukan jama’ar da suka ragu a ƙasar, wato Hittiyawa, da Amoriyawa, da Ferizziyawa, da Hiwiyawa, da Yebusiyawa, waɗanda Isra’ilawa ba su hallaka ba,
8 daga cikin zuriyarsu waɗanda suka ragu a ƙasar a bayansu, waɗanda Isra’ilawa ba su hallaka ba, su ne Sulemanu ya tilasta su biya gandu, haka kuwa suke har wa yau.
9 Amma Sulemanu bai bautar da kowa daga cikin mutanen Isra’ila ba, su ne mayaƙansa, da shugabannin yaƙi, da shugabannin karusansa, da mahayan dawakansa.
10 Manyan shugabanni na sarki Sulemanu, mutum ɗari biyu ne da hamsin waɗanda suke iko da jama’a.
11 Sulemanu kuwa ya kawo ‘yar Fir’auna daga birnin Dawuda zuwa gidan da ya gina mata, gama ya ce, “Matata ba za ta zauna a gidan Dawuda, Sarkin Isra’ilawa ba, saboda duk wuraren da akwatin Ubangiji ya shiga sun tsarkaka.”
12 Sai Sulemanu ya miƙa hadayun ƙonawa ga Ubangiji a kan bagaden da ya gina wa Ubangiji a gaban shirayi.
13 Sulemanu ya yi bisa ga abin da aka wajabta a yi kowace rana, bisa ga umarnin Musa a miƙa hadayu domin ranakun Asabar, da na amaryar wata, da kuma lokatan idodi uku na shekara, wato idin abinci marar yisti, da idin makonni, da na bukkoki.
14 Bisa ga ka’idar da tsohonsa Dawuda ya tsara, sai Sulemanu ya karkasa firistoci ƙungiya ƙungiya domin su yi hidima, Lawiyawa kuma bisa ga matsayinsu na yin yabo da hidima a gaban firistoci, kamar yadda aka wajabta kowace rana. Matsaran ƙofa kuma aka karkasa su ƙungiya ƙungiya bisa ga yawan ƙofofin, gama haka Dawuda, mutumin Allah, ya umarta.
15 Firistoci da Lawiyawa kuwa, ba su kauce wa umarnin sarki a kan kowane al’amari ba, ko a kan sha’anin taskoki.
16 Haka Sulemanu ya kammala aikinsa, da aka aza harsashin gina Haikalin Ubangiji, har zuwa ran da aka gama. Haka kuwa aka kammala aikin Haikalin Ubangiji.
17 Sai Sulemanu ya tafi Eziyon-geber da Elat da suke a gaɓar teku a ƙasar Edom.
18 Hiram kuwa ya aika wa Sulemanu jiragen ruwa tare da barori waɗanda suka saba da sha’ani a teku. Sai barorin tare da barorin Sulemanu, suka tafi Ofir, suka ɗauko zinariya talanti ɗari huɗu da hamsin, suka kawo wa sarki Sulemanu.