Ƙeɓewar Haikali
1 Sa’ad da Sulemanu ya gama yin addu’arsa, sai wuta ta sauko daga sama, ta cinye hadayar ƙonawa tare da sauran hadayu, darajar Ubangiji kuma ta cika Haikalin.
2 Firistoci ba su iya shiga Haikalin Ubangiji ba saboda darajar Ubangiji ta cika Haikalin.
3 Sa’ad da dukan Isra’ilawa suka ga wuta ta sauko daga sama, ɗaukakar Ubangiji kuma na cike da Haikalin, sai suka sunkuyar da kansu ƙasa, suka yi sujada, suka yabi Ubangiji, saboda nagarinsa da madawwamiyar ƙaunarsa.
4 Sa’an nan sarki da dukan jama’a suka miƙa hadaya a gaban Ubangiji.
5 Sarki Sulemanu kuwa ya miƙa hadayar bijimai dubu ashirin da dubu biyu (22,000), da tumaki dubu ɗari da dubu ashirin (120,000). Ta haka sarki tare da dukan jama’a suka keɓe Haikalin Allah.
6 Sai firistoci suka tsaya a matsayinsu, haka kuma Lawiyawa suka tsaya a nasu matsayi riƙe da kayansu na bushe-bushe da na kaɗe-kaɗe, waɗanda sarki Dawuda ya yi domin yabon Ubangiji, gama madawwamiyar ƙaunarsa tabbatacciya ce har abada. A duk lokacin da Dawuda zai yabi Ubangiji tare da su, sai firistoci waɗanda suke daura da su su busa ƙaho, sa’an nan sai dukan Isra’ilawa su miƙe tsaye.
7 Sa’an nan Sulemanu ya tsarkake tsakiyar filin da yake a gaban Haikalin Ubangiji, gama a wurin ne ya miƙa hadayun ƙonawa da kitsen hadayu domin salama, saboda bagaden tagulla wanda Sulemanu ya yi bai iya ɗaukar hadayu domin ƙonawa, da ta gari, da ta kitse ba.
8 A wannan lokaci, Sulemanu ya yi biki a wurin har kwana bakwai, tare da dukan Isra’ilawa, da waɗanda suka zo tun daga ƙofar Hamat, har zuwa rafin Masar, taron kuwa mai girma ne ƙwarai.
9 A rana ta takwas kuwa suka yi wani muhimmin taro, domin su keɓe bagaden. Sun yi kwana bakwai suna yin bikin.
10 A ran ashirin da uku ga watan bakwai, sai sarki ya sallami jama’a su koma gidajensu, suna ta murna da farin ciki a zuciyarsu saboda alherin da Ubangiji ya nuna wa Dawuda, da Sulemanu, da kuma jama’arsa Isra’ila.
Ubangiji Ya Sāke Bayyana ga Sulemanu
11 Haka kuwa Sulemanu ya gama Haikalin Ubangiji da fādar sarki. Ya fa yi nasara cikin dukan irin abin da ya yi niyya game da Haikalin Ubangiji da fādarsa.
12 Sa’an nan Ubangiji ya bayyana ga Sulemanu da dare, ya ce masa, “Na ji addu’arka, na kuwa zaɓi wannan wuri domin kaina, domin ya zama Haikalin miƙa hadaya.
13 Har idan na kulle sammai yadda ba za a yi ruwan sama ba, ko kuma in umarci fara su cinye ƙasar, ko kuwa in aiko da annoba cikin jama’ata,
14 in jama’ata waɗanda ake kiransu da sunana za su yi tawali’u, su yi addu’a, su nemi fuskata, su juyo su bar mugayen ayyukansu, sa’an nan sai in ji su daga Sama, in gafarta zunubansu, in kuma warkar da ƙasarsu.
15 Yanzu idanuna za su kasance a buɗe, kunnuwana kuma za su saurari addu’ar da za a yi a wannan wuri.
16 Yanzu fa na riga na zaɓi wannan Haikali, na kuwa keɓe shi domin sunana ya kasance a wurin har abada. Idanuna da zuciyata kuma za su kasance a wurin kullayaumin.
17 Amma kai, idan za ka yi zamanka a gabana kamar yadda tsohonka Dawuda ya yi, ka kuma aikata bisa ga dukan abin da na umarce ka, ka kiyaye dokokina da farillaina,
18 to, zan kafa gadon sarautarka, yadda na alkawarta wa tsohonka Dawuda, cewa ba za a rasa mutumin da zai yi mulkin Isra’ila ba.
19 Amma idan ka juya, ka bar dokokina da umarnaina waɗanda na sa a gabanka, har ka shiga bautar gumaka kana musu sujada,
20 to, sai in tumɓuke ka daga ƙasata wadda na ba ka, wannan Haikali kuma wanda na riga na keɓe domin sunana, zan kawar da shi daga fuskata, zan kuwa maishe shi abin karin magana, abin raini ga dukan sauran al’umma.
21 “Haikali kuwa, wanda aka ɗaukaka, duk mai wucewa zai yi mamaki ya ce, ‘Me ya sa Ubangiji ya yi wa wannan ƙasa da wannan Haikali haka?’
22 “Sa’an nan kuma za su ce, ‘Saboda sun rabu da Ubangiji, Allah na kakanninsu, wanda ya fitar da su daga ƙasar Masar, amma suka bi waɗansu gumaka, suka yi musu sujada, suka bauta musu, saboda haka ne ya aukar musu da duk wannan bala’i.’ ”