Maganar Sulemanu ga Mutane
1 Sulemanu ya ce,
“Ubangiji ya riga ya faɗa zai zauna a cikin girgije mai duhu.
2 Yanzu kuwa na gina maka ƙasaitaccen ɗaki,
Na gina maka wurin da za ka zauna har abada.”
3 Sa’an nan sarki ya juya, ya dudduba, ya sa wa dukan taron jama’ar Isra’ila albarka, dukansu kuwa suka tsaya.
4 Sai ya ce, “Ubangiji Maɗaukaki ne, Allah na Isra’ila wanda ya yi wa tsohona Dawuda alkawari, ga shi kuwa ya cika shi, gama ya ce,
5 ‘Tun daga ranar da na fito da jama’ata daga ƙasar Masar, ban zaɓi wani birni daga cikin dukan kabilan Isra’ila ba, inda zan gina wurin da sunana zai kasance, ban kuma zaɓi wani mutum da zai shugabanci jama’ata Isra’ila ba.
6 Amma na zaɓi Urushalima domin sunana ya kasance a wurin, na kuma zaɓi Dawuda ya zama shugaban jama’ata Isra’ila.’
7 “Ya zama kuwa tsohona Dawuda ya yi niyyar gina Haikali domin sunan Ubangiji, Allah na Isra’ila.
8 Amma Ubangiji ya ce wa ubana Dawuda, ya kyauta, tun da yake ya yi niyya a zuciyarsa zai gina ɗaki saboda sunansa.
9 Duk da haka, ba shi zai gina Haikalin ba, ɗansa wanda za a haifa masa, shi ne zai gina Haikalin domin sunansa.
10 “Yanzu fa Ubangiji ya cika alkawarin da ya yi, gama na gāji matsayin ubana Dawuda, na kuwa hau gadon sarautar Isra’ila, yadda Ubangiji ya alkawarta, na kuwa gina Haikali domin sunan Ubangiji, Allah na Isra’ila.
11 A can na ajiye akwati inda aka sa alkawarin da Ubangiji ya yi wa jama’ar Isra’ila.”
Addu’ar Sulemanu
12 Sulemanu ya miƙe a gaban bagaden Ubangiji a idon dukan taron Isra’ila ya ɗaga hannuwansa.
13 Sulemanu ya riga ya yi dakali na tagulla, tsawonsa kamu biyar, fāɗinsa kamu biyar, tsayinsa kamu uku, ya ajiye shi a tsakiyar filin, ya tsaya a kai. Ya durƙusa a gwiwoyinsa, a idon dukan taron jama’ar Isra’ila, ya ɗaga hannuwansa sama,
14 ya ce, “Ya Ubangiji, Allah na Isra’ila, ba wani Allah kamarka a sama ko a duniya, wanda yake cika alkawari, kana nuna madawwamiyar ƙauna ga bayinka masu tafiya a gabanka da zuciya ɗaya.
15 Kai ka cika alkawarin da ka yi wa bawanka, tsohona Dawuda. Abin da ka faɗa ka kuma aikata.
16 Yanzu fa, ya Ubangiji, Allah na Isra’ila, ka cika alkawarin da ka yi wa bawanka tsohona cewa, ‘Daɗai, ba za a rasa wanda zai hau gadon sarautar Isra’ila ba, in dai ‘ya’yanka maza za su lura da al’amuransu, don su yi tafiya bisa ga shari’ata, yadda kai ka yi tafiya a gabana.’
17 Saboda haka, ya Ubangiji, Allah na Isra’ila, ka tabbatar da maganarka wadda ka yi wa bawanka Dawuda.
18 “Ashe kuwa Allah zai zauna tare da ɗan adam a duniya? Ga shi kuwa, sama da saman sammai ba su iya ɗaukarka ba, balle fa ɗakin da na gina.
19 Duk da haka ka kula da addu’ar bawanka da roƙe-roƙensa. Ya Ubangiji Allahna, ka kasa kunne ga kuka da addu’ar da bawanka yake yi a gabanka.
20 Ka dubi wajen Haikalin nan dare da rana, wurin da ka yi alkawari za ka sa sunanka, ka kasa kunne ga addu’ar da bawanka zai yi wajen wannan wuri,
21 ka ji roƙe-roƙen bawanka da na jama’ar Isra’ila, sa’ad da suke addu’a suna fuskantar wannan wuri, ka ji daga wurin da kake zaune a Sama, sa’ad da ka ji, ka gafarta.
22 “Idan wani ya yi wa maƙwabcinsa laifi, har aka sa shi ya rantse, ya kuwa zo ya rantse a gaban bagaden a wannan Haikali,
23 sai ka ji ka yi wa bayinka shari’a daga Sama, ka hukunta wa mugun, ka ɗora masa alhakinsa, ka baratar da adalin, ka ba shi sakayyar adalcinsa.
24 “Idan abokan gāba sun kori jama’arka, wato Isra’ila, saboda laifin da suka yi maka, sa’an nan suka juyo suka shaida sunanka, suka yi addu’a, suka yi roƙo a gabanka a wannan Haikali,
25 sai ka ji daga Sama ka gafarta zunubin jama’arka Isra’ila, ka komo da su ƙasar da ka ba su, su da kakanninsu.
26 “Sa’ad da aka kulle sammai, ba ruwan sama saboda sun yi maka zunubi, sa’an nan suka fuskanci wurin nan suka yi addu’a, suka shaida sunanka, suka juyo suka daina zunubinsu a sa’ad da ka hukunta su,
27 sai ka ji daga Sama ka gafarta zunubin bayinka, wato jama’arka Isra’ila, lokacin da ka koya musu kyakkyawar hanya da za su bi. Sai ka sa a yi ruwa a ƙasarka, wadda ka ba jama’arka gādo.
28 “Idan ana yunwa a ƙasar, ko annoba, ko burtuntuna, ko fumfuna, ko fārā, ko gamzari, ko da maƙiyansu za su kewaye biranensu da yaƙi, ko kowace irin annoba, da kowace irin cuta da take akwai,
29 kowace irin addu’a, kowane irin roƙo da kowane mutum, ko jama’ar Isra’ila suka yi, ko wannensu yana sane da irin wahalarsa, da baƙin cikinsa, ya kuwa ɗaga hannunsa wajen wannan Haikali,
30 sa’an nan za ka ji daga wurin zamanka a Sama, ka yi gafara, ka kuwa sāka wa kowa bisa ga al’amuransa, wanda ka san zuciyarsa, gama kai kaɗai ne ka san zukatan mutane,
31 don su yi tsoronka su yi tafiya bisa ga dokokinka muddin ransu, a ƙasar da ka ba kakanninmu.
32 “Haka kuma baƙo wanda ba cikin jama’arka Isra’ila yake ba, idan ya taho daga wata ƙasa mai nisa saboda girman sunanka da ƙarfin ikonka, in ya zo ya yi sujada, yana fuskantar Haikalin nan,
33 ka ji daga Sama wurin zamanka, ka kuwa aikata bisa ga dukan irin roƙon da baƙon ya yi gare ka. Domin ta haka sauran al’umman duniya za su san sunanka, su kuma yi tsoronka, yadda jama’arka Isra’ila suke yi, za su kuma sani cewa wannan Haikali da na gina, ana kiransa da sunanka.
34 “Sa’ad da jama’arka za su fita don yin yaƙi da magabtansu, duk dai ko ta ina ne za ka aike su, in sun yi addu’a gare ka, suna fuskantar wannan birni wanda kai ka zaɓa, da Haikalin nan da na gina saboda sunanka,
35 sai ka ji addu’arsu da roƙe-roƙensu daga Sama, ka biya muradinsu.
36 “Sa’ad da suka yi maka zunubi (gama ba wani ɗan adam da ba ya yin zunubi), ka kuwa yi fushi da su, har ka bashe su a hannun magabtansu, magabtansu suka kakkama su suka kai wata ƙasa ta nesa ko ta kusa,
37 duk da haka idan sun yi niyya a ransu a can ƙasar da aka kai su baƙunta, suka tuba, suka roƙe ka a can ƙasar baƙunci tasu, suna cewa, ‘Mun yi zunubi, mun aikata laifi, mun kuma yi mugunta,’
38 in sun tuba da zuciya ɗaya, a ƙasar da aka kai su, in sun fuskanci ƙasarsu wadda ka ba kakanninsu, da birnin da ka zaɓa, suka yi addu’a, suna kuma fuskantar Haikalin nan da na gina domin sunanka,
39 sai ka ji addu’arsu da roƙe-roƙensu, daga wurin zamanka a Sama, ka sa su yi nasara, ka biya musu muradinsu, ka gafarta wa jama’arka waɗanda suka yi maka zunubi.
40 “Yanzu fa, ya Allahna, ina roƙonka, ka buɗe idanunka, ka kasa kunnuwanka, ka saurari addu’ar da ake yi a wannan wuri.
41 Yanzu fa, ya Ubangiji ka tashi ka tafi wurin hutawarka, kai da akwatin ikonka. Ya Ubangiji Allah ka yi wa firistocinka sutura da cetonka, adalanka kuma su yi farin ciki da nagartarka.
42 Ya Ubangiji Allah kada ka juya baya ga keɓaɓɓenka, ka tuna da madawwamiyar ƙaunarka ga bawanka Dawuda.”