2 TAR 4

1 Ya yi bagade na tagulla, tsawonsa kamu ashirin ne, fāɗinsa kuma kamu ashirin, tsayinsa kuwa kamu goma.

2 Ya yi kwatarniya kewayayyiya ta zubi, kamu goma daga gāɓa zuwa gāɓa, tsayinsa kuwa kamu biyar ne, da’irarsa kuwa kamu talatin.

3 A ƙashiyar kwatarniya akwai siffofin bijimai kamu goma kewaye da ita har jeji biyu. Gaba ɗaya aka yi zubinsu da na kwatarniya.

4 Kwatarniya tana bisa bijimai goma sha biyu, uku suna fuskantar gabas, uku suna fuskantar yamma, uku suna fuskantar kudu, uku kuma suna fuskantar arewa. Kwatarniya tana bisa bijiman, gindin kowannensu yana daga ciki.

5 Kaurin kwatarniya taƙi guda ne, bakinsa kamar bakin finjali ne, kamar kuma siffar furen bi-rana. Kwatarniya kuwa tana iya ɗaukar fiye da garwa dubu uku na ruwa.

6 Ya kuma yi daro goma na wanki, ya ajiye biyar a wajen kudu, biyar kuma a wajen arewa, don a riƙa ɗauraye abubuwan da ake hadayar ƙonawa da su. Amma kwatarniya don firistoci su riƙa wanka a ciki ne.

7 Sa’an nan ya yi alkuki goma na zinariya kamar yadda aka tsara. Ya sa su cikin Haikali, biyar a sashen dama, biyar kuma a hagu.

8 Ya kuma yi tebur goma, ya ajiye a cikin Haikalin, biyar a dama, biyar kuma a hagu. Ya kuma yi kwanonin zinariya guda ɗari.

9 Sa’an nan ya yi wani shirayi domin firistoci, ya kuma yi wani babban shirayi, ya yi ƙofofi domin shirayun. Ya dalaye ƙyamaren ƙofofin da tagulla.

10 Ya girka kwatarniya a kusurwar kudu maso gabas daura da Haikalin.

11-16 Huram kuma ya yi tukwanen ƙarfe, da manyan cokula, da daruna. Huram kuwa ya gama dukan aikin da ya alkawarta wa sarki Sulemanu a Haikalin Allah:

ginshiƙi biyu

dajiya biyu a kan ginshiƙi biyu

siffar tukakkiyar sarƙa a kan kowane ginshiƙi

Siffar rumman guda ɗari huɗu domin raga don rufe dajiyar ginshiƙan

dakali goma

daro goma

kwatarniya

bijimi goma sha biyu da suke ɗauke da kwatarniya

kwanoni, manyan cokula masu yatsotsi, wato ya yi dukan kayan nan da tagulla domin haikalin Ubangiji

17 Sarki ya yi zubinsu a filin Urdun tsakanin Sukkot da Zaretan a wuri mai yumɓu.

18 Haka Sulemanu ya yi kayayyakin nan da yawa ƙwarai, har ba a iya lissafin yawan nauyin tagullar da aka yi amfani da ita ba.

19-22 Haka kuwa Sulemanu ya yi dukan kayayyakin nan da suke cikin Haikalin Allah, duk da zinariya tsantsa aka yi su.

bagade na zinariya

tebur don ajiye gurasar ajiyewa

alkukai tare da fitilunsu na zinariya tsantsa, domin a kunna su a gaban Wuri Mafi Tsarki na ciki kamar yadda aka tsara

furanni

fitilu

arautaki

hantsuka

daruna

cokula

farantan wuta

ƙofofi na can ciki

ƙofofi na waje