Ba Da Kyautai domin Gina Haikali
1 Sarki Dawuda fa ya yi magana da dukan taron, ya ce, “Ga shi, ɗana Sulemanu, wanda Allah ya zaɓa, shi dai saurayi ne tukuna, bai gogu da duniya ba tukuna, aikin kuwa babba ne, gama Haikali ba na mutum ba ne, amma na Ubangiji Allah ne.
2 A halin yanzu dai na riga na yi iyakacin ƙoƙarina, har na tanada waɗannan abubuwa saboda Haikalin Allahna, wato zinariya saboda kayayyakin zinariya, azurfa saboda kayayyakin azurfa, tagulla saboda kayayyakin tagulla, baƙin ƙarfe saboda kayayyakin baƙin ƙarfe, itace kuwa saboda kayayyakin itace, da duwatsu da yawa masu daraja, da masu launi iri iri.
3 Saboda kuma ƙaunar Haikalin Allahna da nake yi, shi ya sa na ba da zinariyata da azurfata domin Haikalin Allahna, banda wanda na riga na tanada saboda Haikali mai tsarki.
4 Na ba da zinariya tsantsa, talanti dubu uku (3,000), da azurfa tsantsa, talanti dubu bakwai (7,000), domin yin ado a bangon Haikalin,
5 da kuma dukan kayayyakin da masu sana’a za su yi. Yanzu fa ko akwai mai niyyar ba da sadaka ta yardar rai ga Ubangiji?”
6 Sa’an nan shugabannin gidajen kakanni, da shugabannin kabilai, da shugabanni na dubu dubu, da na ɗari ɗari, da masu lura da aikin sarki, suka bayar da yardar rai.
7 Sun ba da zinariya talanti dubu biyar (5,000), da darik dubu goma (10,000), da azurfa talanti dubu goma (10,000), da tagulla talanti goma sha takwas (18,000), da ƙarfe talanti dubu ɗari (100,000).
8 Dukan waɗanda suke da duwatsu masu daraja suka bayar da su cikin taskar Haikalin Ubangiji, ta hannun Yehiyel Bagershone.
9 Sai jama’a suka yi murna da ganin yadda suka bayar hannu sake, gama sun kawo sadakokinsu a gaban Ubangiji da zuciya ɗaya, shi sarki Dawuda kuma ya yi murna ƙwarai.
Dawuda Ya Yabi Allah
10 Dawuda ya yabi Ubangiji a gaban dukan taron, ya ce, “Ya Ubangiji Allah na kakanmu Yakubu, yabo ya tabbata gare ka har abada abadin!
11 Girma, da iko, da daraja, da nasara, da ɗaukaka duk naka ne, ya Ubangiji, gama dukan abin da yake cikin sammai da duniya naka ne. Mulki kuma naka ne, ya Ubangiji. Kai ne Maɗaukaki duka.
12 Dukan wadata da girma daga gare ka suke, kai kake mulki da dukan iko da ƙarfi. Kai ne kake da iko ka ba mutum iko da ƙarfi.
13 Yanzu ya Allahnmu, muna gode maka muna kuma yabon sunanka mai daraja.
14 “Amma wane ni ko kuma jama’ata, da za mu iya kawo sadaka mai yawa haka? Gama dukan kome daga gare ka yake. Daga cikin abin da muka karɓa daga wurinka muka ba ka.
15 Gama mu kamar baƙi ne, masu yawo a gabanka kamar kakanninmu. Kwanakinmu a duniya kamar inuwa ne, ba za mu tsere wa mutuwa ba.
16 Ya Ubangiji Allahnmu, duk wannan da muka kawo domin mu gina maka Haikali saboda sunanka mai tsarki, daga gare ka ne muka samu, duka naka ne.
17 Da yake na sani, ya Allahna, kakan gwada zuciya, kana ƙaunar gaskiya, bisa ga amincewar zuciyata, da yardar rai, na miƙa maka dukan waɗannan abubuwa. Ina murna da ganin jama’arka waɗanda suke nan a tattare, sun kawo maka sadakokinsu da yardar rai.
18 Ya Ubangiji, Allah na Ibrahim, da Ishaku, da Yakubu, kakanninmu, ka tabbatar da yardar rai ɗin nan a rayukan jama’arka, ka bi da zukatansu zuwa gare ka.
19 Ka kuma ba ɗana Sulemanu cikakkiyar zuciya, har da zai kiyaye umarnanka, da shaidunka, da dokokinka, domin ya aikata su duka, ya kuma gina Haikali wanda na riga na yi tanadi dominsa.”
Sulemanu Ya Gāji Dawuda
20 Sa’an nan Dawuda ya ce wa taro duka, “Sai ku yabi Ubangiji Allahnku yanzu.” Taron jama’a kuwa suka yabi Ubangiji Allah na kakanninsu, suka rusuna har ƙasa, suka yi wa Ubangiji sujada, suka kuma girmama sarki.
21 Kashegari sai suka miƙa wa Ubangiji hadayu, suka kuma miƙa hadayun ƙonawa ga Ubangiji, bijimai dubu ɗaya (1,000), da raguna dubu ɗaya (1,000), da ‘yan raguna dubu ɗaya (1,000), da hadayunsu na sha, da hadayu masu yawa domin Isra’ila duka.
22 Sai suka ci, suka sha, suka yi murna a gaban Ubangiji a wannan rana.
Sai suka sake shelar naɗin Sulemanu ɗan Dawuda sarki, a karo na biyu, suka shafa masa man keɓewa domin ya zama mai mulki na Ubangiji, Zadok kuwa shi ne firist.
23 Sai Sulemanu ya zauna a kan gādon sarauta na Ubangiji maimakon tsohonsa Dawuda. Ya yi nasara a cikin sarautar, Isra’ilawa dukansu suka yi masa biyayya.
24 Dukan ma’aikatan hukuma kuwa, da manyan mutane, da kuma dukan ‘ya’yan sarki Dawuda, suka yi alkawari za su yi wa sarki Sulemanu biyayya.
25 Ubangiji kuwa ya ɗaukaka Sulemanu ƙwarai da gaske a gaban dukan Isra’ilawa, ya ɗaukaka sarautarsa fiye da ta waɗanda suka riga shi sarauta a Isra’ila.
Sarautar Dawuda a Taƙaice
26 Dawuda ɗan Yesse ya yi mulki bisa dukan Isra’ila,
27 har shekara arba’in. Ya yi mulki a Hebron shekara bakwai sa’an nan ya yi mulki shekara talatin da uku a Urushalima.
28 Sa’an nan ya rasu da kyakkyawan tsufa, cike da shekaru, da arziki, da daraja. Ɗansa Sulemanu kuma ya gāji sarautarsa.
29 An fa rubuta ayyukan sarki Dawuda daga farko har ƙarshe a tarihin Sama’ila, annabi, da na annabi Natan, da na annabi Gad.
30 An rubuta labarin mulkinsa, da ikonsa, da al’amuran da suka same shi, da Isra’ilawa, da dukan mulkokin ƙasashe na kewaye.