Gaisuwa
1 Daga Bulus, manzon Almasihu Yesu da yardar Allah, tare da Timoti, ɗan’uwanmu,
2 zuwa ga tsarkaka da amintattun ‘yan’uwa cikin Almasihu da suke a Kolosi.
Alheri da salamar Allah Ubanmu su tabbata a gare ku.
Addu’ar Bulus domin Kolosiyawa Masu Bin Almasihu
3 A kullum muna gode wa Allah, Uban Ubangijinmu Yesu Almasihu, duk sa’ad da muke yi muku addu’a,
4 saboda mun ji labarin bangaskiyarku ga Almasihu Yesu, da kuma ƙaunar da kuke yi wa dukan tsarkaka,
5 saboda bege ga abin da aka tanadar muku a sama. Kun riga kun ji labarin wannan a maganar gaskiya,
6 wato, bisharar da ta zo muku, kamar yadda ta zo wa duniya duka, tana hayayyafa, tana kuma ƙara yaɗuwa, kamar yadda take yi a tsakaninku tun daga ranar da kuka ji, kuka kuma fahimci alherin Allah na hakika.
7 Haka ma kuka koya wurin Abafaras, ƙaunataccen abokin bautarmu. Shi amintaccen mai hidima ne na Almasihu a madadinmu,
8 ya kuma sanasshe mu ƙaunar da kuke yi cikin Ruhu.
9 Shi ya sa tun a ran da muka ji labarin, ba mu fāsa yi muku addu’a ba, muna roƙo a cika ku da sanin nufin Allah da matuƙar hikima da fahimta na ruhu,
10 domin ku yi zaman da ya cancanci bautar Ubangiji, kuna faranta masa ta kowane fanni, kuna ba da amfani a kowane aiki nagari, kuna ƙaruwa da sanin Allah.
11 Allah yă dai ƙarfafa ku da matuƙar ƙarfi bisa ga ƙarfin ɗaukakarsa, domin ku jure matuƙa a game da haƙuri da farin ciki,
12 kuna gode wa Uba, wanda ya maishe mu mu isa samun rabo cikin gādon tsarkakan da suke a cikin haske.
13 Ya tsamo mu daga mulkin duhu, ya maishe mu ga mulkin ƙaunataccen Ɗansa,
14 wanda ta gare shi ne muka sami fansa, wato, gafarar zunubanmu.
Cikar Allah
15 Shi ne surar Allah marar ganuwa, magāji ne tun ba a halicci kome ba,
16 don ta gare shi ne aka halicci dukkan kome, abubuwan da suke a sama da abubuwan da suke a ƙasa, masu ganuwa da marasa ganuwa, ko kursiyai, ko masu mulki, ko masarauta, ko masu iko, wato, dukkan abubuwa an halicce su ne ta wurinsa, shi ne kuma makomarsu.
17 Shi ne a gaba da dukkan abubuwa, dukkan abubuwa kuma shi ne yake riƙe da su.
18 Shi ne kai ga jikin nan, wato Ikilisiya. Shi ne tushe, na farko a cikin masu tashi daga matattu, domin ta wurin kowane abu ya zama shi ne mafifici.
19 A gare shi dukkan cikar Allah ta tabbata, domin Allah yana farin ciki da haka,
20 da nufin ta wurinsa, Allah yă sulhunta dukkan abubuwa da shi kansa, na ƙasa ko na sama, yana ƙulla zumunci ta wurin jininsa na gicciye.
21 Ku kuma dā a rabe kuke da Allah, maƙiyansa a zuci, masu mugun aiki.
22 Amma a yanzu ya sulhunta ku ta hanyar jikinsa na mutuntaka, wato, ta wurin mutuwarsa, domin ya miƙa ku tsarkakakku, marasa aibu, marasa abin zargi kuma a gabansa.
23 Sai dai fa ku nace wa bangaskiya, zaunannu, kafaffu, ba tare da wata ƙaura daga begen nan na bishara wadda kuka ji ba, wadda aka yi wa dukkan talikan da suke a duniya, wadda kuma ni Bulus na zama mai hidimarta.
Hidimar Bulus zuwa ga Ikilisiya
24 To, a yanzu ina farin ciki saboda wuyar da nake sha dominku, a jikina kuma ina cikasa abin da ya saura ga wahalar Almasihu, da aka aza mini saboda jikinsa, wato Ikilisiya,
25 wadda na zama mai hidimarta bisa ga aikin nan da Allah ya ba ni amana saboda ku, domin in sanar da Maganar Allah sosai,
26 wato, asirin nan da yake a ɓoye tun zamanai masu yawa, amma a yanzu an bayyana shi ga tsarkakansa.
27 Su ne Allah ya so ya sanar da yadda irin yalwar ɗaukakar asirin nan take a cikin al’ummai, asirin nan kuwa shi ne Almasihu a cikinku, begen ɗaukakar da za a bayyana.
28 Shi ne kuwa muke sanarwa, muna yi wa kowane mutum gargaɗi, muna kuma koya wa kowane mutum da matuƙar hikima, da nufin mu miƙa kowane mutum cikakke a cikin Almasihu.
29 Saboda wannan nake shan wahala, nake fama da matuƙar himma, wadda yake sa mini ta ƙarfin ikonsa.