Alkawarin da Allah Ya Yi wa Dawuda
1 Sa’ad da Dawuda yake zaune a fādarsa, sai ya ce, wa annabi Natan, “Ga shi, ni ina zaune a cikin gidan da aka yi da itacen al’ul, amma akwatin alkawarin Ubangiji yana cikin alfarwa.”
2 Natan ya amsa masa ya ce, “Ka yi duk abin da zuciyarka ta ɗauka, gama Allah yana tare da kai.”
3 Amma a wannan dare Ubangiji ya yi magana da Natan, ya ce,
4 “Ka tafi, ka faɗa wa bawana, Dawuda, cewa ni Ubangiji na ce, ‘Ba za ka gina mini ɗakin da zan zauna a ciki ba.
5 Gama tun ranar da na fito da Isra’ilawa ban taɓa zama a cikin ɗaki ba, amma daga alfarwa zuwa alfarwa, daga wannan mazauni kuma zuwa wancan.
6 A dukan wuraren da na tafi tare da Isra’ilawa, ban taɓa faɗa wa wani daga cikin hakiman Isra’ila, waɗanda na ba da umarni su yi kiwon jama’ata, cewa su gina mini ɗaki da itacen al’ul ba.’
7 “Saboda haka fa sai ka faɗa wa bawana Dawuda cewa, ‘Ni Ubangiji Mai Runduna, na ɗauko ka daga kiwon tumaki domin ka zama sarkin jama’ata Isra’ila.
8 Na kuwa kasance tare da kai a duk inda ka tafi, na kuma hallaka maƙiyanka a gabanka. Zan sa ka shahara kamar waɗanda suka shahara a duniya.
9 Zan zaɓo wa jama’ata, wato Isra’ila, wuri, zan dasa su, su zauna a wuri na kansu, don kada a sāke damunsu, kada kuma masu mugunta su ƙara lalata su kamar dā,
10 tun lokacin da na sa hakimai su shugabanci jama’ata Isra’ila. Zan rinjayi dukan maƙiyanka. Banda wannan kuma na yi alkawari zan ci dukan maƙiyanka, in mallakar da su ga zuriyarka.
11 Sa’ad da lokacinka ya yi da za ka mutu, zan ta da ɗaya daga cikin zuriyarka, ɗaya daga cikin ‘ya’yanka maza, zan kafa mulkinsa.
12 Shi ne zai gina mini Haikali, zan kafa gadon sarautarsa har abada.
13 Ni zan zama uba a gare shi, shi kuwa ya zama ɗa a gare ni, ba zan kawar masa da madawwamiyar ƙaunata ba, kamar yadda na kawar da ita daga wanda ya riga ka sarauta.
14 Zan zauna da shi a gidana da mulkina har abada. Gadon sarautarsa kuwa zai kahu har abada.’ ”
15 Natan kuwa ya faɗa wa Dawuda dukan abin da Allah ya bayyana masa.
Addu’ar Dawuda ta Godiya
16 Sarki Dawuda kuwa ya shiga alfarwa, ya zauna a gaban Ubangiji ya ce, “Wane ne ni, ya Ubangiji Allah, mene kuma gidana da za ka yi mini haka?
17 Amma wannan ƙanƙanen abu ne a gare ka, ya Allah. Ka kuma yi alkawari, cewa za ka tsawaita kwanakin zuriyar bawanka, ka ɗauke ni kamar ni wani babban mutum ne, ya Ubangiji Allah.
18 Me kuma ni Dawuda zan ƙara ce maka, a kan girman da ka ba bawanka? Gama ka san bawanka.
19 Ya Ubangiji, saboda bawanka ne, da kuma bisa ga yardar ranka, ka aikata wannan babban al’amari, domin ka bayyana waɗannan manyan abubuwa.
20 Ya Ubangiji, ba wani kamarka, ba kuma wani Allah sai kai, bisa ga duk abin da muka ji da kunnuwanmu.
21 Wace al’umma ce take a duniyar nan kamar jama’arka, Isra’ila, wadda kai, Allah, ka je ka fanshe ta, ta zama jama’arka, domin ka yi suna ta wurin manyan abubuwa masu banmamaki, kamar yadda ka kori al’ummai a gaban jama’arka, wadda ka fansa daga Masar?
22 Gama ka mai da jama’ar Isra’ila ta zama taka har abada. Kai kuma, ya Ubangiji, ka zama Allahnsu.
23 “Yanzu dai, ya Ubangiji, bari maganar da ka yi wa bawanka da gidansa ta tabbata har abada, ka kuma aikata yadda ka faɗa.
24 Bari sunanka ya kahu, ya ɗaukaka har abada, a riƙa cewa, ‘Ubangiji Mai Runduna, shi ne Allah na Isra’ilawa.’ Gidan bawanka Dawuda kuma ya kahu a gabanka.
25 Gama kai, ya Allahna, ka riga ka bayyana wa bawanka, cewa za ka sa zuriyata su zama sarakuna, don haka ne, ni bawanka na sami ƙarfin halin yin wannan addu’a gare ka.
26 Yanzu dai ya Ubangiji, kai Allah ne, ka riga ka yi alkawarin wannan kyakkyawan abu gare ni, bawanka.
27 Ina roƙonka, ka sa wa gidan bawanka albarka, domin ya dawwama a gabanka, gama ya Ubangiji, abin da ka sa wa albarka, ya albarkatu ke nan har abada.”