Zuriyar Ra’ubainu
1 Ra’ubainu shi ne ɗan farin Isra’ila, amma saboda ya ƙazantar da gadon mahaifinsa aka ba ‘ya’yan Yusufu, maza, ɗan Isra’ila, gādonsa na ɗan fari. Don haka ba a lasafta shi a kan matsayin ɗan fari ba.
2 Ko da yake Yahuza ya rinjayi ‘yan’uwansa, har daga gare shi aka sami shugaba, duk da haka matsayin ɗan farin na Yusufu ne.
3 ‘Ya’yan Ra’ubainu, maza, wato ɗan farin Isra’ila, su ne Hanok, da Fallu, da Hesruna, da Karmi.
4 ‘Ya’yan Yowel, maza, su ne Shemaiya, da Gog, da Shimai,
5 da Mika, da Rewaiya, da Ba’al,
6 da Biyera wanda Tiglat-filesar Sarkin Assuriya ya kai bauta. Shi ne shugaban Ra’ubainawa.
7 Danginsa bisa ga iyalansu da asalinsu a zamaninsu, su ne sarki Yehiyel, da Zakariya,
8 da Bela ɗan Azaz, wato jīkan Shema, ɗan Yowel, wanda ya zauna a Arower har zuwa Nebo da Ba’al-meyon.
9 Ya kuma zauna wajen gabas, har zuwa goshin jejin da yake wajen Kogin Yufiretis, saboda shanunsu sun ƙaru a ƙasar Gileyad.
10 Zuriyar Ra’ubainu suka yi yaƙi da Hagarawa a kwanakin Saul. Suka ci Hagarawa, saboda haka suka zauna a ƙasar da take gabashin Gileyad.
Zuriyar Gad
11 ‘Ya’yan Gad, maza, suka zauna a ƙasar Bashan, daura da Ra’ubainawa har zuwa Salka.
12 Yowel ne sarki, Shafam kuwa shi ne na biyun, da Yanai, da Shafat, su ne tushen Bashan.
13 Danginsu bisa ga gidajen kakanninsu, su ne Maikel, da Meshullam, da Sheba, da Yorai, da Jakan, da Ziya, da Eber, su bakwai ke nan.
14 Waɗannan su ne ‘ya’ya maza na Abihail ɗan Huri. Ga yadda kakanninsu suke, wato Abihail, ɗan Huri ɗan Yarowa, ɗan Gileyad, ɗan Maikel, ɗan Yeshishai, ɗan Yado, ɗan Buz.
15 Ahi ɗan Abdiyel, wato jīkan Guni, shi ne shugaban gidan kakanninsu.
16 Suka zauna a Gileyad, da Bashan, da garuruwanta, da dukan iyakar makiyayar Sharon.
17 (An rubuta waɗannan duka bisa ga asalinsu a zamanin Yotam, Sarkin Yahuza, da Yerobowam Sarkin Isra’ila.)
Tarihin Kabilai Biyu da Rabi
18 ‘Ya’yan Ra’ubainu, maza, da Gadawa, da rabin kabilar Manassa suna da jarumawa masu riƙon garkuwa da takobi, masu harbi kuma da baka. Gwanayen yaƙi ne, su dubu arba’in da huɗu, da ɗari bakwai da sittin ne (44,760).
19 Suka yi yaƙi da Hagarawa, da Yetur, da Nafish, da Nodab.
20 Aka taimake su yin yaƙi da abokan gābansu, sai aka ba da Hagarawa da duk waɗanda suke tare da su a hannunsu, saboda suka yi roƙo ga Allah a cikin yaƙin, Allah kuwa ya amsa musu roƙonsu saboda sun dogara gare shi.
21 Sai suka kwashe dabbobinsu, raƙuma dubu hamsin (50,000), da tumaki dubu ɗari biyu da dubu hamsin (250,000), da jakuna dubu biyu (2,000), da kuma mutane dubu ɗari (100,000).
22 Aka karkashe mutane da yawa, domin yaƙin na Allah ne. Sai suka gāje wurin zamansu, har lokacin da aka kai su bauta.
23 Mutanen rabin kabilar Manassa suna da yawa, sun zauna a ƙasar, daga Bashan har zuwa Ba’al-harmon, da Senir, da Dutsen Harmon.
24 Waɗannan su ne shugabannin gidajen kakanninsu, Efer, da Ishi, da Eliyel, da Azriyel, da Irmiya, da Hodawiya, da Yadiyel. Su jarumawa ne na gaske, masu suna, su ne shugabannin gidajen kakanninsu.
25 Amma mutanen suka yi rashin gaskiya ga Allah na kakanninsu, suka bi gumakan mutanen ƙasar, waɗanda Allah ya hallaka a gabansu.
26 Don haka Allah na Isra’ila ya zuga Ful, Sarkin Assuriya, wato Tiglat-filesar, ya zo ya kwashe su, ya kai su bauta, wato su Ra’ubainawa, da Gadawa, da rabin kabilar Manassa. Ya kai su Hala, da Habor, da Hara, har zuwa kogin Gozan, can suke har yau.