Zuriyar Yahuza
1 ‘Ya’yan Yahuza, maza, su ne Feresa, da Hesruna, da Karmi, da Hur, da Shobal.
2 Rewaiya ɗan Shobal, shi ne mahaifin Yahat. Yahat shi ya haifi Ahumai, da Lahad. Waɗannan su ne iyalin Zoratiyawa.
3 Waɗannan kuma su ne ‘ya’yan Itam, Yezreyel, da Ishma, da Idbasha, da ‘ya ɗaya, ita ce Hazzelelfoni.
4 Feniyel shi ne mahaifin Gedor, Ezer kuwa shi ne mahaifin Husha. Waɗannan su ne ‘ya’yan Hur, maza, wato ɗan farin Efrata, zuriyarsa ne suka kafa Baitalami.
5 Ashur, wanda ya kafa Tekowa, yana da mata biyu, su ne Hela, da Nayara.
6 Nayara ta haifa masa Ahuzzam, da Hefer, da Temeni, da Hayahashtari. Waɗannan su ne ‘ya’yan Nayara, maza.
7 ‘Ya’yan Hela, maza, su ne Zeret, da Izhara, da Etnan.
8 Hakkoz shi ne mahaifin Anub, da Zobeba, shi ne kuma kakan iyalin da suka fito daga zuriyar Aharhel ɗan Harum.
9 Yabez ya fi sauran ‘yan’uwansa kwarjini saboda haka mahaifiyarsa ta sa masa suna Yabez, wato da wahala ta haife shi.
10 Yabez ya roƙi Allah na Isra’ila, ya ce, “Ka sa mini albarka, ka faɗaɗa kan iyakata, hannunka kuma ya kasance tare da ni, ka kuma kiyaye ni daga abin da zai cuce ni.” Allah kuwa ya biya masa bukatarsa.
11 Kalibu ɗan’uwan Shuwa, shi ne mahaifin Mehir wanda ya haifi Eshton.
12 Eshton kuwa shi ne ya haifi Bet-rafa, da Faseya, da Tehinna wanda ya kafa birnin Ir-nahash, zuriyar waɗannan mutane kuwa su suka zauna a Reka.
13 ‘Ya’yan Kenaz, maza, su ne Otniyel da Seraiya. Yana kuma da waɗansu ‘ya’ya maza, su ne Hatata da Meyonotai.
14 Meyonotai kuwa shi ne mahaifin Ofra.
Seraiya shi ne ya haifi Yowab, Yowab ya kafa kwarin Ge-harashim, saboda su masu sana’a ne.
15 ‘Ya’yan Kalibu, maza, ɗan Yefunne, su ne Airu, da Ila, da Na’am. Ila shi ya haifi Kenaz.
16 ‘Ya’yan Yehallelel, maza, su ne Zif, da Zifa, da Tiriya, da Asarel.
17-18 ‘Ya’yan Ezra, maza, su ne Yeter, da Mered, da Efer, da Yalon. Bitiya ‘yar Fir’auna, wadda Mered ya aura, ta haifi waɗannan, Maryamu, da Shammai, da Ishaba wanda ya haifi Eshtemowa. Mered kuma ya auri wata daga kabilar Yahuza, ta haifi Yered wanda ya kafa garin Gedor. Eber kuma ya kafa garin Soko, Yekutiyel kuwa ya kafa garin Zanowa.
19 ‘Ya’ya maza na matar Hodiya ‘yar’uwar Naham, su ne suka zama kakannin Kaila, Bagarme, da Eshtemowa da suke zaune a Ma’aka.
20 ‘Ya’yan Shimon, maza, su ne Amnon, da Rinna, da Ben-hanan, da Tilon.
‘Ya’yan Ishi, maza kuwa, su ne Zohet da Ben-zohet.
21 ‘Ya’yan Shela, maza, ɗan Yahuza, su ne Er wanda ya kafa garin Leka, da La’ada wanda ya kafa garin Maresha, da iyalan gidan masu aikin lilin da suke zaune a Bet-ashbeya,
22 da Yokim, da mutanen da suke zaune a Kozeba, da Yowash, da Saraf, waɗanda suka yi sarauta a Mowab, sa’an nan suka zauna a Baitalami. (Waɗannan labaru na tun dā ne.)
23 Su ne maginan tukwane, waɗanda suke zaune a Netayim da Gedera. Sun zauna tare da sarki don su yi masa aiki.
Zuriyar Saminu
24 ‘Ya’yan Saminu, maza, su ne Yemuwel, da Yamin, da Yakin, da Zohar, da Shawul,
25 da Shallum ɗansa, da Mibsam jīkansa, da Mishma jīkan ɗansa.
26 ‘Ya’yan Mishma, maza, su ne Hammuwel, da Zakkur, da Shimai.
27 Shimai yana da ‘ya’ya maza goma sha shida, da ‘ya’ya mata shida, amma ‘yan’uwansa ba su da ‘ya’ya da yawa kamarsa. Iyalin Saminu ba su kai yawan na Yahuza ba.
28 Suka zauna a waɗannan garuruwa, wato Biyer-sheba, da Molada, da Hazar-shuwal,
29 da Bilha, da Ezem, da Eltola,
30 da Betuwel, da Horma, da Ziklag,
31 da Bet-markabot, da Hazarsusa, da Bet-biri, da Shayarim. Waɗannan su ne biranensu tun kafin Dawuda ya yi sarauta.
32-33 Sun kuwa zauna a waɗansu wurare guda biyar, wato Itam, da Ayin, da Rimmon, da Token, da Ashan, da ƙauyukan da suke kewaye, har zuwa kudu maso gabas da garin Ba’al: Ga lissafin iyalansu da wuraren da suka zauna.
34-37 Meshobab, da Yamlek, da Yosha ɗan Amaziya,
Yowel, da Yehu ɗan Yoshibiya, wato jīkan Seraiya, ɗan Asiyel,
Eliyehoyenai, da Ya’akoba, da Yeshohaya, da Asaya, da Adiyel, da Yesimiyel, da Benaiya,
Ziza ɗan Shifi, wato jīkan Allon, zuriyar Yedaiya, da Shimri ɗan Shemaiya.
38 Waɗannan da aka jera sunayensu, su ne shugabannin iyalansu da gidajen kakanninsu.
Sun ƙaru ƙwarai.
39 Suka yi tafiya har zuwa mashigin Gedor, zuwa gabashin kwarin don nemar wa garkunansu makiyaya.
40 A can suka sami makiyaya mai kyau mai dausayi. Ƙasar kuwa tana da faɗi, babu fitina, sai salama, gama mazaunan wurin a dā Hamawa ne.
41 Waɗannan da aka lasafta sunayensu, su ne suka zo a kwanakin Hezekiya Sarkin Yahuza, suka fāɗa wa alfarwai da bukkoki waɗanda suka tarar a can, suka hallaka su sarai, sa’an nan suka maye wurinsu saboda akwai makiyaya domin garkunansu a wurin.
42 Waɗansu daga cikinsu, mutum ɗari biyar daga zuriyar Saminu, suka tafi wajen gabashin Edom. Waɗanda suka shugabance su kuwa, su ne ‘ya’yan Ishi, wato Felatiya, da Neyariya, da Refaya, da Uzziyel.
43 A can suka karkashe sauran Amalekawan da suka ragu, sa’an nan suka zauna a can har wa yau.