1 A shekara ta tara ta sarautar Zadakiya a kan rana ta goma ga watan goma, sai Nebukadnezzar Sarkin Babila, tare da sojojinsa, ya kawo wa Urushalima yaƙi. Suka kewaye ta da yaƙi, suka gina mata kagarai.
2 Aka kewaye birnin da yaƙi har shekara ta goma sha ɗaya ta sarautar Zadakiya.
3 A kan rana ta tara ga watan huɗu, yunwa ta tsananta a birnin gama ba abinci domin mutanen ƙasar.
4 Sai aka huda garun birnin, sarki da mayaƙa suka tsere da dare ta hanyar ƙofar da take tsakanin bango biyu kusa da gonar sarki, suka bi ta hanyar Araba, ko da yake Kaldiyawa suna kewaye da birnin.
5 Amma sojojin Kaldiyawa suka runtumi sarki suka kamo shi a filayen Yariko. Sojojinsa duka suka watse, suka bar shi.
6 Da suka kama sarkin, sai suka kawo shi wurin Sarkin Babila a Ribla, inda aka yanke masa hukunci.
7 Aka kashe ‘ya’yansa maza a idonsa, sa’an nan aka ƙwaƙule masa idanu, aka kuma ɗaure shi da sarƙa, aka kai shi Babila.
Cin Yahuza
8 A shekara ta goma sha tara ta sarautar Nebukadnezzar Sarkin Babila, a rana ta bakwai ga watan biyar, sai Nebuzaradan, mashawarcin sarki, shugaban sojojinsa kuma, ya shiga Urushalima.
9 Ya ƙone Haikalin Ubangiji, da gidan sarki, da dukan gidajen urushalima. Ya ƙone kowane babban gida.
10 Dukan sojojin Kaldiyawa waɗanda suke tare da shugaban, suka rushe garun da yake kewaye da Urushalima.
11 Sai Nebuzaradan shugaban sojojin, ya kwashe sauran mutanen da suka ragu a birnin, da waɗanda suka gudu zuwa wurin Sarkin Babila, da sauran da suka ragu, ya kwashe ya kai su zaman talala.
12 Amma shugaban sojojin ya bar matalautan ƙasar su zama masu gyaran inabi, da masu noma.
13 Sai Kaldiyawa suka farfasa ginshiƙan tagulla, da dakalansu, da kwatarniyar ruwa na tagullar da take cikin Haikalin Ubangiji. Suka kwashe tagullar zuwa Babila.
14 Suka kuma kwashe tukwanen ƙarfe, da manyan cokula, da hantsuka, da cokula, da tasoshin tagulla da ake amfani da su don hidimar Haikali.
15 Suka kuma kwashe farantan wuta da daruna. Duk abin da yake na zinariya da azurfa, shugaban sojojin ya kwashe.
16 Tagullar da Sulemanu ya yi abubuwan nan da su, wato ginshiƙai biyu, da kwatarniya, da dakalai, ta fi ƙarfin a auna.
17 Tsayin kowane ginshiƙi kamu goma sha takwas ne. A kan kowane ginshiƙi akwai dajiyar tagulla, wadda tsayinta ya kai kamu uku. Akwai raga da rumman na tagulla kewaye da dajiyar.
An Kwashe Mutanen Yahuza zuwa Babila
18 Nebuzaradan kuma ya tafi da Seraiya babban firist, da Zafaniya wanda yake biye da babban firist, da mutum uku masu tsaron ƙofa.
19 Daga cikin birnin kuma ya tafi da wani shugaban sojoji, da ‘yan majalisar sarki mutum biyar, da magatakardan shugaban sojoji wanda ya tattara jama’ar ƙasar, da mutum sittin na ƙasar waɗanda aka samu a birnin.
20 Nebuzaradan shugaban sojoji ya kai su wurin Sarkin Babila a Ribla ta ƙasar Hamat.
21 Sarkin Babila kuwa ya kashe su a can.
Haka aka kai mutanen Yahuza zuwa zaman talala.
Gedaliya Gwamnan Yahuza
22 A kan sauran waɗanda suka ragu a ƙasar Yahuza, waɗanda Sarkin Babila, Nebukadnezzar, ya bari, ya naɗa musu Gedaliya ɗan Ahikam, wato jikan Shafan, ya zama hakiminsu.
23 Sa’ad da shugabannin mayaƙa su da mayaƙansu suka ji Sarkin Babila ya naɗa Gedaliya ya zama hakimi, sai suka zo tare da mutanensu wurin Gedaliya a Mizfa, wato su Isma’ilu ɗan Netaniya, da Yohenan ɗan Kareya, da Seraiya ɗan Tanhumet, mutumin Netofa, da Yazaniya mutumin Ma’aka.
24 Sai Gedaliya ya rantse musu, su da mutanensu, cewa kada su ji tsoron barorin Kaldiyawa, su zauna a ƙasar, su bauta wa Sarkin Babila, haka zai fi zamar musu alheri.
25 Amma a watan bakwai, sai Isma’ilu ɗan Netaniya, wato jikan Elishama, daga gidan sarauta, ya zo tare da mutum goma ya fāda wa Gedaliya, ya kashe shi tare da Yahudawa da Kaldiyawa da suke tare da shi a Mizfa.
26 Sai dukan mutane, manya da ƙanana, da shugabannin mayaƙa, suka tashi, suka gudu zuwa Masar, gama sun ji tsoron Kaldiyawa.
An fitar da Yekoniya daga Kurkuku
27 A rana ta ashirin da bakwai ga watan goma sha biyu, a shekara ta talatin da bakwai ta ɗaurin Yekoniya Sarkin Yahuda, sai Ewil-merodak da ya zama Sarkin Babila ya yi wa Yekoniya alheri, ya sake shi a shekarar da ya ci sarautar.
28 Ya yi masa magana mai kyau, ya kuma ba shi matsayi fiye da sarakunan da suke tare da shi a Babila.
29 Sai Yekoniya ya tuɓe tufafinsa na kurkuku. Kowace rana kuwa yakan ci abinci a teburin sarki har muddin ransa.
30 Sarki kuma ya yanka masa kuɗin da za a dinga ba shi, kowace rana muddin ransa.