1 A zamanin Yehoyakim ne Nebukadnezzar Sarkin Babila ya kawo wa Yahuza yaƙi, Yehoyakim kuwa ya zama baransa har shekara uku daga nan kuma ya tayar masa.
2 Ubangiji kuwa ya sa ƙungiyar maharar Kaldiyawa, da ta Suriyawa, da ta Mowabawa, da ta Ammonawa su yi gāba da Yahuza, su hallaka su bisa ga maganar Ubangiji, wadda ya faɗa wa bayinsa annabawa.
3 Hakika haka ya faru ga Yahuza bisa ga umarnin Ubangiji domin a kawar da su daga gaban Ubangiji saboda dukan zunubin Manassa da ya aikata,
4 saboda kuma marasa laifi waɗanda ya kashe, gama ya cika Urushalima da jinin marasa laifi, Ubangiji kuwa ba zai gafarta wa Manassa ba.
5 Sauran ayyukan Yehoyakim da dukan abin da ya yi an rubuta su a littafin tarihin sarakunan Yahuza.
6 Yehoyakim ya rasu. Ɗansa Yekoniya ya gāji gadon sarautarsa.
7 Sarkin Masar kuma bai sāke fitowa daga Masar ba, gama Sarkin Babila ya ƙwace dukan ƙasar da take ta Sarkin Masar, tun daga rafin Masar har zuwa Kogin Yufiretis.
An Kama Sarki Yekoniya da Manya na Yahuza
8 Yekoniya yana da shekara goma sha takwas sa’ad da ya ci sarauta. Ya yi mulki wata uku a Urushalima. Sunan tsohuwarsa Nehushta ‘yar Elnatan, mutumin Urushalima.
9 Ya aikata mugunta a gaban Ubangiji kamar yadda tsohonsa ya yi.
10 A zamaninsa ne sojojin Nebukadnezzar Sarkin Babila suka zo Urushalima, suka kewaye ta da yaƙi.
11 Nebukadnezzar ya zo birnin lokacin da sojojinsa suka kewaye birnin da yaƙi.
12 Sai Yekoniya Sarkin Yahuza ya ba da kansa ga Sarkin Babila shi da tsohuwarsa, da fādawansa da hakimansa. Sarkin Babila ya kama shi yana da shekara takwas da sarautar,
13 ya kuma kwashe dukan dukiyar da take cikin Haikalin Ubangiji, da dukiyar da take cikin gidan sarki. Sai ya farfashe tasoshin zinariya da suke cikin Haikalin Ubangiji, waɗanda Sulemanu Sarkin Isra’ila, ya yi. Ya aikata abin da Ubangiji ya riga ya faɗa.
14 Nebukadnezzar ya kwashe dukan mutanen Urushalima, da dukan hakimai da dukan jarumawa, da masu sana’a, da maƙera, har sun kai dubu goma (10,000). Ba wanda ya ragu sai dai matalautan ƙasar.
15 Ya tafi da Yekoniya a Babila, shi da tsohuwarsa, da fādawansa, da masu maƙami na ƙasar.
16 Sarkin Babila ya kai kamammu Babila, wato jarumawa dubu bakwai (7,000), masu sana’a da maƙera dubu ɗaya (1,000), dukansu ƙarfafa ne, sun isa zuwa yaƙi.
17 Sai Nebukadnezzar, Sarkin Babila, ya naɗa Mattaniya ɗan’uwan tsohon Yekoniya sarki a maimakon Yekoniya sa’an nan ya ba shi suna Zadakiya.
Sarki Zadakiya na Yahuza
18 Zadakiya yana da shekara ashirin da ɗaya sa’ad da ya ci sarauta. Ya yi mulki a Urushalima shekara goma sha ɗaya. Sunan tsohuwarsa Hamutal, ‘yar Irmiya, mutumin Libna.
19 Ya aikata mugunta a gaban Ubangiji kamar yadda Yehoyakim ya yi.
20 Ubangiji kuwa ya husata ƙwarai da mutanen Urushalima da dukan mutanen Yahuza, sai ya kore su daga gabansa.
Faɗuwar Urushalima
Zadakiya kuwa ya tayar wa Sarkin Babila.