Gyare-gyaren da Yosiya Ya Yi
1 Sarki Yosiya kuwa ya aika, aka tattaro masa dukan dattawan Yahuza da na Urushalima.
2 Sa’an nan ya haura zuwa Haikalin Ubangiji tare da dukan jama’ar Yahuza, da dukan mazaunan Urushalima, da firistoci, da annabawa, da jama’a duka, ƙanana da manya. Sai ya karanta musu dukan maganar littafin alkawarin da aka iske a Haikalin Ubangiji.
3 Sarki ya tsaya kusa da ginshiƙi ya yi alkawari ga Ubangiji, cewa zai bi Ubangiji da zuciya ɗaya, da dukan ransa. Zai kiyaye umarnansa, da farillansa, da dokokinsa, ya bi maganar alkawarin da aka rubuta a littafin. Dukan jama’a kuma suka yi alkawarin.
4 Sa’an nan sarki Yosiya ya umarci Hilkiya, babban firist, da firistoci masu daraja ta biyu, da masu tsaron ƙofa, su fitar da tasoshin da aka yi wa Ba’al, da Ashtoret, da dukan taurarin sama, daga cikin Haikalin Ubangiji. Sai ya ƙone su a bayan Urushalima a saurar Kidron, sa’an nan ya kwashe tokarsu zuwa Betel.
5 Ya kuma tuɓe firistocin gumaka waɗanda sarakunan Yahuza suka naɗa domin su ƙona turare a matsafai na kan tuddai a garuruwan Yahuza, da kewayen Urushalima, da firistoci waɗanda suka ƙona turare ga Ba’al, da rana, da wata, da taurari, da dukan rundunan sama.
6 Sai sarki ya fitar da gunkiyan nan Ashtoret, daga cikin Haikalin Ubangiji a Urushalima, ya kai Kidron, ya ƙone ta a ƙoramar Kidron, ta zama toka, ya kuwa watsar da tokar a makabarta.
7 Ya rurrushe ɗakunan karuwai mata da maza da suke a Haikalin Ubangiji, wato wurin da mata suke saƙa labulan gunkiyar.
8 Ya fitar da dukan firistoci daga cikin garuruwan Yahuza, sa’an nan ya lalatar da matsafai na kan tuddai inda firistoci suka ƙona turare, tun daga Geba har zuwa Biyer-sheba. Ya kuma rurrushe matsafai na kan tuddai waɗanda suke a ƙofofin shiga ƙofar Joshuwa, hakimin birnin, waɗanda suke hagu da ƙofar birnin.
9 Duk da haka firistoci matsafai na kan tuddai ba su haura zuwa bagaden Ubangiji a Urushalima ba, amma suka ci abinci marar yisti tare da ‘yan’uwansu.
10 Ya kuma lalatar da Tofet, wurin da yake kwarin ‘ya’yan Hinnom, don kada kowa ya ƙara miƙa ɗansa ko ‘yarsa hadaya ta ƙonawa ga Molek.
11 Ya kawar da dawakan da sarakunan Yahuza suka keɓe wa rana, a ƙofar Haikalin Ubangiji, kusa da shirayin Natan-melek shugaban shirayin da yake cikin farfajiya. Haka kuma ya ƙone karusai waɗanda aka yi wa rana.
12 Ya rurrushe, ya kuma farfasa bagaden da yake bisa rufin benen Ahaz, waɗanda sarakunan Yahuza suka gina, da kuma bagaden da Manassa ya gina a farfajiya biyu ta Haikalin Ubangiji. Sai ya watsar da tokar da ƙurar a rafin Kidron.
13 Ya kuma lalatar da matsafai na kan tuddan da suke gabashin Urushalima, kudu da Dutsen Hallaka, waɗanda Sulemanu Sarkin Isra’ila, ya gina wa Ashtoret gunkiyar Sidoniyawa, da Kemosh gunkin Mowab, da Milkom gunkin Ammonawa.
14 Ya rurrushe ginshiƙai, ya sassare siffofin gumakan, sa’an nan ya rufe wurarensu da ƙasusuwan mutane.
15 Yosiya ya kuma rushe bagaden da yake a Betel, wanda Yerobowam ɗan Nebat ya gina, wanda ya sa mutanen Isra’ila su yi zunubi, tare da tudun, ya farfashe duwatsun, ya niƙe su, sun zama gari, ya kuma ƙone Ashtoret.
16 Da Yosiya ya waiwaya, sai ya ga kaburbura a kan dutse. Ya aika a kwaso ƙasusuwan da suke cikin kaburburan, sai ya ƙone su a bisa bagaden, ya lalatar da shi kamar yadda Ubangiji ya faɗa ta bakin annabi.
17 Ya kuma ce, “Kabarin wane ne wancan da nake gani?”
Sai mutanen Betel suka ce masa, “Ai,kabarin annabin Allah ne wanda ya fito daga Yahuza ya yi annabcin waɗannan abubuwan da ka aikata gāba da bagaden Betel.”
18 Sarki kuwa ya ce, “A bar shi yadda yake, kada wani ya taɓa ƙasusuwansa.”
Sai suka bar ƙasusuwan annabin da ya zo daga Samariya.
19 Dukan matsafai na kan tuddai da suke a garuruwan Samariya waɗanda sarakunan Isra’ila suka gina, har suka sa Ubangiji ya yi fushi, Yosiya ya watsar da su. Ya yi da su kamar yadda ya yi a Betel.
20 Ya kuma karkashe dukan firistocin matsafai na kan tuddai a bisa bagadan da suke can. Ya ƙone ƙasusuwansu a bisa bagadan. Sa’an nan ya komo Urushalima.
An Kiyaye Idin Ƙetarewa
21 Sarki Yosiya kuwa ya umarci dukan mutane, ya ce, “Ku kiyaye Idin Ƙetarewa ga Ubangiji Allahnku kamar yadda aka rubuta a littafin alkawari.”
22 Gama ba a ƙara kiyaye Idin Ƙetarewa ba tun daga zamanin hakimai waɗanda suka yi hukuncin Isra’ila, ko a zamanin sarakunan Isra’ila da na Yahuza,
23 sai dai a shekara ta goma sha takwas ta sarautar sarki Yosiya an kiyaye Idin Ƙetarewa ɗin nan ga Ubangiji a Urushalima.
Yosiya Ya Yi Sāke-sāke
24 Yosiya kuma ya kori dukan masu mabiya, da masu maita, da kawunan gidaje, da gumaka, da dukan abubuwa masu banƙyama da ake gani a ƙasar Yahuza, da a Urushalima, don ya sa maganar dokokin da aka rubuta a littafin da Hilkiya firist ya tarar a Haikalin Ubangiji ta kahu.
25 A gabansa, ko bayansa ba wani sarki kamarsa, wanda ya juyo ga Ubangiji da zuciya ɗaya da dukan ransa, da dukan ƙarfinsa domin ya bi dukan dokokin Musa.
Fushin Ubangiji a kan Yahuza
26 Duk da haka Ubangiji bai huce daga fushinsa mai zafi da yake yi da jama’ar Yahuza ba, saboda yawan tsokanar da Manassa ya yi masa.
27 Ubangiji kuwa ya ce, “Zan kawar da jama’ar Yahuza daga gabana kamar yadda na kawar da jama’ar Isra’ila. Zan yi watsi da birnin nan da na zaɓa, wato Urushalima, da Haikalin da na ce sunana zai kasance a wurin.”
Rasuwar Yosiya
28 Sauran ayyukan Yosiya da dukan abin da ya yi, an rubuta su a littafin tarihin sarakunan Yahuza.
29 A zamaninsa Fir’auna-neko, Sarkin Masar, ya tafi ya tasar wa Sarkin Assuriya da yaƙi a Kogin Yufiretis. Sarki Yosiya kuwa ya yi ƙoƙari ya hana shi wucewa, sa’ad da Fir’auna-neko ya gan shi, sai ya kashe shi a filin yaƙi a Magiddo.
30 Fādawansa kuwa suka ɗauko gawarsa a karusa daga Magiddo, suka kawo Urushalima, suka binne a kabarinsa.
Sai jama’ar ƙasa suka naɗa Yehowahaz ɗan Yosiya sarki a matsayin tsohonsa.
Sarki Yehowahaz na Yahuza
31 Yehowahaz yana da shekara ashirin da uku sa’ad da ya ci sarauta. Ya yi mulki wata uku a Urushalima. Sunan tsohuwarsa Hamutal ‘yar Irmiya na Libna.
32 Ya aikata mugunta a gaban Ubangiji kamar yadda kakanninsa suka yi.
33 Fir’auna-neko ya sa shi a kurkuku a Ribla a ƙasar Hamat, don kada ya yi mulki a Urushalima. Ya kuma sa ƙasar ta riƙa ba da gandu, wato haraji, talanti ɗari na azurfa da talanti guda na zinariya.
34 Sai Fir’auna-neko ya sarautar da Eliyakim ɗan Yosiya a matsayin tsohonsa. Ya sāke masa suna ya sa masa suna Yehoyakim. Ya ɗauki Yehowahaz ya tafi da shi Masar, can ya mutu.
35 Yehoyakim yakan ba Fir’auna azurfa da zinariya, ya kuwa sa wa ƙasar haraji don ya sami kuɗin da Fir’auna ya umarta. Ya tilasta wa kowa ya biya azurfa da zinariya bisa ga yadda ya sa masa don ya ba Fir’auna-neko.
Sarki Yehoyakim na Yahuza
36 Yehoyakim yana da shekara ashirin da biyar sa’ad da ya ci sarauta. Ya yi mulki shekara goma sha ɗaya a Urushalima. Sunan tsohuwarsa kuwa Zebida, ‘yar Fediya mutumin Ruma.
37 Ya aikata mugunta a gaban Ubangiji kamar yadda dukan kakanninsa suka yi.