An Ceci Yahuza daga Sennakerib
1 Da sarki Hezekiya ya ji wannan magana, sai ya kyakketa tufafinsa, ya sa rigar makoki, sa’an nan ya shiga Haikalin Ubangiji.
2 Sai ya aiki Eliyakim wakilin gidan sarki, da Shebna magatakarda, da manyan firistoci, saye da tufafin makoki zuwa wurin annabi Ishaya, ɗan Amoz,
3 su ce masa, “Hezekiya ya ce, yau ranar wahala ce, da ta cin mutunci, da ta shan kunya, ga shi, ‘ya’ya suna gab da a haife su, amma ba ƙarfin da za a yi yunƙuri a haife su.
4 Mai yiwuwa ne Ubangiji Allahnka ya ji dukan maganganun da Rabshake ya yi wanda ubangidansa, Sarkin Assuriya, ya aiko don yi wa Allah mai rai ba’a. Bari Ubangiji Allahnka ya hukunta masa saboda maganganunsa, sai ka yi addu’a saboda sauran da suka ragu.”
5 Sa’ad da fādawan sarki Hezekiya suka iso wurin Ishaya,
6 sai ya aike da amsa, ya ce musu, “Ku faɗa wa ubangidanku, Ubangiji ya ce, ‘Kada ka ji tsoron maganganun da ka ji daga bakin barorin Sarkin Assuriya, waɗanda suka saɓe ni.
7 Ga shi, zan sa wani ruhu a cikinsa da zai ji jita-jita, har ya koma ƙasarsa, zan sa a kashe shi da takobi a ƙasarsa.’ ”
8 Rabshake kuwa ya koma, ya tarar Sarkin Assuriya yana yaƙi da Libna, gama ya ji labari sarki ya riga ya bar Lakish.
9 Da sarki ya ji labari Tirhaka, Sarkin Habasha, ya fito don ya yi yaƙi da shi, sai ya sāke aikar manzanni wurin Hezekiya, ya ce,
10 “Ku faɗa wa Hezekiya Sarkin Yahuza, kada ya yarda Allahnsa wanda yake dogara gare shi ya yaudare shi da yi masa alkawari, cewa Sarkin Assuriya ba zai ci Urushalima ba.
11 Ya ji abin da Sarkin Assuriya ya yi wa dukan ƙasashe yadda ya hallaka su sarai. To, shi zai kuɓuta?
12 Allolin al’ummai sun cece su ne? Wato al’umman da kakannina suka hallaka, wato Gozan, da Haran, da Rezef, da mutanen Eden da suke Telassar.
13 Ina Sarkin Hamat, da Sarkin Arfad, da sarkin birnin Sefarwayim, da Sarkin Hena, da Sarkin Iwwa?”
14 Hezekiya ya karɓi wasiƙa daga hannun manzannin ya karanta ta, sa’an nan ya shiga Haikalin Ubangiji, ya buɗe ta, ya ajiye ta a gaban Ubangiji.
15 Sa’an nan ya yi addu’a ga Ubangiji ya ce, “Ya Ubangiji Allah na Isra’ila, kai da kake zaune a kan gadon sarautarka, kai kaɗai ne Allah a dukan mulkokin duniya, kai ne ka yi sama da ƙasa.
16 Ka kasa kunne, ya Ubangiji, ka yi. Ka buɗe idanunka, ya Ubangiji, ka gani, ka kuma ji irin maganar Sennakerib wadda ya aiko don a yi wa Allah mai rai ba’a.
17 A gaskiya kam, ya Ubangiji, sarakunan Assuriya sun lalatar da al’ummai da ƙasashensu.
18 Sun jefar da gumakansu cikin wuta, gama su ba Allah ba ne, amma ayyukan hannuwan mutane ne, waɗanda aka yi da itace da dutse, saboda haka an iya a hallaka su.
19 Yanzu ya Ubangiji Allahnmu, ina roƙonka ka cece mu daga hannunsa domin dukan mulkokin duniya su sani kai kaɗai ne Allah, ya Ubangiji.”
20 Sa’an nan Ishaya, ɗan Amoz, ya aika wa Hezekiya cewa, “Ubangiji Allah na Isra’ila ya ji addu’arka, ya kuma amsa.”
21 Ubangiji ya ce, “Birnin Urushalima ya yi maka dariya, kai Sennakerib, yana yi maka ba’a.
22 Wa kake tsammani ka yi wa ba’a har da zagi? Ba ka ga girmana ba, ni Allah Mai Tsarki na Isra’ila?
23 Ka aiki manzanninka su nuna mini girmankai saboda ka ci duwatsu mafi tsayi da karusanka, har ma ka ci duwatsun Lebanon. Ka yi fariyar a kan ka datse itatuwan al’ul mafi tsayi da na fir, har kuma ka shiga har can tsakiyar kurmi.
24 Ka yi fariya a kan gina rijiyoyi, ka sha ruwan baƙuwar ƙasa, ƙafafun sojojinka kuma sun tattake Kogin Nilu, ya ƙafe.
25 “Ba ka taɓa ji ba, cewa na ƙaddara wannan tun dā? Abin da yake faruwa yanzu, na shirya shi tun tuni, yadda za ka mai da birane masu garu su zama kufai.
26 Mazauna cikinsu suka rasa ƙarfi, suka damu, suka ruɗe. Suka zama kamar ciyawar saura, ko kuma ciyawar da ta tsiro a rufin soro, da iskar gabas mai zafi ta busa, har ta bushe.
27 “Na san zamanka, da fitarka, da shigowarka, da fushin da kake yi da ni.
28 Na ji irin fushinka da girmankanka, yanzu kuwa zan sa ƙugiya a hancinka, linzami kuma a bakinka, in komar da kai baya, ta hanyar da ka biyo.”
29 Sa’an nan Ishaya ya ce wa sarki Hezekiya, “Wannan zai zama alama a gare ka. A wannan shekara za ku ci gyauro, a shekara ta biyu za ku ci gyauron gyauron, a shekara ta uku kuwa za ku shuka ku girbe, ku dasa inabi a gonakin inabi, ku ci ‘ya’yansu.
30 Ringin mutanen gidan Yahuza za su yi saiwa a ƙasa, sa’an nan su ba da ‘ya’ya a sama.
31 Gama daga Urushalima ringi zai fito, daga Dutsen Sihiyona kuma waɗanda suka tsira za su fito. Kishin Ubangiji ne zai yi wannan.”
32 Saboda haka Ubangiji ya ce, “Sarkin Assuriya ba zai zo birnin ba, ko ya harba kibiya, ko ya zo kusa da shi da garkuwa, ko ya tsiba masa tudu.
33 Zai koma ta hanyar da ya zo. Ba zai shiga wannan birni ba.
34 Gama zan tsare wannan birni, in cece shi don kaina, da kuma don bawana Dawuda.”
35 A daren nan, sai mala’ikan Ubangiji ya tafi ya kashe Assuriyawa a sansaninsu, mutum dubu ɗari da dubu tamanin da dubu biyar (185,000). Sa’ad da mutanen Isra’ila suka tashi da sassafe, sai suka ga gawawwakin nan kwance.
36 Sennakerib Sarkin Assuriya, kuwa ya tashi, ya koma gida, ya zauna a Nineba.
37 Sa’ad da yake yin sujada a haikalin gunkinsa Nisrok, sai ‘ya’yansa, Adrammelek da Sharezer, suka kashe shi da takobi, sa’an nan suka tsere zuwa ƙasar Ararat. Sai ɗansa guda, wato Esar-haddon ya gāji gadon sarautarsa.