1 A shekara ta bakwai ta sarautar Yehu, Yowash ya ci sarautar. Ya yi shekara arba’in yana sarauta a Urushalima. Sunan tsohuwarsa Zibiya ta Biyer-sheba.
2 Yowash kuwa ya yi abin da yake daidai ga Ubangiji dukan kwanakinsa, domin Yehoyaka, firist, ya koya masa.
3 Duk da haka ba a kawar da wuraren yin tsafi a tuddai ba, mutane suka ci gaba da miƙa hadayu da ƙona turare a kan tuddan.
4 Yowash ya ce wa firistoci, “Dukan kuɗin tsarkakan abubuwa da ake kawowa a Haikalin ubangiji, da kuɗin da aka tsara wa kowane mutum, da kuɗin da aka bayar da yardar rai, da ake kawowa a Haikali,
5 sai ku karɓa daga junanku, don a gyara duk inda ake bukatar gyara a Haikalin.”
6 Amma har a shekara ta ashirin da uku ta sarautar sarki Yowash, firistocin ba su yi wani gyara a Haikalin ba.
7 Saboda haka Yowash ya kirawo Yehoyada, firist, da sauran firistoci, ya ce musu, “Me ya sa ba ku gyara Haikalin? Daga yanzu kada ku karɓi kuɗi daga wurin abokanku, sai in za ku ba da shi domin gyaran Haikalin.”
8 Firistocin kuwa suka yarda, ba za su karɓi kuɗi daga wurin jama’a ba, ba su kuwa gyara Haikalin ba.
9 Sa’an nan Yehoyada, firist, ya ɗauki akwati, ya huda rami a murfin, sa’an nan ya ajiye shi kusa da bagade a sashin dama na shiga Haikalin Ubangiji. Firistocin da suke tsaron ƙofar suka saka dukan kuɗin da aka kawo a Haikalin Ubangiji.
10 Sa’ad da suka gani akwai kuɗi da yawa a cikin akwatin, sai magatakardan sarki, da babban firist suka zo, suka ƙirga kuɗin da yake a Haikalin Ubangiji suka ƙunsa shi a babbar jaka.
11 Sa’an nan suka ba da kuɗin da aka ƙirga a hannun waɗanda suke lura da aikin Haikalin Ubangiji, domin su biya masassaƙan katakai, da masu haɗawa da suke aikin Haikalin Ubangiji,
12 da masu gini, da masu sassaƙa duwatsu, a kuma sayi katako da sassaƙaƙƙun duwatsu don gyaran Haikalin Ubangiji, da kowane irin abu da ake bukata domin gyaran Haikalin.
13 Amma ba a mori kuɗin da aka kawo a Haikalin Ubangiji domin yin kwanonin azurfa, da abin katse fitila, da tasoshi, da ƙahoni, da kwanonin zinariya ko na azurfa ba.
14 Gama an ba da kuɗin ga ma’aikatan da suke gyaran Haikalin ubangiji.
15 Ba a nemi lissafin kuɗin a wurin mutanen da aka ba su kuɗin don su biya ma’aikatan ba, gama su amintattu ne.
16 Ba a kawo kuɗi na hadaya don laifi da hadaya don zunubi a cikin Haikalin Ubangiji ba, ya zama na firistoci.
17 Hazayel Sarkin Suriya kuwa ya tafi ya yi yaƙi da Gat har ya cinye ta, ya kuma shirya zai yi yaƙi da Urushalima.
18 Sai Yowash Sarkin Yahuza ya kwashe dukan kyautai na yardar rai waɗanda Yehoshafat, da Yoram, da Ahaziya, kakanninsa, sarakunan Yahuza suka keɓe, ya kuma kwashe kyauta ta yardar rai ta kansa, da dukan zinariya da aka samu a baitulmalin Haikalin Ubangiji da baitulmalin gidan sarki, ya aika wa Hazayel, Sarkin Suriya. Sa’an nan Hazayel ya tashi ya bar Urushalima.
19 Sauran ayyukan Yowash da dukan abin da ya yi, an rubuta su a littafin tarihin sarakunan Yahuza.
20 Fādawansa suka ƙulla maƙarƙashiya, suka kashe shi a gidan da yake Millo, a kan hanyar da ta nufi Silla.
21 Yozakar ɗan Shimeyat, da Yehozabad ɗan Shemer su ne fādawansa da suka kashe shi. Aka binne shi a makabartar kakanninsa cikin birnin Dawuda. Amaziya ɗansa ya gāji sarautarsa.