Sarauniya Ataliya ta Yahuza
1 Sa’ad da Ataliya, uwar Ahaziya, ta ga ɗanta ya rasu, sai ta tashi ta hallaka dukan ‘ya’yan sarauta.
2 Amma Yehosheba ‘yar sarki Yoram, ‘yar’uwar Ahaziya, ta ɗauki Yowash ɗan Ahaziya daga cikin ‘ya’yan sarki waɗanda aka kashe, ta ɓoye shi da mai renonsa, an yi ta renonsa cikin ɗaki. Da haka ta tserar da shi daga Ataliya, har ba a kashe shi ba.
3 Ya zauna tare da ita shekara shida a ɓoye, a cikin Haikalin Ubangiji sa’ad da Ataliya take mulkin ƙasar.
Yehoyada Ya Tayar
4 A shekara ta bakwai sai Yehoyada ya aika ya kawo shugabannin Keretiyawa da na masu tsaro a Haikalin Ubangiji. Ya yi alkawari da su, ya sa suka yi rantsuwa a Haikalin Ubangiji, sa’an nan ya nuna musu ɗan sarki.
5 Ya kuma umarce su cewa, “Abin da za ku yi ke nan, sai sulusinku da sukan zo aiki a ranar Asabar, su yi tsaron gidan sarki.
6 Sulusinku kuma zai kasance a ƙofar Sur. Ɗaya sulusin kuma zai kasance a bayan masu tsaro, haka za ku yi tsaron gidan, ku tsare shi.
7 Ƙungiyarku biyu kuma waɗanda sukan tashi aiki ran Asabar, za su yi tsaron Haikalin Ubangiji da kuma sarki.
8 Za ku kewaye sarki, kowane mutum ya riƙe makaminsa. Duk wanda ya yi ƙoƙari ya zo kusa, sai a kashe shi. Sai ku kasance tare da sarki duk lokacin da zai fita da duk lokacin da zai shiga.”
9 Shugabannin fa suka aikata bisa ga dukan abin da Yehoyada firist ya umarta. Kowa ya zo duk da mutanensa waɗanda za su huta aiki ran Asabar tare da waɗanda za su yi aiki ran Asabar, suka zo wurin Yehoyada.
10 Firist kuwa ya ba shugabannin māsu da garkuwoyin Dawuda waɗanda suke cikin Haikalin Ubangiji.
11 Matsara suka tsaya, kowa da makaminsa a hannu, daga wajen kudu na Haikalin zuwa wajen arewa. Suka kewaye bagade da Haikali.
12 Sa’an nan ya fito da ɗan sarki, ya sa kambin sarauta a kansa, ya kuma ba shi dokokin. Suka naɗa shi, suka zuba masa man naɗawa, sa’an nan suka yi tāfi suna cewa, “Ran sarki ya daɗe.”
13 Da Ataliya ta ji muryoyin matsara da na jama’a, sai ta zo wurin mutane a Haikalin Ubangiji.
14 Da ta duba, sai ta ga sarki a tsaye kusa da ginshiƙi bisa ga al’ada, shugabanni da masu busa kuwa suna tsaye kusa da sarki. Dukan mutanen ƙasar suna ta murna suna ta busa ƙaho. Sai Ataliya ta kece tufafinta, ta yi ihu, tana cewa, “Tawaye, tawaye!”
15 Yehoyada, firist kuwa, ya umarci shugabannin sojoji, ya ce, “Ku fitar da ita daga nan, duk kuma wanda yake son kāre ta, ku sa takobi ku kashe shi.” Ya kuma ce, “Kada a kashe ta a Haikalin Ubangiji.”
16 Suka kama ta, suka fitar da ita ta ƙofar dawakai zuwa gidan sarki, can suka kashe ta.
Gyare-gyaren Yehoyada
17 Yehoyada kuwa ya yi alkawari tsakanin Ubangiji, da sarki, da jama’a, yadda za su zama jama’ar Ubangiji. Ya kuma yi alkawari tsakanin sarki da jama’a.
18 Sai dukan jama’ar ƙasa suka tafi haikalin Ba’al suka farfashe shi, da bagadensa da siffofinsa. Suka kuma kashe Mattan firist na Ba’al a gaban bagaden.
Yehoyada kuwa ya sa matsara su yi tsaron Haikalin Ubangiji,
19 ya kuma sa shugabanni, da Keretiyawa, da matsara, da dukan jama’ar ƙasar, su fito da sarki daga Haikalin Ubangiji, suka rufa masa baya ta ƙofar matsara zuwa gidan sarki. Suka sa shi a gadon sarautar sarakuna.
20 Dukan jama’ar ƙasar suka yi farin ciki. Birnin kuwa ya huta bayan da an kashe Ataliya a gidan sarki.
Sarki Yowash na Yahuza
21 Jowash yana da shekara bakwai sa’ad da ya ci sarauta.