An Kashe Zuriyar Ahab
1 Ahab yana da ‘ya’ya maza saba’in a Samariya, sai Yehu ya rubuta wasiƙu, ya aika zuwa Samariya wurin shugabanni da dattawan birni, da masu lura da ‘ya’yan Ahab.
2 Ya ce, “Yanzu dai, da zarar wasiƙun nan sun iso wurinku, da yake kuke lura da ‘ya’yan Ahab, kuna kuma da karusai, da dawakai, da kagara, da makamai,
3 sai ku zaɓi wanda ya fi dacewa duka daga cikin ‘ya’yan Ahab, ku naɗa shi sarki, ku yi yaƙi, domin ku tsare gidan Ahab.”
4 Amma suka ji tsoro ƙwarai, suka ce, “Ga shi, sarakuna biyu ba su iya karawa da shi ba, balle mu.”
5 Sai wakilin gidan, da wakilin birnin, da dattawa, da masu lura da ‘ya’yan sarki, suka aika wurin Yehu suka ce, “Mu barorinka ne, duk abin da ka umarce mu, za mu yi. Ba za mu naɗa wani sarki ba, sai ka yi duk abin da ka ga ya yi maka kyau.”
6 Sa’an nan Yehu ya rubuta musu wasiƙa ta biyu, ya ce, “Idan kuna goyon bayana, idan kuma kun shirya za ku yi mini biyayya, to, sai ku fille kawunan ‘ya’yan Ahab, sa’an nan ku zo wurina a Yezreyel gobe war haka.”
‘Ya’yan sarki, maza, su saba’in ne, suna a hannun manyan mutanen birni ne waɗanda suke lura da su.
7 Da wasiƙar ta iso wurinsu, sai suka kwashi ‘ya’yan sarki guda saba’in, suka karkashe su. Suka sa kawunansu cikin kwanduna, suka aika wa Yehu a Yezreyel.
8 Da aka faɗa masa cewa an kawo kawunan ‘ya’yan sarki, sai ya ce, “Ku ajiye su kashi biyu a ƙofar garin har safiya.”
9 Da safe, sa’ad da ya fita, ya tsaya, sai ya ce wa mutane duka, “Ba ku da laifi, ni ne na tayar wa maigidana har na kashe shi, amma wane ne ya kashe dukan waɗannan?
10 Ku sani fa ba maganar da Ubangiji ya faɗa a kan gidan Ahab da ba za ta cika ba, gama Ubangiji ya aikata abin da ya faɗa ta bakin bawansa Iliya.”
11 Haka kuwa Yehu ya karkashe waɗanda suka ragu na gidan Ahab a Yezreyel, wato dukan manyan mutanensa, da abokansa, da firistocinsa. Bai rage masa ko guda ba.
An Kashe Dangin Ahaziya
12 Yehu kuma ya fita zai tafi Samariya. A hanya, sa’ad da yake a Bet-eked ta makiyaya,
13 sai ya sadu da ‘yan’uwan Ahaziya Sarkin Yahuza, sai ya ce, “Ku su wane ne?”
Sai suka amsa, “Mu ‘yan’uwan Ahaziya ne, mun zo mu gai da ‘ya’yan sarki ne da ‘ya’yan sarauniya.”
14 Yehu kuwa ya ce, “Ku kama su da rai.” Sai suka kama su da rai, suka karkashe su a ramin Bet-eked, su arba’in da biyu ne, ba a rage ko ɗaya a cikinsu ba.
An Kashe Dukan Sauran Dangin Ahab
15 Da ya tashi daga can, sai ya sadu da Yehonadab ɗan Rekab yana zuwa ya tarye shi. Yehu ya gaishe shi, ya tambaye shi, “Zuciyarka ta amince da ni kamar yadda tawa ta amince da kai?”
Yehonadab ya amsa, “I.”
Sai Yehu ya ce, “Idan haka ne, to, miƙo mini hannunka.” Sai ya miƙa masa hannunsa. Yehu kuwa ya ɗauke shi zuwa cikin karusa.
16 Ya ce, “Ka zo tare da ni, ka ga kishin da nake da shi domin Ubangiji.” Sai suka tafi cikin karusarsa.
17 Da suka isa Samariya, sai ya kashe duk wanda ya ragu na gidan Ahab a Samariya. Ya share mutanen gidan Ahab kaf kamar yadda Ubangiji ya faɗa ta bakin annabi Iliya.
An Kashe Masu Sujada ga Ba’al
18 Yehu kuwa ya tara mutane duka, ya ce musu, “Ahab ya bauta wa Ba’al kaɗan, amma Yehu zai bauta masa da yawa.
19 Saboda haka, yanzu sai ku kirawo mini dukan annabawan Ba’al, da dukan masu yi masa sujada, da dukan firistocinsa. Kada a manta da wani, gama ina da babbar hadayar da zan miƙa wa Ba’al. Duk wanda bai zo ba, za a kashe shi.” Amma dabara ce Yehu yake yi don ya hallaka waɗanda suke yi wa Ba’al sujada.
20 Yehu kuma ya sa a yi muhimmin taro saboda Ba’al. Aka kuwa kira taron,
21 sai ya aika cikin Isra’ila duka, dukan masu yi wa Ba’al sujada kuwa suka zo, ba wanda bai zo ba. Suka shiga, suka cika haikalin Ba’al makil daga wannan gefe zuwa wancan.
22 Sa’an nan Yehu ya ce wa wanda yake lura da ɗakin tufafi, “Ku fito da tufafi na dukan waɗanda suke yi wa Ba’al sujada.” Shi kuwa ya fito musu da tufafin.
23 Bayan wannan Yehu ya shiga haikalin Ba’al tare da Yehonadab ɗan Rekab, ya ce wa masu yi wa Ba’al sujada, “Ku bincike, ku tabbata, ba wani bawan Ubangiji tare da ku, sai dai masu yi wa Ba’al sujada kaɗai.”
24 Sa’an nan Yehu da Yehonadab suka shiga don su miƙa sadaka da hadayu na ƙonawa. Yehu ya riga ya sa mutum tamanin a waje, ya ce musu, “Mutumin da ya bar wani daga cikin waɗanda na bashe su a hannunku ya tsere, to, a bakin ransa.”
25 Nan da nan da Yehu ya gama miƙa hadaya ta ƙonawa, sai ya ce wa mai tsaro da shugabannin, “Ku shiga, ku karkashe su, kada ku bar wani ya tsere.” Da suka karkashe su, sai suka fitar da su waje, sa’an nan suka shiga can cikin haikalin Ba’al.
26 Suka fitar da gumakan da suke cikin haikalin Ba’al, suka ƙone su.
27 Suka yi kaca kaca da gunkin Ba’al da haikalinsa, suka mai da haikalin ya zama salga har wa yau.
28 Yehu ya kawar da Ba’al daga cikin Isra’ila.
29 Amma bai rabu da zunubin Yerobowam ɗan Nebat ba, wanda ya sa Isra’ila su yi zunubi. Siffofin maruƙa biyu suna nan a Betel da Dan.
30 Ubangiji kuwa ya ce wa Yehu, “Da yake ka yi abin da yake daidai a gare ni, ka yi wa gidan ahab bisa ga dukan abin da yake a zuciyata, ‘ya’yanka, har tsara ta huɗu, za su ci sarautar Isra’ila.”
31 Amma Yehu bai mai da hankali ya yi tafiya a tafarkin Ubangiji Allah na Isra’ila da zuciya ɗaya ba. Bai rabu da zunuban Yerobowam ba, wanda ya sa Isra’ila su yi zunubi.
Mutuwar Yehu
32 A kwanakin an Ubangiji ya soma rage ƙasar Isra’ila. Hazayel kuwa ya yaƙe su a karkarar Isra’ila,
33 tun daga Urdun har zuwa wajen gabas, da dukan ƙasar Gileyad, da ta Gad, da ta Ra’ubainu, da ta Manassa, tun daga Arower wadda dake kusa da kwarin Arnon haɗe da Gileyad da Bashan.
34 Sauran ayyukan Yehu da dukan abin da ya yi, da dukan ƙarfinsa an rubuta su a littafin tarihin sarakuna Isra’ila.
35 Yehu kuwa ya rasu, aka binne shi a Samariya. Yehowahaz ɗansa ya gaji sarautarsa.
36 Yehu ya yi mulkin Isra’ila a Samariya shekara ashirin da takwas.