An Naɗa Yehu Sarkin Isra’ila
1 Elisha kuwa ya kirawo ɗaya daga cikin annabawa matasa, ya ce masa, “Ka sha ɗamara, ka ɗauki wannan kurtun mai, ka tafi Ramot-gileyad.
2 Sa’ad da ka isa can, sai ka nemi Yehu, ɗan Yehoshafat, wato jikan Nimshi, ka shiga, ka sa ya tashi daga wurin abokansa, ka kai shi cikin ɗaki.
3 Sa’an nan ka ɗauki kurtun man, ka zuba masa a ka, ka ce, ‘Ubangiji ya ce ya keɓe ka Sarkin Isra’ila.’ Sa’an nan ka buɗe ƙofa, ka gudu, kada ka tsaya.”
4 Sai saurayin nan, annabin, ya tafi Ramot-gileyad.
5 Sa’ad da ya isa, sai ga shugabannin sojoji suna taro. Sai ya ce, “Ina da saƙo dominka, ya shugaba.”
Yehu kuwa ya ce, “Wane ne a cikinmu?”
Sai ya ce, “Kai ne, ya shugaba.”
6 Sai Yehu ya tashi ya shiga ɗaki, saurayin kuwa ya zuba masa mai a ka, ya ce, “Ubangiji, Allah na Isra’ila, ya keɓe ka sarkin jama’arsa, wato Isra’ila.
7 Za ka hallaka gidan Ahab, maigidanka, domin in ɗau fansar jinin annabawa bayinsa, da fansar jinin sauran bayin Ubangiji a kan Yezebel.
8 Gama dukan gidan Ahab zai hallaka. Zan datse wa Ahab kowane ɗa namiji, bawa ko ‘yantacce, cikin Isra’ila.
9 Zan mai da gidan Ahab kamar gidan Yeroboam ɗan Nebat, da kuma kamar gidan Ba’asha ɗan Ahija.
10 Karnuka za su cinye Yezebel a cikin Yezreyel, ba wanda zai binne ta.” Sa’an nan ya buɗe ƙofar, ya gudu.
11 Da Yehu ya fita zuwa wurin sauran shugabannin, sai suka tambaye shi, “Lafiya kuwa, me ya sa mahaukacin nan ya zo wurinka?”
Sai ya ce musu, “Ai, kun san mutumin da irin maganarsa.”
12 Suka ce, “Ba mu sani ba, sai ka faɗa mana.”
Shi kuwa ya ce, “Ya faɗa mini, wai Ubangiji ya ce ya keɓe ni Sarkin Isra’ila.”
13 Sai kowane mutum a cikinsu ya yi maza ya tuɓe rigarsa, ya shimfiɗa a kan matakan, sa’an nan suka busa ƙaho, suna cewa, “Yehu ne sarki.”
Yehu Ya Kashe Yehoram Sarkin Isra’ila
14 Ta haka Yehu, ɗan Yehoshafat, wato jikan Nimshi, ya tayar wa Yehoram. A lokacin, Yehoram tare da dukan Isra’ila suna tsaron Ramot-gileyad, don kada Hazayel, Sarkin Suriya, ya fāɗa mata.
15 Amma sarki Yehoram ya komo Yezreyel, don ya yi jiyyar raunukan da Suriyawa suka yi masa sa’ad da ya yi yaƙi da Hazayel Sarkin Suriya. Sai Yehu ya ce, “Idan wannan shi ne nufinku, to, kada kowa ya zurare, ya tafi, ya ba da labari a Yezreyel.”
16 Sa’an nan Yehu ya hau karusarsa ya tafi Yezreyel, gama a can ne Yehoram yake kwance. Ahaziya Sarkin Yahuza ya gangara don ya gai da Yehoram.
17 Mai tsaro kuwa yana tsaye a kan hasumiya a Yezreyel, sai ya hangi rundunar Yehu sa’ad da yake zuwa. Ya ce, “Na ga wata runduna.”
Sai Yehoram ya ce, “Ka aiki wani, ya hau doki, ya tafi ya tarye su, ya tambaye su, ko lafiya.”
18 Sai wani mutum ya hau doki ya tafi ya tarye su, ya ce, “Sarki ya ce, lafiya kuwa?”
Sai Yehu ya ce, “Ina ruwanka da lafiya? Kewaya ka bi bayana.”
Mai tsaro kuma ya ce, “Manzo ya kai wurinsu, amma bai komo ba.”
19 Ya kuma aiki wani, na biyu, a kan doki, ya je wurinsu ya ce musu, “Sarki ya ce, lafiya kuwa?”
Yehu ya amsa, ya ce, “Ina ruwanka da lafiya? Kewaya ka bi bayana.”
20 Mai tsaro ya sāke cewa, “Ya kai wurinsu, amma bai komo ba. Ina ganin sukuwar kamar irin ta Yehu, jikan Nimshi, gama yakan yi sukuwa da hauka.”
21 Yehoram kuwa ya ce, “Ku shirya karusa.” Suka shirya masa karusa. Sa’an nan Yehoram Sarkin Isra’ila, da Ahaziya Sarkin Yahuza suka fita, kowa a cikin karusarsa, suka tafi su taryi Yehu. Suka sadu da shi a daidai gonar Nabot mutumin Yezreyel.”
22 Da Yehoram ya ga Yehu, sai ya ce, “Lafiya dai?”
Yehu ya ce, “Ina fa lafiya, tun da karuwanci da sihirin uwarka, Yezebel, sun yi yawa haka?
23 Yehoram kuwa ya juyar da karusarsa baya, ya gudu, yana ce wa Ahaziya, “Maƙarƙashiya ce, ya Ahaziya!”
24 Sai Yehu ya ja bakansa da iyakar ƙarfinsa ya ɗirka wa Yehoram kibiya, ta sha zarar zuciyarsa, sai ya ɓingire cikin karusarsa.
25 Yehu ya ce wa Bidkar, “Ka ɗauke shi ka jefar a gonar Nabot mutumin Yezreyel, gama ka tuna sa’ad da ni da kai muke kan dawakai muna biye da Ahab, tsohonsa, yadda Ubangiji ya faɗi wannan magana a kansa cewa,
26 ‘Hakika, kamar yadda jiya na ga jinin Nabot da na ‘ya’yansa, ni Ubangiji, zan sāka maka saboda wannan gona.’ Yanzu sai ka ɗauke shi, ka jefar da shi a wannan gona kamar yadda Ubangiji ya faɗa.”
Yehu Ya Kashe Ahaziya
27 Da Ahaziya Sarkin Yahuza, ya ga haka, sai ya gudu ta hanyar Bet-haggan.Yehu kuwa ya bi shi, ya ce, “Shi ma a harbe shi.” Sai suka harbe shi a cikin karusarsa a hawan Gur, wanda yake kusa da Ibleyam. Sai ya gudu zuwa Magiddo, ya mutu a can.
28 Fādawansa suka ɗauke shi a cikin karusar zuwa Urushalima, suka binne shi a kabarinsa tare da kakanninsa a birnin Dawuda.
29 Ahaziya ya ci sarautar Yahuza a shekara ta goma sha ɗaya ta sarautar Yehoram ɗan Ahab.
Mutuwar Yezebel
30 Da Yezebel ta ji Yehu ya zo Yezreyel, sai ta shafa wa idanunta launi, ta gyara gashin kanta, sa’an nan ta leƙa ta taga.
31 Da Yehu ya shiga ƙofar garin, sai ta ce, “Kai Zimri, mai kashe maigidansa, me kake yi a nan?”
32 Sai ya ɗaga idanunsa wajen tagar, ya ce, “Wa yake wajena?” Sai babani biyu ko uku suka dube shi,
33 shi kuwa ya ce, “Ku wurgo ta ƙasa.” Sai suka wurgo ta ƙasa. Jininta ya fantsama a jikin bangon da jikin dawakan da suka tattake ta.
34 Sa’an nan Yehu ya shiga gida, ya ci ya sha, ya ce, “Ku san yadda za ku yi da wannan la’ananniyar mace, ku binne ta, gama ita ‘yar sarki ce.”
35 Amma da suka tafi don su binne ta, ba su tarar da kome ba sai ƙwaƙwalwa, da ƙafafu, da tafin hannuwanta.
36 Sai suka komo, suka faɗa masa. Sai ya ce musu, “Wannan, ai, faɗar Ubangiji, wadda ya faɗa ta bakin bawansa Iliya Batishbe, ya ce, ‘Karnuka za su cinye naman Yezebel a cikin Yezreyel.
37 Gawar Yezebel za ta zama wa ƙasa taki a Yezreyel don kada wani ya iya cewa wannan ita ce Yezebel.’ ”