An Tsamo Ruwan Gatari
1 Ƙungiyar annabawa da suke a hannun Elisha suka kawo masa kuka, suka ce, “Ga shi, wurin da muke zaune ya yi mana kaɗan.
2 Ka ba mu izini mu tafi Kogin Urdun, domin mu saro gumagumai a can, mu ƙara wa kanmu wurin zama.”
Sai ya ce, “Ku tafi.”
3 Ɗaya daga cikinsu kuwa ya ce, “In ka yarda, ka tafi tare da mu.”
Elisha kuwa ya yarda, ya ce, “To, mu tafi.”
4 Ya kuwa tafi tare da su.
Sa’ad da suka isa Urdun, suka sassari itatuwa.
5 Amma sa’ad da ɗaya daga cikinsu yake saran wani gungume, sai ruwan gatarinsa ya kwaɓe ya fāɗa a ruwa. Sai ya yi ihu, ya ce, “Wayyo, maigida, me zan yi? Abin aro ne.”
6 Sa’an nan Elisha ya ce, “Daidai ina ya fāɗa?”
Da ya nuna masa wurin, sai ya karyi tsumagiya, ya jefa a wurin, ya sa ruwan gatarin ya taso bisa kan ruwan.
7 Sa’an nan ya ce, “Ɗauko.” Sai mutumin ya miƙa hannu, ya ɗauka.
Elisha da Suriyawa
8 Wata rana, sa’ad da Sarkin Suriya yake yaƙi da Isra’ila, sai ya shawarci fādawansa, suka zaɓi wurin da za su kafa sansani.
9 Amma Elisha ya aika wa Sarkin Isra’ila, ya ce, “Ka yi hankali, kada ka wuce wuri kaza, gama Suriyawa suna gangarawa zuwa can.”
10 Sarkin Isra’ila kuwa ya aika zuwa wurin da Elisha ya faɗa masa. Da haka ya riƙa faɗakar da shi, har ya ceci kansa ba sau ɗaya, ba sau biyu ba.
11 Zuciyar Sarkin Suriya kuwa ta ɓaci ƙwarai a kan wannan al’amari, don haka ya kirawo fādawansa, ya ce musu, “Wane ne wannan da yake cikinmu, yana goyon bayan Sarkin Isra’ila?”
12 Ɗaya daga cikin fādawan ya ce, “A’a, ranka ya daɗe, sarki, ai, annabi Elisha ne wanda yake cikin Isra’ila, yake faɗa wa Sarkin Isra’ila maganar da kake faɗa a ɗakin kwananka.”
13 Sai ya ce, “Ku tafi, ku ga inda yake don in aika a kamo shi.” Aka faɗa masa, cewa a Dotan yake.
14 Sai ya aika da dawakai, da karusai, da sojoji da yawa. Suka tafi da dare suka kewaye garin.
15 Da baran annabi Elisha ya tashi da sassafe, ya fita waje, sai ga sojoji, da dawakai, da karusai sun kewaye gari. Sai baran ya ce, “Wayyo, maigidana! Me za mu yi?”
16 Elisha kuwa ya ce masa, “Kada ka ji tsoro gama waɗanda suke tare da mu, sun fi waɗanda suke tare da su yawa.”
17 Sa’an nan Elisha ya yi addu’a ya ce, “Ya Ubangiji, ka buɗe idanunsa ya gani.” Ubangiji kuwa ya buɗe idanun saurayin, sai ga dutsen cike da dawakai da karusan wuta kewaye da Elisha.
18 Da Suriyawa suka gangaro wurinsa, sai Elisha ya yi addu’a ga Ubangiji, ya ce, “Ina roƙonka, ka bugi mutanen nan da makanta.” Ubangiji kuwa ya buge su da makanta bisa ga addu’ar Elisha.
19 Sa’an nan Elisha ya ce musu, “Wannan ba ita ce hanyar ba, ba kuma gari ke nan ba, ku bi ni, ni kuwa in kai ku wurin mutumin da kuke nema.” Sai ya kai su Samariya.
20 Da shigarsu Samariya, sai Elisha, ya ce, “Ya Ubangiji, ka buɗe idanun mutanen nan su gani.” Ubangiji kuwa ya buɗe idanunsu, suka gani, ashe, suna tsakiyar Samariya ne.
21 Da Sarkin Isra’ila ya gan su, sai ya ce wa Elisha, “Ya mai girma, in karkashe su? In karkashe su?”
22 Amma Elisha ya ce, “Ba za ka karkashe su ba. Ba za ka karkashe waɗanda ba kai ka kama su ta wurin takobinka ko bakanka ba. Ka ba su abinci da ruwa su ci su sha, su koma wurin shugabansu.”
23 Sai ya shirya musu babbar liyafa. Sa’ad da suka ci suka sha, sai ya sallame su, suka koma wurin shugabansu. Suriyawa kuwa ba su ƙara kai wa ƙasar Isra’ila hari ba.
Elisha da Yaƙi a Samariya
24 Bayan wannan kuwa Ben-hadad, Sarkin Suriya, ya tattara sojojinsa duka, ya haura ya kewaye Samariya da yaƙi.
25 Aka yi yunwa mai tsanani a Samariya a lokacin da aka kewaye ta da yaƙin, har aka riƙa sayar da kan jaki a bakin shekel tamanin, an kuma sayar da rubu’in mudu na kashin kurciya a bakin shekel biyar.
26 Sa’ad da Sarkin Isra’ila yake wucewa ta kan garun birni, sai wata mace ta yi masa kuka, ta ce, “Ka yi taimako, ran sarki ya daɗe.”
27 Shi kuwa ya ce, “Idan Ubangiji bai taimake ki ba, ƙaƙa zan yi, ni in taimake ki? Ina da alkama ne ko kuwa ina da ruwan inabi?
28 Me yake damunki?”
Sai ta amsa, ta ce, “Wannan mace ta ce mini, in kawo ɗana mu ci yau, gobe kuma mu ci nata.
29 Sai muka dafa ɗana muka cinye. Kashegari kuwa na ce mata ta kawo ɗanta mu ci, amma sai ta ɓoye shi.”
30 Da sarki ya ji maganar macen, sai ya keta tufafinsa, sa’ad da yake wucewa ta kan garun birni. Sai mutane suka gani, ashe, yana saye da rigar makoki a ciki.
31 Ya ce, “Allah ya yi mini hukunci mai tsanani, idan ban fille kan Elisha ɗan Shafat yau ba.”
32 Elisha kuwa yana zaune a gidansa, dattawa kuma suna zaune tare da shi. Sai sarki ya aiki mutum, amma kafin mutumin ya isa, sai Elisha ya ce wa dattawan, “Kun ga yadda mai kisankan nan ya aiko don a fille mini kai? Idan mutumin ya zo, sai ku rufe ƙofar, ku riƙe ta da ƙarfi. Ba da jimawa ba sarki zai bi bayansa.”
33 Yana magana da su ke nan, sai sarki ya iso, ya ce, “Wannan masifa daga wurin Ubangiji ta fito, don me zan ƙara jiran Ubangiji kuma?”