Na’aman Ya Warke daga Kuturta
1 Na’aman kuwa, shugaban sojojin Sarkin Suriya, shi babba ne mai farin jini ƙwarai a wurin ubangidansa, domin ta wurinsa ne Ubangiji ya ba Suriyawa nasara. Shi mutum ne ƙaƙƙarfan jarumi, amma kuma kuturu ne.
2 Daga cikin hare-haren da Suriyawa suke kaiwa, sai suka kama wata yarinya daga ƙasar Isra’ila, aka sa ta zama mai yi wa matar Na’aman aiki.
3 Wata rana sai ta ce wa uwargijyarta, “Da a ce ubangijina yana tare da annabin nan wanda yake Samariya, da ya warkar da shi daga kuturtarsa!”
4 Na’aman kuwa ya tafi, ya faɗa wa ubangidansa, ya ce, “Ka ji abin da yarinyan nan ta ƙasar Isra’ila ta ce?”
5 Sai Sarkin Suriya ya ce, “Ka tafi yanzu, zan aika wa Sarkin Isra’ila da takarda.”
Na’aman kuwa ya ɗauki azurfa na talanti goma, zinariya kuma na shekel dubu shida (6,000), da rigunan ado guda goma, ya kama hanya.
6 Ya kai wa Sarkin Isra’ila tarkardar, wadda ta ce, “Sa’ad da wannan takarda ta sadu da kai, ka sani fa, ni ne na aiko barana, Na’aman, wurinka domin ka warkar da shi daga kuturtarsa.”
7 Da Sarkin Isra’ila ya karanta takardar, sai ya keta tufafinsa, ya ce, “Ni Allah ne, da zan kashe in rayar, har mutumin nan zai aiko mini da cewa in warkar da mutum daga kuturtarsa? Ku duba fa, ku ga yadda yake nemana da faɗa.”
8 Amma sa’ad da Elisha, annabin Allah, ya ji cewa Sarkin Isra’ila ya keta tufafinsa, sai ya aika wa sarki ya ce, “Me ya sa ka keta tufafinka? Bari ya zo wurina, zai sani akwai annabi a Isra’ila.”
9 Na’aman kuwa da dawakansa da karusansa suka tafi suka tsaya a ƙofar gidan Elisha.
10 Sai Elisha ya aiki manzo ya faɗa wa Na’aman ya tafi, ya yi wanka a Kogin Urdun har sau bakwai, naman jikinsa zai warke, zai tsarkaka.
11 Amma Na’aman ya husata, ya yi tafiyarsa, yana cewa, “Na yi tsammani zai fito ya zo wurina ne, ya tsaya, ya yi kira sunan Ubangiji Allahnsa ya kaɗa hannunsa a wurin kuturtar, ya warkar da ni.
12 Ashe, kogin Abana da na Farfar, wato kogunan Dimashƙu, ba su fi dukan ruwayen Isra’ila ba? Da ban yi wanka a cikinsu na tsarkaka ba?” Ya juya, ya yi tafiyarsa da fushi.
13 Amma barorinsa suka je wurinsa, suka ce masa, “Ranka ya daɗe, da a ce annabin ya umarce ka ka yi wani babban abu ne, ashe, da ba ka yi ba, balle wannan, da ya ce ka tafi ka yi wanka, ka tsarkaka?”
14 Sai ya tafi ya yi wanka har sau bakwai a Kogin Urdun bisa ga maganar annabin Allah, sai naman jikinsa ya warke ya zama kamar na ƙaramin yaro, ya tsarkaka.
15 Ya kuwa komo wurin annabi Elisha shi da jama’arsa duka, ya zo ya tsaya a gabansa, ya ce, “Yanzu na sani a duniya duka ba wani Allah banda na Isra’ila, saboda haka, sai ka karɓi kyauta daga wurina.”
16 Amma Elisha ya ce, “Na rantse da Ubangiji, wanda nake bauta masa, ba zan karɓi kome ba.”
Ya yi ta roƙonsa ya karɓa, amma ya ƙi.
17 Na’aman kuwa ya ce, “Da yake ka ƙi ka karɓa, ina roƙonka, ka ba baranka labtun alfadari biyu na ƙasa, gama nan gaba baranka ba zai ƙara miƙa hadaya ta ƙonawa ko baiko ga wani gunki ba, sai dai Ubangiji.
18 Sai dai Ubangiji ya gafarta mini lokacin da na bi sarki zuwa cikin haikalin Rimmon, gunkin Suriya, don ya yi sujada. Na gaskata Ubangiji zai gafarta mini.”
19 Elisha kuwa ya ce masa, “Ka sauka lafiya.” Na’aman ya tafi.
Amma tun Na’aman bai yi nisa ba,
20 sai Gehazi, baran annabi Elisha, ya ce, “Duba, maigidana ya bar Na’aman Basuriyen nan ya tafi, bai karɓi kome daga cikin abin da ya kawo masa ba. Na rantse da Ubangiji, zan sheƙa a guje, in bi shi, in karɓi wani abu daga gare shi.”
21 Gehazi kuwa ya bi bayan Na’aman.
Da Na’aman ya ga wani yana biye da shi a guje, sai ya sauka daga karusarsa, ya juya ya tarye shi, ya ce, “In ce ko lafiya?”
22 Gehazi ya ce, “Lafiya ƙalau, maigidana ne ya aiko ni in faɗa maka, yanzu yanzu waɗansu samari biyu daga ƙungiyar annabawa suka zo wurinsa daga ƙasar tudu ta Ifraimu, yana roƙonka, ka ba ni talanti ɗaya na azurfa da rigunan ado guda biyu in kai masa.”
23 Na’aman kuwa ya ce, “In ka yarda ka karɓi talanti biyu na azurfa.” Ya ƙirga su ya ɗaure kashi biyu, da kuma rigunan ado masu kyau ya ɗora wa barorinsa biyu, ya umarce su su kai wa Gehazi har gida.
24 Sa’ad da Gehazi ya kai tudu, sai ya karɓi kayan daga hannunsu, ya ajiye a gida, sa’an nan ya sallame su, suka tafi.
25 Sai ya shiga, ya tsaya a gaban Elisha, Elisha kuwa ya tambaye shi, “Ina ka tafi, Gehazi?”
Sai ya ce, “Ranka ya daɗe ban tafi ko’ina ba.”
26 Amma Elisha ya ce masa, “Ashe, ba ina tare da kai a ruhu ba, sa’ad da mutumin ya juyo daga karusarsa don ya tarye ka? Wannan shi ne lokacin karɓar kuɗi, da riguna, da gonaki na zaitun, da na inabi, da tumaki, da shanu, da barori mata da maza?
27 Saboda haka kuturtar Na’aman za ta kama ka, kai da zuriyarka har abada.”
Haka kuwa ya fita a wurinsa kuturu, fari fat kamar auduga.