Yaƙi tsakanin Isra’ila da Mowab
1 A shekara ta goma sha takwas ta sarautar Yehoshafat Sarkin Yahuza, Yehoram ɗan Ahab ya zama Sarkin Isra’ila a Samariya. Ya yi mulki shekara goma sha biyu.
2 Ya aikata mugun abu a gaban Ubangiji, amma bai kai na tsohonsa da tsohuwarsa ba, gama ya kawar da ginshiƙin gunkin nan Ba’al wanda tsohonsa ya yi.
3 Duk da haka, bai rabu da zunubin Yerobowam ɗan Nebat ba, wanda ya sa mutanen Isra’ila su yi zunubi.
4 Mesha Sarkin Mowab kuwa makiyayin tumaki ni. Yakan ba Sarkin Isra’ila ‘yan tumaki dubu ɗari (100,000), da raguna dubu ɗari (100,000) duk da ulunsu, gandu a shekara.
5 Amma da Ahab ya rasu, Sarkin Mowab kuwa ya tayar wa Sarkin Isra’ila.
6 Sai sarki Yehoram ya fita daga Samariya a lokacin, ya tattara Isra’ila duka.
7 Ya kuma aika wa Yehoshafat Sarkin Yahuza, ya ce, “Sarkin Mowab ya tayar mini, ko za ka yarda ka tafi tare da ni mu yaƙi Mowabawa?”
Yehoshafat ya ce, “Zan tafi, ni kamarka ne, mutanena kuma kamar mutanenka, dawakaina kuma kamar naka.
8 Wace hanya za mu bi?”
Yehoram kuwa ya ce, “Ta hanyar jejin Edom.”
9 Yehoram Sarkin Isra’ila ya tafi tare da Sarkin Yahuza da Sarkin Edom. Da suka yi kwana bakwai suna ta zagawa, sai sojoji da dabbobi suka rasa ruwan sha.
10 Sa’an nan Sarkin Isra’ila ya ce, “Kaito! Ubangiji ya kirawo mu sarakunan nan uku don ya bashe mu a hannun Mowabawa.”
11 Yehoshafat ya ce, “Ba wani annabin Ubangiji ne a nan, wanda zai tambayar mana Ubangiji?”
Sai ɗaya daga cikin fādawan Sarkin Isra’ila ya amsa ya ce, “Ai, akwai Elisha ɗan Shafat, na’ibin Iliya.”
12 Yehoshafat kuwa ya ce, “Gaskiya ne, maganar Ubangiji tana tare da shi.” Saboda haka sai sarakunan nan uku suka ɗunguma zuwa wurin Elisha.
13 Elisha kuwa ya ce wa Sarkin Isra’ila, “Ina ruwana da kai? Tafi wurin annabawan tsohonka da na tsohuwarka.”
Amma Sarkin Isra’ila ya ce masa, “A’a, ai, Ubangiji ya kirawo mu, mu sarakunan nan uku, domin ya bashe mu a hannun Mowabawa.”
14 Elisha ya amsa ya ce, “Na rantse da Ubangiji Mai Runduna, wanda nake bautarsa, da ba domin ina ganin girman Yehoshafat Sarkin Yahuza ba, da ba zan kula da kai har ma in dube ka ba.
15 Amma yanzu ku kawo mini makaɗin garaya.”
Da makaɗin garaya ya kaɗa, sai ikon Ubangiji ya sauko a kan Elisha.
16 Sai ya ce, “Ubangiji ya ce, ‘Ku haƙa kududdufai a kwarin nan.
17 Ko da yake ba ku ga iska, ko ruwan sama ba, duk da haka kwarin zai cika da ruwa domin ku sha, ku da dabbobinku.’
18 Wannan abu mai sauƙi ne a wurin Ubangiji, zai kuma ba da Mowabawa a hannunku.
19 Za ku ci kowane birni mai garu da kowane birni na musamman. Za ku sassare kowane kyakkyawan itace, ku kuma tattoshe maɓuɓɓugan ruwa. Za ku lalatar da gonaki masu kyau da duwatsu.”
20 Kashegari, da safe a lokacin miƙa hadaya, sai ga ruwa ya malalo daga wajen Edom har ƙasar ta cika da ruwa.
21 Da Mowabawa suka ji labari, sarakuna sun kawo musu yaƙi, sai dukan waɗanda suka isa ɗaukar makamai, daga ƙarami zuwa babba, aka kirawo su, suka ja dāga a kan iyaka.
22 Sa’ad da suka tashi da sassafe, rana tana haskaka ruwa, sai suka ga ruwan a gabansu ja wur kamar jini.
23 Sai suka ce, “Wannan jini ne, hakika sarakunan sun yi yaƙi da juna, sun karkashe juna. Bari mu tafi mu kwashi ganima!”
24 Da suka kai sansanin Isra’ilawa, sai Isra’ilawa suka tashi, suka fāɗa musu, har suka gudu. Isra’ilawa kuwa suka bi su, suna ta karkashe su,
25 suka lalatar da biranensu, a kowace kyakkyawar gona kuma, kowannensu ya jefa dutse a cikinta, har aka cika ta da duwatsu, suka kuma tattoshe kowace maɓuɓɓugar ruwa, suka sassare kyawawan itatuwa. Babban birnin Kir-hareset kaɗai ya ragu, Isra’ilawa suka kewaye shi suka fāɗa shi da yaƙi.
26 Da Sarkin Mowab ya ga yaƙin ya juya masa baya, sai ya zaɓi masu takobi ɗari bakwai ya kutsa kai a wajen ɓayar Sarkin Edom, amma suka kāsa.
27 Sai Sarkin Mowab ya kama babban ɗansa, wanda zai gāji sarautarsa, ya miƙa shi hadayar ƙonawa a kan garu. Isra’ilawa kuwa suka tsorata ko allahn abokan gāba zai cuce su, don haka suka janye, suka koma ƙasarsu.