An Ɗauki Iliya zuwa Sama
1 Sa’ad da Ubangiji zai ɗauki Iliya zuwa Sama cikin guguwa, Iliya da Elisha suka kama hanya daga Gilgal.
2 Sai Iliya ya ce wa Elisha, “Ina roƙonka, ka dakata a nan, gama Ubangiji ya aike ni har zuwa Betel.”
Amma Elisha ya ce, “Na rantse da Ubangiji da kuma kai kanka, ba zan rabu da kai ba.” Saboda haka suka tafi Betel.
3 Akwai wata ƙungiyar annabawa da take a Betel suka zo, suka ce wa Elisha, “Ko ka sani, yau Ubangiji zai ɗauke maigidanka?”
Elisha ya ce, “I, na sani, amma mu bar zancen tukuna.”
4 Sa’an nan Iliya ya ce masa, “Elisha, ina roƙonka ka dakata a nan gama Ubangiji ya aike ni Yariko.”
Amma Elisha ya ce, “Na rantse da Ubangiji da kuma kai kanka, ba zan rabu da kai ba.” Sai suka tafi Yariko.
5 Ƙungiyar annabawa da take Yariko suka zo wurin Elisha suka ce masa, “Ko ka sani yau Ubangiji zai ɗauke maigidanka?”
Ya ce, “Na sani, amma mu bar zancen tukuna.”
6 Sa’an nan Iliya ya ce masa, “Ina roƙonka, ka dakata a nan, gama Ubangiji ya aike ni zuwa Kogin Urdun.”
Amma Elisha ya ce, “Na rantse da Ubangiji da kuma kai kanka, ba zan rabu da kai ba.” Saboda haka suka tafi tare.
7 Waɗansu annabawa hamsin kuma suka tafi tare da su. Iliya da Elisha suka tsaya kusa da kogi, annabawa hamsin ɗin suka tsaya da ɗan nisa.
8 Sa’an nan Iliya ya tuɓe alkyabbarsa, ya naɗe ta, ya bugi ruwa da ita, sai ruwan ya dāre, ya rabu biyu, dukansu biyu fa suka taka sandararriyar ƙasa suka haye.
9 Sa’ad da suka haye, sai Iliya ya ce wa Elisha, “Ka faɗa mini abin da kake so in yi maka kafin a ɗauke ni daga wurinka.”
Elisha ya ce, “Bari in sami rabo daga cikin ikonka domin in gaje ka.”
10 Iliya kuwa ya ce, “Ka roƙi abu mai wuya, duk da haka, idan ka gan ni lokacin da za a ɗauke ni, to, abin da ka roƙa za ka samu, amma idan ba ka gan ni ba, to, ba za ka samu ba ke nan.”
11 Da suka ci gaba da tafiya suna taɗi, sai ga karusar wuta da dawakan wuta suka raba su. Aka ɗauke Iliya zuwa Sama cikin guguwa.
12 Elisha kuwa ya gani, ya yi kuka yana cewa, “Ubana, ubana! Mai ikon tsaron Isra’ila! Ka tafi ke nan!” Bai kuwa ƙara ganin Iliya ba.
Elisha Ya Gāji Iliya
Da baƙin ciki Elisha ya kama tufafinsa ya kece.
13 Sa’an nan ya ɗauki alkyabbar Iliya wadda ta faɗo daga wurinsa, ya tafi ya tsaya a gaɓar Kogin Urdun.
14 Sai ya ɗauki alkyabban nan da ta faɗo daga wurin Iliya, ya bugi ruwan, yana cewa, “Ina Ubangiji, Allah na Iliya?” Sa’ad da ya bugi ruwan, sai ruwan ya dāre, ya rabu biyu, Elisha kuwa ya haye.
15 Sa’ad da annabawa hamsin da suke Yariko suka ga ya haye ya nufo su, sai suka ce, “Ai, ruhun Iliya yana kan Elisha.” Sai suka tafi su tarye shi, suka rusuna har ƙasa a gabansa,
16 suka kuma ce masa, “Yanzu fa, ga mu mu hamsin ƙarfafa. Bari mu tafi mu nemo maigidanka, mai yiwuwa ne Ruhun Ubangiji ya ɗauke shi, ya jefa shi kan wani dutse, ko cikin wani kwari.”
Elisha ya ce, “Kada ku tafi.”
17 Amma suka matsa masa har suka i masa, sai ya yardar musu su tafi. Su kuwa suka tafi su hamsin. Suka yi ta neman Iliya, har kwana uku, amma ba su same shi ba.
18 Sa’an nan suka komo wurinsa a Yariko. Sai ya ce musu, “Ai, dā ma na ce muku kada ku tafi.”
Mu’ujizan Elisha
19 Waɗansu mutanen gari suka ce wa Elisha, “Ga shi, garin yana da kyan gani, amma ruwan ba kyau, yana sa ana yin ɓari.”
20 Elisha kuwa ya ce, “Ku kawo mini gishiri a sabuwar ƙwarya.” Su kuwa suka kawo masa,
21 sai ya tafi maɓuɓɓugar ruwa yana barbaɗa gishirin, ya ce, “Haka Ubangiji ya ce, ‘Na warkar da wannan ruwa, ba zai ƙara sa a mutu ko a yi ɓari ba.’ ”
22 Ruwan kuwa ya gyaru bisa ga maganar Elisha, har wa yau.
23 Daga nan Elisha ya haura zuwa Betel. A hanya sai ga waɗansu samari sun fito daga cikin gari, suna yi masa eho, suna cewa, “Ka bar wurin nan, kai mai saiƙo.”
24 Elisha ya waiga, ya gan su, ya la’anta su da sunan Ubangiji. Sai waɗansu namomin jeji guda biyu suka fito daga cikin kurmi suka yayyage arba’in da biyu daga cikin samarin.
25 Daga nan Elisha ya tafi har Dutsen Karmel, sa’an nan ya koma Samariya.