Rasuwar Ahaziya
1 Bayan rasuwar Ahab, Sarkin Isra’ila, sai Mowabawa suka tayar wa Isra’ilawa.
2 Ahaziya ya faɗo daga tagar benensa a Samariya, ya kuwa ji ciwo ƙwarai. Sai ya aiki manzanni, ya ce musu, “Ku tafi, ku tambayi Ba’alzabul, gunkin Ekron, ko zan warke daga wannan ciwo.”
3 Sai mala’ikan Ubangiji ya yi magana da Iliya Batishbe, ya ce, “Tashi, ka tafi, ka sadu da manzannin Sarkin Samariya, ka ce musu, ‘Ba Allah a Isra’ila da za ku tafi ku tambayi Ba’alzabul, gunkin Ekron?’
4 Ku faɗa wa sarki, Ubangiji ya ce, ‘Ba za ka tashi daga kan gadon da kake kwance ba, amma lalle za ka mutu.’ ”
Iliya ya yi kamar yadda Ubangiji ya umarce shi, sai ya tafi.
5 Manzannin kuwa suka koma wurin sarki. Sarki ya ce, “Me ya sa kuka komo?”
6 Suka ce masa, “Wani mutum ya sadu da mu, ya ce mana, mu koma wurinka mu shaida maka, ‘Ubangiji ya ce, ba Allah a Isra’ila, har aka aike ku ku tambayi Ba’alzabul, gunkin Ekron? Domin haka ba za ka tashi daga kan gadon da kake kwance ba, amma lalle za ka mutu.’ ”
7 Sarki ya tambaye su, “Yaya mutumin yake, shi wanda ya sadu da ku, ya faɗa muku irin wannan magana?”
8 Suka ce masa, “Ai, wani gargasa ne mai ɗamara ta fata.”
Sarki ya ce, “Ai, Iliya ne Batishbe.”
9 Sa’an nan sarki ya aiki shugaba tare da mutum hamsin su taho da Iliya. Mutumin kuwa ya haura wurin Iliya a kan dutse, ya ce masa, “Ya mutumin Allah, sarki ya umarta ka sauko.”
10 Iliya ya ce wa shugaban da mutum hamsin ɗin, “Idan ni mutumin Allah ne, bari wuta ta sauko daga sama ta cinye ka da mutane naka hamsin.” Wuta kuwa ta sauko daga sama, ta cinye shugaban tare da mutanensa hamsin.
11 Sarki kuma ya sāke aiken wani shugaba tare da mutum hamsin. Suka tafi, shugaban ya ce wa Iliya, “Ya mutumin Allah, sarki ya umarta ka sauko da sauri.”
12 Iliya kuwa ya ce musu, “Idan ni mutumin Allah ne, bari wuta ta sauko daga sama ta cinye ka da mutane naka guda hamsin.” Wuta kuwa daga wurin Allah ta sauko daga sama ta cinye shugaban da mutanensa hamsin.
13 Sarki kuma ya sāke aiken wani shugaba, na uku ke nan, tare da mutanensa hamsin. Sai shugaba na uku ya tafi ya rusuna a gaban Iliya, ya roƙe shi, ya ce, “Ya mutumin Allah, ina roƙonka ka ga darajar raina da na barorinka, su hamsin.
14 Gama wuta ta sauko daga sama ta cinye shugabanni biyu tare da mutanensu hamsin hamsin, amma ka dubi darajar raina.”
15 Sa’an nan mala’ikan Ubangiji ya ce wa Iliya, “Ka sauka, ka tafi tare da shi, kada ka ji tsoronsa.” Iliya kuwa ya tashi, ya tafi tare da shi har gaban sarki.
16 Ya ce wa sarki, “Ubangiji ya ce, ‘Domin ka aiki manzanni su yi tambaya wurin Ba’alzabul, gunkin Ekron, ba Allah a Isra’ila ne wanda za ka yi tambaya a wurinsa? Domin haka ba za ka sauko daga kan gadon da kake kwance ba, amma za ka mutu lalle.’ ”
17 Ahaziya kuwa ya mutu bisa ga maganar Ubangiji, daidai yadda Iliya ya faɗa. Sai ɗan’uwansa Yehoram ya gāji gadon sarautarsa a shekara ta biyu ta Yoram ɗan Yehoshafat Sarkin Yahuza, gama Ahaziya ba shi da ɗa.
18 Sauran ayyukan da Ahaziya ya yi, an rubuta su a littafin tarihin sarakunan Isra’ila.