Ahab Ya Ci Suriyawa
1 Ben-hadad Sarkin Suriya kuwa ya tara dukan sojojinsa. Sarakuna talatin da biyu kuma suna tare da shi, da dawakai, da karusai. Ya haura ya kai wa Samariya yaƙi. Ya kuwa yi yaƙi da ita.
2 Sai ya aika da jakadu zuwa cikin birni wurin sarki Ahab na Isra’ila, ya ce masa, “In ji Ben-hadad,
3 ‘Azurfarka da zinariyarka nawa ne, matanka kuma mafi kyau da ‘ya’yanka nawa ne!’ ”
4 Ahab Sarkin Isra’ila kuwa ya amsa, ya ce, “Ya maigirma sarki, kamar yadda ka faɗa, ni naka ne da dukan abin da nake da shi.”
5 Jakadun kuwa suka sāke komawa suka ce wa Ahab, “Ben-hadad ya ce, ‘Na aika maka ka ba ni azurfarka, da zinariyarka, da matanka, da ‘ya’yanka.
6 Banda haka kuma zan aiko barorina wurinka gobe war haka su bincike gidanka da gidajen fādawanka, su kwashe dukan abubuwan da kake ganin darajarsu su tafi da su.’ ”
7 Ahab Sarkin Isra’ila kuwa ya kirawo dukan dattawan ƙasar, ya ce, “Ku gani fa, ku duba yadda mutumin nan yake neman rikici, gama ya aiko don in ba shi matana, da ‘ya’yana, da azurfata, da zinariyata, ni kuwa ban hana masa ba.”
8 Dukan dattawan da mutane, suka ce masa, “Kada ka kula, balle ka yarda.”
9 Sai ya ce wa jakadun Ben-hadad, “Ku ce wa maigirma, sarki, dukan abin da ya nema a wurina da farko, zan yi, amma wannan na ƙarshe, ban zan iya yi ba.”
Jakadun kuwa suka koma da wannan labari.
10 Ben-hadad kuwa ya sāke aikawa wurinsa ya ce, “Bari alloli su kashe ni idan ban kai mutane da yawa da za su hallaka Samariya ba.”
11 Sarki Ahab ya amsa, ya ce, “Ku faɗa masa, sojan ainihi, sai ya gama yaƙi sa’an nan ya yi fāriya, amma ba tun kafin a fara ba.”
12 Da Ben-hadad ya ji wannan saƙo sa’ad da yake sha tare da sarakuna a sansani, sai ya ce wa mutanensa, “Kowa ya tsaya a wurinsa.” Sai kowa ya tsaya a wurinsa don yin yaƙi da birnin.
13 Ba da jimawa ba, sai ga annabi ya zo wurin sarki Ahab na Isra’ila, ya ce, “Ubangiji ya ce, ‘Ka ga wannan babban taron sojoji? Zan ba da su a hannunka yau, za ka kuwa sani ni ne Ubangiji.’ ”
14 Ahab ya ce, “Wane ne zai yi jagorar yaƙin?”
Annabin ya ce, “Ubangiji ya ce, sojoji matasa, wato na hakiman larduna, za su yi yaƙin.”
Sarki ya ce, “Wa zai yi jagorar babbar rundunar?”
Annabin ya ce, “Kai ne.”
15 Sai ya tara sojoji matasa na hakiman larduna, mutum ɗari biyu da talatin da biyu. Sa’an nan kuma, ya tara dukan mutanen Isra’ila dubu bakwai (7,000).
16 Suka tafi da tsakar rana sa’ad da Ben-hadad yake a buge da sha a sansani, shi da sarakuna talatin da biyu waɗanda suka taimake shi.
17 Samarin ne suka fara fita. Sai Ben-hadad ya aiki mutane, suka faɗa masa cewa, “Mutane suna zuwa daga Samariya.”
18 Sai ya ce, “Ku kama su da rai, ko sun zo da nufin salama ko da na yaƙi.”
19 Waɗannan kuwa suka fita daga birnin, wato sojoji matasa, rundunar Isra’ilawa kuma tana biye da su,
20 kowa ya kashe abokin gābansa. Suriyawa kuwa suka gudu, Isra’ilawa kuma suka runtume su. Amma Ben-hadad, Sarkin Suriya, ya tsere kan doki tare da mahayan dawakai.
21 Sarkin Isra’ila ya fita, ya ƙwace dawakai da karusai, ya kashe Suriyawa da yawa.
22 Sa’an nan annabin ya je wurin Sarkin Isra’ila, ya ce masa, “Tafi, ka ƙarfafa kanka, ka yi tunani sosai a kan abin da za ka yi, gama da juyawar shekara Sarkin Suriya zai kawo maka yaƙi.”
Suriyawa Sun Kai Yaƙi na Biyu
23 Fādawan Sarkin Suriya suka ce masa, “Allolinsu na tuddai ne, don haka suka fi mu ƙarfi, bari mu yi yaƙi da su a cikin kwari, ta haka za mu ci su ba shakka.
24 Yanzu abin da za ka yi ke nan, sai ka fitar da sarakuna daga matsayinsu, ka sa shugabannin sojoji maimakonsu.
25 Sa’an nan ka tara sojoji kamar yawan waɗanda ka rasa, ka kuma tara dawakai a maimakon na dā, da karusai a maimakon karusai na dā. Mu kuwa za mu yi yaƙi da su a kwari. Ba shakka za mu ci su.”
Sarki Ben-hadad ya ji maganarsu, ya kuwa yi haka nan.
26 Da shekara ta juyo, sai Ben-hadad ya tara Suriyawa, suka haura zuwa Afek don su yi yaƙi da Isra’ilawa.
27 Aka tara mutanen Isra’ila, aka ba su guzuri, suka tafi, su yi yaƙi da Suriyawa. Isra’ilawa suka kafa sansani a gabansu kamar ‘yan garkuna biyu na awaki, amma Suriyawa suka cika ƙasar.
28 Annabin Allah kuwa ya je wurin Sarkin Isra’ila ya ce masa, “Ubangiji ya ce, ‘Tun da yake Suriyawa sun ce, Ubangiji shi Allah na tuddai ne, ba Allah na kwari ba, saboda haka zan ba da dukan wannan taron jama’a a hannunka, za ka sani ni ne Ubangiji.’ ”
29 Suka kafa sansani daura da juna kwana bakwai. A rana ta bakwai ɗin, suka kama yaƙi. Isra’ilawa suka kashe Suriyawa mutum dubu ɗari (100,000) a rana ɗaya.
30 Sauran kuwa suka gudu zuwa birnin Afek. Garun birnin kuma ya fāɗa a kan mutum dubu ashirin da bakwai (27,000) waɗanda suka ragu.
Ben-hadad kuwa ya gudu ya shiga ƙurewar ɗaki, a cikin birnin.
31 Fadawansa suka je suka ce masa, “Mun ji an ce sarakunan Isra’ila masu jinƙai ne, bari mu sa tufafin makoki, mu ɗaura igiyoyi a wuyanmu, sa’an nan mu tafi wurin Sarkin Isra’ila, watakila zai bar ka da rai.”
32 Sai suka sa tufafin makoki, suka ɗaura igiyoyi a wuyansu, suka tafi wurin Sarkin Isra’ila, suka ce, “Baranka, Ben-hadad, yana roƙonka ka bar shi da rai.”
Ahab kuwa ya amsa ya ce, “Har yanzu yana da rai? Ai, shi kamar ɗan’uwana ne.”
33 Da ma abin da fādawan suke so su ji ke nan, sai suka yi sauri, suka karɓi maganar a bakinsa, suka ce, “I, ɗan’uwanka, Ben-hadad.”
Sarki Ahab ya ce musu, “Ku je ku kawo shi.” Ben-hadad kuwa ya zo wurinsa. Ahab ya sa ya shiga tare da shi cikin karusarsa.
34 Ben-hadad ya ce masa, “Biranen da tsohona ya ƙwace daga wurin tsohonka, zan mayar maka. Kai kuma za ka yi karauku a Dimashƙu kamar yadda tsohonka ya yi a Samariya.”
Sai Ahab ya ce, “Zan bar ka, ka tafi a kan wannan sharaɗi.” Ya kuwa yi alkawari da shi, sa’an nan ya bar shi, ya tafi.
Annabi Ya Soki Ahab
35 Ubangiji ya umarci wani daga cikin annabawa ya ce wa abokinsa bisa ga umarnin Ubangiji, “Ina roƙonka ka buge ni.” Abokinsa kuwa ya ƙi ya buge shi.
36 Sai annabin ya ce wa wannan aboki, “Da yake ba ka yi biyayya da muryar Ubangiji ba, da tashinka daga wurina, zaki zai kashe ka.” Da ya tashi daga wurinsa, sai zaki ya gamu da shi, ya kashe shi.
37 Annabin kuma ya tarar da wani mutum, ya ce masa, “Ina roƙonka ka buge ni.” Mutumin kuwa ya buge shi da ƙarfi ya rotsa shi.
38 Sai annabin ya ɓad da kama, ya ɗaure fuskarsa da ƙyalle, ya tafi, ya jira sarki a hanya.
39 Sa’ad da sarki yake wucewa, sai ya kira sarki, ya ce, “Ni baranka na tafi yaƙi, sai ga shi, soja ya kawo mini mutum, ya ce mini, ‘Ka riƙe wannan mutum, kada ka bar shi ya kuɓuta ko da ƙaƙa, idan ka bari ya kuɓuta a bakin ranka, ko kuwa ka biya talanti ɗaya na azurfa.’
40 Da na shiga fama da kai da kawowa sai mutumin ya tsere.”
Sai Sarkin Isra’ila ya ce masa, “Haka shari’arka za ta zama, gama kai da kanka ka yanke shari’ar.”
41 Annabin ya yi saurim, ya kware ƙyallen a fuskarsa, sa’an nan sarki ya gane, ashe, ɗaya daga cikin annabawa ne.
42 Sa’an nan annabin ya ce wa sarki, “Ubangiji ya ce, ‘Da yake ka bar mutumin da na ƙaddara ga mutuwa ya kuɓuta daga hannunka, haka ranka zai zama a maimakon nasa, mutanenka kuwa a maimakon mutanensa.’ ”
43 Sarkin Isra’ila kuwa ya tafi gidansa a Samariya da baƙin ciki.