AFI 4

Ɗayantuwar Ruhu

1 Don haka, ni ɗan sarƙa saboda Ubangiji, ina roƙonku ku yi zaman da ya cancanci kiran da aka yi muku,

2 da matuƙar tawali’u, da salihanci, da haƙuri, kuna jure wa juna saboda ƙauna.

3 Da ƙwazo ku kiyaye ɗayantuwar da Ruhu yake zartarwa, kuna a haɗe a cikin salama.

4 Jiki guda ne, Ruhu kuma guda, kamar yadda aka kira ku a kan begen nan guda, wanda yake game da kiran nan.

5 Ubangiji guda ne, bangaskiya guda, da kuma baftisma guda.

6 Allah ɗaya ne, Ubanmu duka, wanda yake bisa duka, ta wurin duka, a cikin duka kuma.

7 Amma an ba kowannenmu alheri gwargwadon baiwar Almasihu.

8 Saboda haka, Nassi ya ce,

“Sa’ad da ya hau Sama ya bi da rundunar kamammu,

Ya kuma yi wa ‘yan adam baye-baye.”

9 (Wato, da aka ce “ya hau” ɗin, me aka fahimta, in ba cewa dā ya sauka a can ƙasa ba?

10 Shi wanda ya sauka ɗin, shi ne kuma ya hau a can birbishin dukkan sammai, domin yă cika kome.)

11 Ya kuma yi wa waɗansu baiwa su zama manzanni, waɗansu annabawa, waɗansu masu yin bishara, waɗansu makiyaya masu koyarwa,

12 domin tsarkaka su samu, su iya aikin hidimar Ikkilisiya, domin a inganta jikin Almasihu,

13 har mu duka mu riski haɗa kan nan na bangaskiya ga Ɗan Allah, da kuma saninsa, mu kai maƙamin cikakken mutum, mu kuma kai ga matsayin nan na falalar Almasihu.

14 An yi wannan kuwa don kada mu sāke zama kamar yara, waɗanda suke jujjuyawa, iskar kowace koyarwa tana ɗaukar hankalinsu, bisa ga wayon mutane da makircinsu da kissoshinsu.

15 A maimakon haka, sai mu faɗi gaskiya game da ƙauna, muna girma a cikinsa ta kowace hanya, wato Almasihu, shi da yake shugabanmu.

16 Domin ta gare shi ne dukkan jiki yake a game, yake kuma a haɗe, ta wurin gudunmawar kowace gaɓa, ta wurin kuma aikin kowace gaɓa daidai jikin yake ƙara girma, yana kuma ingantuwa da halin ƙauna.

Sabon Rai a Cikin Almasihu

17 To, ina dai faɗa muku, ina kuma nace faɗa muku a cikin Ubangiji, cewa kada ku sāke yin zama irin na al’ummai, masu azancin banza da wofi.

18 Duhun zuciya yake a gare su, bare suke ga rai wanda Allah yake bayarwa, sabili da jahilcin da yake a gare su, saboda taurin kansu.

19 Zuciyarsu ta yi kanta, sun dulmiya a cikin fajirci, sun ɗokanta ido a rufe ga yin kowane irin aikin lalata.

20 Ba haka kuka koyi al’amarin Almasihu ba,

21 in da a ce kun saurare shi, an kuma koya muku ta gare shi ne, wato yadda gaskiya ta Yesu take.

22 Ku yar da halinku na dā, wanda dā kuke a ciki, wanda yake lalacewa saboda sha’awoyinsa na yaudara,

23 ku kuma sabunta ra’ayin hankalinku,

24 ku ɗauki sabon halin nan da aka halitta bisa ga kamannin Allah da hakikanin adalci da tsarki.

25 Saboda haka, sai ku watsar da ƙarya, kowa yă riƙa faɗar gaskiya ga maƙwabcinsa, gama mu gaɓoɓin juna ne.

26 In kun husata, kada ku yi zunubi, kada ma fushinku ya kai faɗuwar rana,

27 kada kuma ku bar wa Iblis wata ƙofa.

28 Kada ɓarawo ya ƙara yin sata, a maimakon haka sai ya motsa jiki yana aikin gaskiya da hannunsa, har da zai sami abin da zai ba matalauta.

29 Kada wata alfasha ta fita daga bakinku, sai dai irin maganar da ta kyautu domin ingantawa, a kuma yi ta a kan kari, domin ta sa alheri ga masu jinta.

30 Ku kuma kula, kada fa ku ɓata wa Ruhu Mai Tsarki na Allah rai, wanda aka hatimce ku da shi, cewa ku nasa ne a ranar fansa.

31 Ku rabu da kowane irin ɗacin rai, da hasala, da fushi, da tankiya, da yanke, da kowace irin ƙeta.

32 Ku yi wa juna kirki, kuna tausayi, kuna yafe wa juna kamar yadda Allah ya yafe muku ta wurin Almasihu.