Gaisuwa
1 Daga Bulus, manzon Almasihu Yesu da yardar Allah, zuwa ga mutanensa tsarkaka da suke a Afisa, amintattu a cikin Almasihu Yesu.
2 Alheri da salama na Allah ubanmu, da na Ubangiji Yesu Almasihu su tabbata a gare ku.
Albarku na Ruhu a Cikin Almasihu
3 Yabo yā tabbata ga Allahn Ubangijinmu Yesu Almasihu, da Ubansa kuma, wanda ya yi mana albarka da kowace albarka ta Ruhu, basamaniya, a cikin Almasihu,
4 domin kuwa ya zaɓe mu a cikin Almasihu tun ba a halicci duniya ba, mu zama tsarkaka, marasa aibu a gabansa.
5 Ya ƙaddara mu mu zama ‘ya’yansa ta wurin Yesu Almasihu, bisa ga nufinsa na alheri,
6 domin mu yabi ɗaukakar alherinsa wanda ya ba mu kyauta hannu sake saboda Ƙaunataccensa.
7 Ta gare shi ne muka sami fansa albarkacin jininsa, wato yafewar laifofinmu, bisa ga yalwar alherin Allah,
8 wanda ya falala mana. Da matuƙar hikima da basira
9 ya sanasshe mu asirin nufinsa, bisa ga kyakkyawan nufinsa da ya nufa ya cika ta wurin Almasihu.
10 Duk wannan kuwa shiri ne, domin a cikar lokaci a harhaɗa dukkan abubuwa ta wurin Almasihu, wato abubuwan da suke sama, da abubuwan da suke a ƙasa.
11 A cikinsa ne aka maishe mu abin gādo na Allah, an kuwa ƙaddara mu ga haka bisa ga nufin wannan da yake zartar da dukkan abubuwa yadda ya yi nufi yă yi,
12 domin mu da muka fara kafa bege ga Almasihu mu yi zaman yabon ɗaukakarsa.
13 A cikinsa ne ku kuma da kuka ji maganar gaskiya, wato, bisharar cetonku, a cikinsa, sa’ad da kuka ba da gaskiya kuma, aka hatimce ku da Ruhu Mai Tsarki wanda aka alkawarta.
14 Shi ne kuwa tabbatawar gādonmu har kafin mu kai ga samunsa, wannan kuma domin yabon ɗaukakarsa ne.
Addu’a don Hikima da Sani
15 Saboda haka da yake na ji labarin bangaskiyarku ga Ubangiji Yesu, da kuma ƙaunarku ga dukan tsarkaka,
16 ban fāsa gode wa Allah saboda ku ba, duk sa’ad da nake yi muku addu’a,
17 da nufin cewa Allah na Ubangijinmu Yesu Almasihu, Uba Maɗaukaki, yă ba ku Ruhu mai ba da hikima da bayani ga sanin Allah,
18 a kuma sa ku ku waye ta idon zuci, domin ku san ko mene ne begen nan da ya kira ku a kai, da kuma ko mene ne yalwar gādonsa mai ɗaukaka a game da tsarkaka,
19 da kuma ko mene ne girman ikonsa marar misaltuwa da yake zartarwa a gare mu, mu masu ba da gaskiya, wato zartarwar ƙarfin ikon nan nasa,
20 wanda ya zartar ga Almasihu sa’ad da ya tashe shi daga matattu, ya kuma ba shi wurin zama a damansa a samaniya,
21 a can a birbishin dukkan sarauta da iko, da ƙarfi, da mulki, a birbishin kowane suna da za a sa, ba ma a duniyar nan kawai ba, har ma a lahira ma.
22 Allah kuma ya sarayar da kome a ƙarƙashin ikon Almasihu, ya kuma ba da shi ga Ikkilisiya ya zama Kai mai mallakar abu duka.
23 Ikkilisiya ita ce jikin Almasihu, cikar mai cika dukkan abu.