Kashedi da Gaisuwa
1 Wannan shi ne zai zama zuwana na uku a gare ku. Lalle ne kuwa a tabbatar da kowace magana a bakin shaidu biyu ko uku.
2 Na gargaɗi waɗanda suka yi zunubi a dā, da kuma saura duka, a yanzu kuma da ba na nan ina yi musu gargaɗi, kamar yadda na yi sa’ad da nake nan a zuwana na biyu, cewa in na sāke zuwa ba zan sawwaƙe musu ba.
3 In dai nema kuke yi ku tabbata, cewa da izinin Almasihu nake magana, to, ai, shi ba rarrauna ba ne a gare ku, amma ƙaƙƙarfa ne a cikinku.
4 Ko da yake an gicciye shi ne da rashin ƙarfi, duk da haka a raye yake ta ikon Allah. Mu ma marasa ƙarfi ne kamarsa, amma a game da al’amuranku da za mu zartar, a raye muke tare da shi, ta ikon Allah.
5 Ku jarraba kanku ku gani, ko har yanzu kuna a raye da bangaskiya. Ku riƙa auna kanku. Ashe, ba ku tabbata Almasihu yana a cikinku ba? Sai ko in kun kasa ga gwajin!
6 Muna fata ku gane, mu ba mu kāsa ba.
7 Amma muna roƙon Allah kada ku yi wani mugun abu, ba don mu mu zama kamar mun ci gwajin kawai ba, sai dai domin ku yi abin da yake daidai, ko da yake za ku ga kamar mun kāsa.
8 Domin ba dama mu sāɓa wa gaskiya, sai dai mu bi bayan gaskiyar.
9 Gama farin ciki muke yi in muna raunana, ku kuna ƙarfafa. Addu’armu ita ce ku kammala.
10 Ina rubuta wannan ne sa’ad da ba na tare da ku, domin sa’ad da na zo, kada ya zama mini tilas in yi muku tsanani a game da nuna ikon nan da Ubangiji ya ba ni saboda ingantawa, ba saboda rushewa ba.
11 Daga ƙarshe kuma, ‘yan’uwa, sai wata rana. Ku kammala halinku. Ku kula da roƙona, ku yi zaman lafiya da juna, ku yi zaman salama, Allah mai zartar da ƙauna da salama kuwa zai kasance a tare da ku.
12 Ku gaggai da juna da tsattsarkar sumba.
13 Dukan tsarkaka suna gaishe ku.
14 Alherin Ubangiji Yesu Almasihu, da ƙaunar Allah, da zumuntar Ruhu Mai Tsarki su tabbata a gare ku duka.