Bayarwa bisa ga Ra’ayi
1 To, ‘yan’uwa, muna so mu sanar da ku alherin Allah da ya bayar a cikin ikilisiyoyin Makidoniya,
2 wato, ko da yake an gwada su da matsananciyar wahala, suna kuma a cikin baƙin talauci, duk da haka, yawan farin cikinsu, har ya kai su ga yin alheri ƙwarai da gaske.
3 Domin na tabbata daidai ƙarfinsu suka bayar, har ma fiye da ƙarfinsu ne, da ra’insu kuma.
4 Sun roƙe mu ƙwarai da gaske mu yi musu alheri su ma, a sa su a cikin masu yi wa tsarkaka gudunmawa,
5 har ma suka bayar fiye da yadda muka zata, amma sai da suka fara miƙa kansu ga Ubangiji da a gare mu kuma, bisa ga nufin Allah.
6 Ganin haka sai muka roƙi Titus, da yake shi ne ya riga ya tsiro da wannan aikin alheri a cikinku, sai yă ƙarasa shi.
7 To, da yake kun fifita a kowane abu, wato, a cikin bangaskiya, da magana, da sani, da matuƙar himma, da kuma ƙaunar da kuke yi mana, to, sai ku fifita a wannan aikin alheri ma.
8 Ba kallafa muku wannan nake yi ba, sai dai ta nuna himmar waɗansu, in tabbata ƙaunarku ma sahihiya ce.
9 Domin kun san alherin Ubangijinmu Yesu Almasihu, ko da yake shi mawadaci ne, sai ya zama matalauci sabili da ku, domin ta wurin talaucinsa ku wadata.
10 A wannan al’amari, ga shawarata. Ai, ya fiye muku a yanzu ku ƙarasa abin da kuka fara yi a bara, har kuka yi da ra’inku.
11 To, sai ku ƙarasa aikin da irin ra’in da kuka fara, gwargwadon ikonku.
12 Domin mutum yana da niyyar bayarwa, bayarwarsa za ta zama abar karɓa ce, bisa ga yawan abin da yake da shi, ba bisa ga abin da ba shi da shi ba.
13 Ba nufi nake yi a sawwaƙe wa waɗansu, ku kuwa a jibga muku nauyin ba.
14 Amma don a raba daidai wa daida, sai ku taimake su a yanzu da yalwarku saboda rashinsu, don wata rana su ma su taimake ku da yalwarsu saboda rashinku, don a daidaita al’amari.
15 Yadda yake a rubuce cewa, “Wanda ya tara mai yawa, bai fi bukatarsa ba, wanda ya tara kaɗan kuwa, ba abin da ya gaza masa.”
Titus da Abokansa
16 Godiya tā tabbata ga Allah wanda ya sa tsananin kula da ku a zuciyar Titus, kamar yadda nake yi.
17 Ba kuwa na’am da roƙonmu kaɗai ya yi ba, har ma saboda tsananin himma tasa yana zuwa wurinku da ra’in kansa.
18 Ga shi, mun aiko ɗan’uwan nan tare da shi, wanda ya yi suna wajen yin bishara a dukan ikilisiyoyi,
19 ba kuwa haka kaɗai ba, har ma ikilisiyoyi sun zaɓe shi ya riƙa tafiya tare da mu kan wannan aikin alheri da muke yi saboda ɗaukakar Ubangiji, da kuma nuna kyakkyawar niyyarmu.
20 Wato, muna gudun kada kowa yă zarge mu a kan kyautan nan da ake yi hannu sake, wadda muke kasaftawa.
21 Niyyarmu ce mu yi abubuwan da suke daidai, ba wai a gaban Ubangiji kaɗai ba, har ma a gaban mutane.
22 Muna kuma aiko da ɗan’uwanmu tare da su, wanda sau da yawa muka tabbatar da himma tasa ta hanya iri iri, yanzu kuma ya fi koyaushe himma, domin amincewa da ku da yake yi ƙwarai da gaske.
23 Titus kuwa, ai, abokin tarayyata ne, abokin aikina kuma game da al’amuranku. ‘Yan’uwan nan namu kuwa, ai, manzanni ne na ikilisiyoyi, masu ɗaukaka Almasihu.
24 Saboda haka sai ku tabbatar wa waɗannan mutane a gaban ikilisiyoyi irin ƙaunarku, da kuma cewa taƙama da ku da muke yi gaskiya ce.