Zunubin Nadab da Abihu
1 ‘Ya’yan Haruna, maza, Nadab da Abihu kuwa kowannensu ya ɗauki faranti ya sa wuta, ya zuba turare a kai, ya miƙa haramtacciyar wuta a gaban Ubangiji, ba irin wadda Ubangiji ya umarta ba.
2 Sai wuta ta fito daga wurin Ubangiji ta kashe su, suka mutu a gaban Ubangiji.
3 Musa kuwa ya ce wa Haruna, “Wannan ita ce ma’anar abin da Ubangiji yake cewa, ‘Dukan waɗanda suke bauta mini, dole su nuna ladabi ga tsarkina, zan kuma bayyana ɗaukakata ga jama’ata.’ ” Haruna kuwa ya yi tsit.
4 Musa ya kirawo Mishayel da Elzafan ‘ya’ya maza na Uzziyel, kawun Haruna, ya ce musu, “Ku zo nan, ku ɗauki gawawwakin ‘yan’uwanku daga gaban wuri mai tsarki zuwa bayan zango.”
5 Sai suka zo, suka kama rigunan matattun suka ɗauke su zuwa bayan zango kamar yadda Musa ya faɗa.
Nawayar Aikin Firist
6 Musa kuma ya ce wa Haruna, da ‘ya’yansa maza, wato, Ele’azara da Itamar, “Kada ku bar gashin kanku barkatai, kada kuma ku kyakketa rigunanku don kada ku mutu, don kada Ubangiji ya yi fushi da taron jama’a duka, amma ‘yan’uwanku, wato, dukan Isra’ilawa, suna iya kuka saboda waɗanda Ubangiji ya ƙone.
7 Kada kuwa ku fita daga cikin alfarwa ta sujada don kada ku mutu, gama an shafa muku man keɓewa na Ubangiji.” Sai suka yi yadda Musa ya faɗa.
Dokoki don Firistoci
8 Ubangiji kuma ya yi magana da Haruna ya ce,
9 “Kada kai da ‘ya’yanka maza ku sha ruwan inabi, ko abin sha mai ƙarfi sa’ad da za ku shiga alfarwa ta sujada don kada ku mutu. Wannan doka ce a dukan zamananku.
10 Sai ku bambanta tsakanin abu mai tsarki da marar tsarki, da tsakanin abin da yake halal da abin da yake haram.
11 Ku kuma koya wa mutanen Isra’ila dukan dokokin da Ubangiji ya ba su ta hannun Musa.”
12 Musa kuwa ya ce wa Haruna da ‘ya’yansa maza, waɗanda suka ragu, wato, Ele’azara da Itamar, “Ku ɗauki ragowar hadaya ta gari wadda aka yi hadaya ta ƙonawa da ita ga Ubangiji, ku ci ba tare da yisti ba a gefen bagaden, gama tsattsarka ne.
13 Za ku ci shi a wuri mai tsarki gama naka rabo ke nan da na ‘ya’yanka maza daga cikin hadayun da akan ƙone da wuta ga Ubangiji, gama haka Ubangiji ya umarce ni.
14 Amma ƙirjin da aka yi hadayar ta kaɗawa da shi da cinyar da aka miƙa, za ka ci su a kowane tsabtataccen wuri, da kai da ‘ya’yanka mata da maza, gama wannan ne rabon da aka ba ku, daga hadayun salama na Isra’ilwa.
15 Za su kawo cinyar hadayar ɗagawa da ƙirjin hadayar kaɗawa tare da kitsen hadayun ƙonawa domin a yi hadaya ta kaɗawa ga Ubangiji. Wannan zai zama rabonka da na ‘ya’yanka har abada kamar yadda Ubangiji ya umarta.”
16 Da Musa ya nemi bunsurun hadaya don zunubi sai ya tarar an ƙone shi. Ya kuwa yi fushi da Ele’azara da Itamar, ‘ya’yan Haruna, maza, waɗanda suka ragu, ya ce,
17 “Don me ba ku ci hadaya don zunubi a wuri mai tsarki ba, da yake tsattsarkan abu ne wanda aka ba ku domin ku kawar da laifin taron jama’a, domin kuma ku yi kafara dominsu a gaban Ubangiji?
18 Ga shi, ba a shigar da jinin can cikin Wuri Mai Tsarki ba. Ga shi kuwa, ya kamata ku ci kamar yadda na umarta amma ba ku yi ba.”
19 Sai Haruna ya ce wa Musa, “Ga shi, yau suka miƙa hadayarsu don zunubi, da ta ƙonawa a gaban Ubangiji, ga kuma irin waɗannan abubuwa da suka same ni, da a ce na ci hadaya don zunubi yau, da zai yi kyau ke nan a gaban Ubangiji?”
20 Da Musa ya ji wannan, sai ya yi na’am da shi.