Bagaden Ƙona Hadaya
1 Ya kuma yi bagaden ƙona hadaya da itacen ƙirya, tsawonsa kamu biyar, fāɗinsa kamu biyar, murabba’i ke nan, tsayinsa kuwa kamu uku.
2 Ya yi masa zankaye a kusurwoyinsa huɗu. Zankayen a haɗe suke da shi. Ya dalaye bagaden da tagulla.
3 Da tagulla ya yi duk kayayyakin bagaden, da kwanoni, da babban cokali, da daruna, da cokula masu yatsotsi, da farantan wuta.
4 Ya yi wa bagaden raga da tagulla, ya sa ta a tsakiya.
5 Ya sa ƙawane huɗu a kusurwoyi huɗu na ragar tagulla don zura sanduna.
6 Ya kuma yi sanduna da itacen ƙirya, ya dalaye su da tagulla.
7 Sai ya zura sandunan cikin ƙawane na gyaffan bagaden don ɗaukarsa. Ya yi bagaden da itace sa’an nan ya robe cikinsa.
Yin Daron Wanka
8 Ya yi daron wanka da tagulla, da gammonsa na tagulla, daga madubai na mata masu yin aiki a ƙofar alfarwa ta sujada.
Farfajiyar Alfarwa ta Sujada
9 Ya kuma yi farfajiya. Ya yi labulenta na gefen kudu da lallausan zaren lilin, tsawonsu kamu ɗari ne.
10 Da tagulla aka yi dirkokinsa ashirin, da kwasfan dirkoki guda ashirin, amma da azurfa aka yi maratayan dirkoki da maɗaurai.
11 Tsawon labule na wajen gefen arewa kamu ɗari ne. An yi dirkokinsa guda ashirin da kwasfansu ashirin da tagulla, amma an yi maratayan dirkoki da maɗaurai da azurfa.
12 Labule na gefen yamma kamu hamsin ne, dirkokinsa kuwa guda goma ne, da kwasfansu guda goma. An yi maratayan dirkoki, da maɗaurai da azurfa.
13 Tsawon gefen gabas kamu hamsin ne.
14 Labule na gefe ɗaya na ƙofar, kamu goma sha biyar ne, da dirkokinsu guda uku da kwasfan dirkoki guda uku.
15 Akwai kuma labule mai kamu goma sha biyar a gefe biyu na ƙofar farfajiyar. Labulen yana da dirkoki guda uku da kwasfan dirkoki guda uku.
16 Duk labulen da yake kewaye da farfajiya an yi shi da lallausan zaren lilin.
17 An yi kwasfan dirkoki duka da tagulla, amma maratayan dirkoki da maɗauransu an yi su da azurfa. An dalaye kawunansu da azurfa. Dirkokin farfajiya duka suna da maɗaurai na azurfa.
18 An yi wa labulen ƙofar farfajiya ado na ɗinki da na shuɗi, da na shunayya, da na mulufi, da na lallausan zaren lilin. Tsawonsa kamu ashirin, tsayinsa kamu biyar daidai da labulen farfajiya.
19 An yi dirkokin labulen guda huɗu, da kwasfan dirkoki guda huɗu da tagulla, amma da azurfa aka yi maratayan dirkokin. An dalaye kawunansu da maɗauransu da azurfa.
20 An yi turakun alfarwa ta sujada da na farfajiya duka da tagulla.
Ƙarafan da aka yi Amfani da Su
21 Wannan shi ne lissafin abubuwan da aka yi alfarwa ta sujada da su, yadda aka lasafta bisa ga umarnin Musa domin aikin Lawiyawa a ƙarƙashin jagorar Itamar, ɗan Haruna firist.
22 Sai Bezalel ɗan Uri, ɗan Hur, na kabilar Yahuza, ya yi dukan abin da Ubangiji ya umarci Musa.
23 Tare da shi kuma ga Oholiyab ɗan Ahisamak na kabilar Dan, gwani ne cikin aikin zāne-zāne, da ɗinki na shuɗi, da na shunayya, da na mulufi, da na lallausan zaren lilin.
24 Dukan zinariya da aka yi aikace-aikacen da ita na alfarwa ta sujada sadaka ce talanti ashirin da tara ne da shekel ɗari bakwai da talatin bisa ga ma’aunin kuɗin da ake aiki da shi.
25 Azurfar da aka samu daga ƙidayar taron jama’a talanti ɗari ne, da shekel dubu ɗaya da ɗari bakwai da saba’in da biyar (1,775) bisa ga ma’aunin kuɗin da ake aiki da shi.
26 Kowane mutum da aka ƙidaya ya ba da rabin shekel. Duk mai shekara ashirin ko fi an ƙidaya shi, aka sami maza dubu ɗari shida da dubu uku da ɗari biyar da hamsin (603,550).
27 An mori azurfa talanti ɗari don yin kwasfa na alfarwa, da kwasfa na labule. An yi kwasfa ɗari da azurfa talanti ɗari, wato kwasfa ɗaya talanti ɗaya ke nan.
28 An yi maratayan dirkoki da azurfa shekel dubu ɗaya da ɗari bakwai da saba’in da biyar (1,775), sa’an nan an dalaye kawunansu, an kuma yi musu maɗaurai.
29 Tagullar da aka bayar kuwa, talanti saba’in da shekel dubu biyu da ɗari huɗu (2,400).
30 Da tagullar ce ya yi kwasfan ƙofar alfarwa ta sujada, da bagade, da ragarsa, da dukan kayayyakin bagaden.
31 Da tagullar kuma aka yi kwasfan farfajiya, da kwasfan ƙofar farfajiya, da dukan turakun alfarwar da na farfajiyar.