Tufafin Firistoci
1 “Daga cikin ‘ya’ya maza na Isra’ila sai ka kirawo ɗan’uwanka Haruna tare da ‘ya’yansa, Nadab, da Abihu, da Ele’azara, da Itamar, su zama firistoci masu yi mini aiki.
2 A ɗinka wa Haruna ɗan’uwanka, tufafi masu tsarki domin daraja da kwarjini.
3 Ka kuma yi magana da gwanayen sana’a duka waɗanda na ba su fasaha, don su ɗinka wa Haruna tufafi, gama za a keɓe shi ya zama firist ɗina.
4 Waɗannan su ne irin tufafin da za su ɗinka, ƙyallen maƙalawa a ƙirji, da falmaran, da taguwa, da zilaika, da rawani, da abin ɗamara. Za su yi wa ɗan’uwanka, Haruna, da ‘ya’yansa tufafi tsarkaka, don su zama firistoci masu yi mini aiki.
5 Sai su yi amfani da zinariya, da shuɗi, da shunayya, da mulufi, da lallausan zaren lilin.
6 “Za su yi falmaran da zinariya, da shuɗi, da shunayya da mulufi, da lallausan zaren lilin, aikin gwani.
7 Za a yi mata kafaɗa biyu, sa’an nan a haɗa su a karbunsu.
8 Za a yi mata abin ɗamara da irin kayan da aka yi falmaran, wato da zinariya, da shuɗi, da shunayya, da mulufi, da lallausan zaren lilin. Za a yi mata saƙar gwaninta.
9 A kuma ɗauki duwatsu biyu masu daraja, a zana sunayen ‘ya’yan Isra’ila a kai.
10 Sunaye shida a kowane dutse bi da bi bisa ga haihuwarsu.
11 Za a zana sunayen ‘ya’yan Isra’ila a bisa duwatsun nan kamar yadda mai yin aiki da lu’ulu’u yakan zana hatimai. Za a sa kowane dutse a cikin tsaiko na zinariya.
12 A sa duwatsun a kafaɗun falmaran domin a riƙa tunawa da ‘ya’yan Isra’ila. Haruna zai rataya sunayensu a kafaɗunsa a gaban Ubangiji domin a tuna da su.
13 Za ku yi tsaiko biyu na zinariya,
14 ku kuma yi tukakkun sarƙoki biyu na zinariya tsantsa. Za ku ɗaura wa tsaikunan nan tukakkun sarƙoƙi.
15 “Ku kuma yi ƙyallen maƙalawa a ƙirji domin neman nufin Allah. Sai a saƙa shi da gwaninta kamar yadda aka saƙa falmaran ɗin. A saƙa shi da zinariya, da shuɗi, da shunayya, da mulufi, da lallausan zaren lilin.
16 Ƙyallen maƙalawa a ƙirji zai zama murabba’i, a ninke shi biyu tsawonsa da fāɗinsa su zama kamu ɗaya ɗaya.
17 Sai a yi jeri huɗu na duwatsun a kanta. A jeri na fari, a sa yakutu, da tofaz, da zumurrudu.
18 A jeri na biyu, a sa turkos, da saffir, da daimon.
19 A jeri na uku, a sa yakinta, da idon mage, da ametis.
20 A jeri na huɗu, a sa beril, da onis, da yasfa. Za a sa su cikin tsaiko na zinariya.
21 A bisa duwatsun nan goma sha biyu, sai a zana sunayen ‘ya’yan Isra’ila bisa ga kabilansu goma sha biyu. Za a zana sunayen kamar hatimi.
22 Ku kuma yi wa ƙyallen maƙalawa a ƙirji tukakkun sarƙoƙi na zinariya tsantsa.
23 Za ku yi ƙawanya biyu na zinariya, ku sa su a gefe biyu na ƙyallen maƙalawa a ƙirji.
24 Ku sa tukakkun sarkoƙin nan biyu na zinariya a cikin ƙawanya biyu na zinariya da suke a gyaffan ƙyallen maƙalawa a ƙirji, a haɗa su daga gaba a kafaɗun falmaran.
25 Za ku kuma sa sauran bakunan sarƙoƙin nan biyu a cikin tsaikuna, sa’an nan a sa shi a gaban kafaɗun falmaran.
26 Ku kuma yi waɗansu ƙawane na zinariya, a sa su a sauran kusurwoyi na ƙyallen maƙalawa a ƙirji, a gefe na cikin da yake manne da falmaran.
27 Ku kuma yi waɗansu ƙawanya biyu na zinariya, a sa su a ƙashiyar kafaɗu biyu na falmaran daga gaba, a sama da abin ɗamaran nan.
28 Za su ɗaure ƙyallen maƙalawa a ƙirji a ƙawanensa haɗe da ƙawanen falmaran da shuɗiyar igiya domin ƙyallen maƙalawa a ƙirji ya zauna bisa abin ɗamarar falmaran, don kuma kada ya yi sako-sako a bisa falmaran.
29 Duk sa’ad da Haruna zai shiga Wuri Mai Tsarki, zai ɗauki sunayen ‘ya’yan Isra’ila a gaban Ubangiji kullum, a kan ƙyallen maƙalawa domin nemar musu nufin Allah.
30 Za ku kuma sa Urim da Tummin a kan ƙyallen maƙalawar domin su kasance a zuciyar Haruna sa’ad da ya shiga gaban Ubangiji. Haka kuwa kullum Haruna zai riƙa kai kokekoken Isra’ilawa a gaban Ubangiji.
31 “Sai ku yi taguwar falmaran da shuɗi duka.
32 Za a yanke wuya a tsakiyarta don sawa. A yi wa wuyan shafi, sa’an nan a yi wa wuyan basitsa, wato cin wuya, domin kada ya kece.
33 Za a yi wa karbun taguwar ado da fasalin ‘ya’yan rumman masu launin shuɗi, da shunayya, da mulufi. A sa ƙararrawa ta zinariya a tsakankaninsu.
34 Za a jera su bi da bi, wato ‘ya’yan rumman na biye da ƙararrawar zinariya.
35 Sai Haruna ya sa taguwar sa’ad da yake aiki. Za a ji ƙarar ƙararrawar a lokacin da yake shiga da lokacin da yake fita Wuri Mai Tsarki a gaban Ubangiji don kada ya mutu.
36 “Sai kuma a yi allo na zinariya tsantsa, a zana rubutu irin na hatimi a kansa haka, ‘MAI TSARKI GA UBANGIJI.’
37 Sai a ɗaura shi da shuɗiyar igiya a rawanin daga gaba.
38 Haruna kuwa zai sa shi bisa goshinsa, ta haka zai ɗauki kurakuran da ya yiwu Isra’ilawa sun yi cikin miƙa sadakokinsu masu tsarki. Kullum Haruna zai riƙa sa shi bisa goshinsa don su zama karɓaɓɓu ga Ubangiji.
39 “Ku saƙa zilaika da lallausan zaren lilin. Ku yi rawani da lallausan zaren lilin, ku kuma saƙa abin ɗamara mai ado.
40 “Za a yi wa ‘ya’yan Haruna, maza, zilaiku, da abubuwan ɗamara, da huluna don daraja da kwarjini.
41 Ka sa wa Haruna, ɗan’uwanka, da ‘ya’yansa maza, sa’an nan ka zuba musu mai, ka keɓe su, ka tsarkake su domin su zama firistoci masu yi mini aiki.
42 Sai kuma ku yi musu mukurai na lilin don su rufe tsiraicinsu daga kwankwaso zuwa cinya.
43 Haruna da ‘ya’yansa maza za su sa su sa’ad da suke shiga alfarwa ta sujada ko kuwa sa’ad da suka kusaci bagade domin su yi aiki cikin Wuri Mai Tsarki domin kada su yi laifin da zai zama sanadin mutuwarsu. Wannan zai zama doka ga Haruna da zuriyarsa har abada.”