Alfarwa, Wato Wurin da Allah Zai Zauna
1 “Alfarwar kanta, za ku yi ta da labule goma na lilin mai laushi ninki biyu, da ulu mai launi shuɗi, da launi shunayya da launi ja. Waɗannan labule za a yi musu zānen siffofin kerubobi, aikin gwani.
2 Tsawon kowane labule zai zama kamu ashirin da takwas, fāɗinsa kuwa kamu huɗu. Labulen su zama daidai wa daida.
3 Labule biyar biyar, za a harhaɗa, a ɗinka.
4 Ku kuma yi wa labulen nan biyu hantuna na shuɗi a karbunsu na bisa.
5 Za ku yi wa kowane labule hantuna hamsin. Hantunan labulen nan biyu su yi daura da juna.
6 Za ku yi maɗauri guda hamsin da zinariya don a haɗa hantuna na labulen nan domin alfarwa ta zama ɗaya.
7 “Ku yi labule goma sha ɗaya da gashin awaki, da za ku rufe alfarwar da shi.
8 Tsawon kowanne zai zama kamu talatin, fāɗinsa kamu huɗu. Labulen za su zama daidai wa daida.
9 Za ku harhaɗa biyar ku ɗinka. Haka kuma za ku yi da sauran shidan. Ku ninka na shida riɓi biyu, ku yi labulen ƙofar alfarwa da shi.
10 Za ku kuma sa hantuna hamsin a karbun labulen daga bisa. Haka nan kuma za a sa hantuna hamsin a karbun ɗayan.
11 Sa’an nan ku yi maɗauri hamsin da tagulla, ku ɗaura hantunan da su don ku haɗa alfarwar ta zama ɗaya.
12 Ragowar rabin labulen da yake a bisa alfarwar, sai a bar shi yana reto a bayan alfarwar.
13 Kamu ɗayan da ya ragu a kowane gefe na tsawon, sai a bar shi yana reto a kowane gefe domin ya rufe alfarwar.
14 Za ku yi abin rufe alfarwa da fatun raguna da aka rina ja, za ku kuma yi wani abin rufewa da fatun da aka jeme.
15 “Za ku yi alfarwar da katakon itacen ƙirya. Za ku kakkafa su a tsaye.
16 Tsawon kowane katako zai zama kamu goma, fāɗinsa kamu ɗaya da rabi.
17 Za a fiƙe kan kowane katako. Haka za ku yi da dukan katakan.
18 Za ku shirya katakan alfarwa kamar haka, katakai ashirin wajen gefen kudu.
19 Ku kuma yi kwasfa arba’in da azurfa da za a sa wa katakan nan ashirin. Za a sa kawunan katakan da aka fiƙe a cikin kwasfa.
20 Za ku kuma kafa katakai ashirin wajen gefen arewa na alfarwar.
21 Haka kuma za ku yi kwasfa arba’in da azurfa dominsu. Kwasfa biyu domin kowane katako.
22 A wajen yamma ga alfarwa kuma ku kafa katakai shida.
23 Ku kuma sa katakai biyu a kowace kusurwa ta yamma a alfarwa.
24 Katakan nan kuwa, sai a haɗa su daga ƙasa zuwa sama, a ɗaure. Haka za a yi da katakan kusurwan nan biyu. Za su zama na kusurwa biyu.
25 Za a sami katakai takwas da kwasfansu na azurfa guda goma sha shida, kowane katako yana da kwasfa biyu.
26 “Sai ku yi sanduna da itacen ƙirya. Sanduna biyar domin katakai na gefe ɗaya.
27 Biyar kuma domin katakai na wancan gefe. Har yanzu kuma biyar domin katakai na gefen yamma.
28 Sandan da yake tsakiyar katakan zai bi daga wannan gefe zuwa ƙarshen wancan gefe.
29 Za ku dalaye katakan da zinariya, ku kuma yi musu ƙawanen zinariya inda za a sa sandunan. Za ku dalaye sanduna kuma da zinariya.
30 Ta haka za ku yi alfarwar bisa ga fasalin da aka nuna maka a bisa dutsen.
31 “Za ku yi labule da lallausan zaren lilin, mai launin shuɗi, da shunayya, da mulufi. A yi shi da gwaninta, a zana siffofin kerubobi a kansa.
32 Ku rataye shi a bisa dirkoki huɗu nan itacen ƙirya waɗanda aka dalaye da zinariya, da maratayansu na zinariya waɗanda aka sa cikin kwasfa huɗu na azurfa.
33 Za ku sa labulen a ƙarƙashin maɗauran, sa’an nan ku shigar da akwatin alkawari a bayan labulen. Labulen zai raba tsakanin Wuri Mai Tsarki da Wuri Mafi Tsarki.
34 Ku sa murfin a bisa akwatin alkawari a Wuri Mafi Tsarki.
35 Sai ku sa teburin a gaban labulen wajen arewa, ku kuma sa alkukin a kudancin alfarwar daura da teburin.
36 Haka nan kuma za ku yi wa ƙofar alfarwa makari da lallausan zaren lilin mai launin shuɗi, da shunayya, da mulufi, aikin mai gwaninta.
37 Ku yi dirkoki biyar da itacen ƙirya saboda makarin, ku dalaye su da zinariya. Ku kuma yi maratayansu da zinariya. Ku yi wa waɗannan dirkoki kwasfa biyar da tagulla.”