Yetro Ya Ziyarci Musa
1 Yetro, firist na Madayana, surukin Musa, ya ji dukan abin da Allah ya yi wa jama’arsa, wato Musa da Isra’ilawa, yadda Ubangiji ya fito da su daga Masar.
2 Ya kawo Ziffora matar Musa, wadda Musa ya aika da ita gida.
3 Yetro kuma ya kawo ‘ya’yanta biyu maza, Gershom da Eliyezer tare da ita. Gama Musa ya ce, “Ni baƙo ne a baƙuwar ƙasa.” Saboda haka ne ya raɗa wa ɗaya daga cikin ‘ya’yansa, suna, Gershom.
4 Ya kuma ce, “Allah na ubanan shi ne ya taimake ni, ya cece ni daga takobin Fir’auna,” saboda haka ya raɗa wa ɗayan, suna, Eliyezer.
5 Sai Yetro ya kawo wa Musa ‘ya’yansa maza da matarsa a cikin jeji inda suka yi zango kusa da dutsen Allah.
6 Aka faɗa wa Musa, “Ga surukinka, Yetro, yana zuwa wurinka da matarka da ‘ya’yanta biyu tare da ita.”
7 Musa kuwa ya fita ya marabce shi, ya sunkuya, ya sumbace shi. Suka gaisa, suka tambayi lafiyar juna, sa’an nan suka shiga alfarwa.
8 Sai Musa ya faɗa wa surukinsa dukan abin da Ubangiji ya yi da Fir’auna da Masarawa saboda Isra’ilawa, ya kuma faɗa masa dukan wahalar da suka sha a kan hanya, da yadda Ubangiji ya cece su.
9 Yetro kuwa ya yi murna saboda alherin da Ubangiji ya yi wa Isra’ilawa da yadda ya cece su daga hannun Masarawa.
10 Yetro kuma ya ce, “Yabo ya tabbata ga Ubangiji wanda ya cece ku daga hannun Masarawa da Fir’auna, wanda kuma ya ceci jama’arsa daga bautar Masarawa.
11 Yanzu na sani Ubangiji yake gāba da sauran alloli duka, gama ya ceci Isra’ilawa daga tsanantawar da Masarawa suka yi musu.”
12 Yetro, surukin Musa kuwa, ya miƙa hadaya ta ƙonawa da sadaka ga Allah. Sai Haruna ya zo tare da dattawan Isra’ila duka don su ci abinci tare da surukin Musa a gaban Allah.
13 Kashegari da Musa ya zauna garin yi wa jama’ar shari’a, mutane suka kekkewaye shi tun dage safiya har zuwa yamma.
14 Da surukin Musa ya ga yadda Musa yake fama da jama’a, sai ya ce, “Mene ne wannan da kake yi wa jama’a? Don me kake zaune kai kaɗai, mutane kuwa na tsattsaye kewaye da kai, tun daga safe har zuwa maraice?”
15 Sai Musa ya ce wa surukinsa, “Mutane suna zuwa wurina ne domin su san faɗar Allah.
16 A sa’ad da suke da wata matsala sukan zo wurina, ni kuwa nakan daidaita tsakanin mutum da maƙwabcinsa, nakan kuma koya musu dokokin Allah da umarnansa.”
17 Amma surukin Musa ya ce, “Abin nan da kake yi ba daidai ba ne.
18 Kai da jama’an nan da suke tare da kai za ku rafke, saboda abin da kake yi ya fi ƙarfinka, kai kaɗai ba za ka iya ba.
19 Yanzu sai ka saurari maganata, zan ba ka shawara, Allah kuwa ya kasance tare da kai. Za ka wakilci jama’a a gaban Allah, ka kai matsalolinsu gare shi.
20 Ka koya musu dokokin da umarnan, ka nuna musu hanyar da ya kamata su yi.
21 Ka kuma zaɓa daga cikin jama’a isassun mutane, masu tsoron Allah, amintattu, waɗanda suke ƙyamar cin hanci. Ka naɗa su shugabannin jama’a na dubu dubu da na ɗari ɗari, da na hamsin hamsin, da na goma goma.
22 Za su yi wa mutane shari’a koyaushe, amma kowace babbar matsala sai su kawo maka, ƙaramar matsala kuwa su yanke da kansu. Da haka za su ɗauki nauyin jama’a tare da kai don ya yi maka sauƙi.
23 In ka bi wannan shawara, in kuma Allah ya umarce ka da yin haka, za ka iya ɗaukar nawayar jama’ar. Mutane duka kuwa za su yi zamansu lafiya.”
24 Musa kuwa ya saurari maganar surukinsa, ya yi abin da ya ce duka.
25 Sai Musa ya zaɓi isassun mutane daga cikin Isra’ilawa ya naɗa su shugabannin jama’a na dubu dubu, da na ɗari ɗari, da na hamsin hamsin, da na goma goma.
26 Suka yi ta yi wa jama’a duka shari’a kullayaumin, amma matsaloli masu wuya sukan kawo wa Musa, ƙananan kuwa sukan yanke da kansu.
27 Sa’an nan Musa ya sallami surukinsa, ya koma garinsu.