Ruwa daga Dutse
1 Dukan taron jama’ar Isra’ila suka tashi daga jejin Sin, suna tafiya daga zango zuwa zango bisa ga umarnin Ubangiji. Suka yi zango a Refidim, amma ba ruwan da jama’a za su sha.
2 Domin haka jama’a suka zargi Musa suka ce, “Ba mu ruwa, mu sha.”
Musa ya amsa musu ya ce, “Don me kuke zargina? Don me kuke gwada Ubangiji?”
3 Amma jama’a suna fama da ƙishirwa, suka yi wa Musa gunaguni. Suka ce, “Don me ka fito da mu daga Masar? Ashe, domin ka kashe mu ne, da mu, da ‘ya’yanmu, da dabbobinmu da ƙishi?”
4 Sai Musa ya yi roƙo ga Ubangiji, ya ce, “Me zan yi wa jama’an nan? Ga shi, saura kaɗan su jajjefe ni da duwatsu.”
5 Ubangiji kuwa ya ce wa Musa, “Ɗauki waɗansu dattawa daga cikin jama’ar Isra’ila, ka wuce a gaban jama’ar. Ka kuma ɗauki sandanka wanda ka bugi Nilu da shi, ka tafi.
6 Zan tsaya a dutsen Horeb can a gabanka. Za ka bugi dutsen, ruwa kuwa zai fito domin jama’a su sha.” Musa kuma ya yi haka nan a gaban dattawan Isra’ila.
7 Sai aka sa wa wurin suna, “Masaha” da “Meriba”, saboda Isra’ilawa suka yi husuma, suka kuma jarraba Ubangiji suna cewa, “Ubangiji yana tare da mu, ko babu?”
Yaƙi da Amalekawa
8 Amalekawa suka zo su yi yaƙi da Isra’ilawa a Refidim.
9 Sai Musa ya ce wa Joshuwa, “Zaɓo mana mutane, ka fita ka yi yaƙi da Amalekawa gobe. Zan tsaya a bisa dutsen da sandan mu’ujiza a hannuna.”
10 Joshuwa kuwa ya yi yadda Musa ya faɗa masa, ya fita ya yi yaƙi da Amalekawa. Musa, da Haruna, da Hur kuma suka hau kan dutsen.
11 Muddin hannun Musa na miƙe, sai Isra’ilawa su yi ta cin nasara, amma da zarar hannunsa ya sauka, sai Amalekawa su yi ta cin nasara.
12 Sa’ad da hannuwan Musa suka gaji, Haruna da Hur suka ɗauki dutse suka ajiye wa Musa, ya zauna a kai, su kuwa suka tsaya a gefen damansa da hagunsa suna tallabe da hannunsa sama, suka tallabe su har faɗuwar rana.
13 Joshuwa kuwa ya ragargaza rundunar Amalekawa da takobi.
14 Ubangiji ya ce wa Musa, “Rubuta wannan a littafi domin a tuna da shi, ka kuma faɗa wa Joshuwa zan shafe Amalekawa ɗungum.”
15 Sai Musa ya gina bagade ya sa masa suna, Yahweh Nissi, wato Ubangiji ne tutarmu.
16 Ya ce, “Ubangiji ya tabbata zai yaƙi Amalekawa har abada.”