Manna da Makware
1 Taron jama’ar Isra’ila suka tashi daga Elim suka shiga jejin Sin wanda yake tsakanin Elim da Sina’i, a rana ta goma sha biyar ga watan biyu bayan fitowarsu daga ƙasar Masar.
2 Sai dukan taron jama’ar Isra’ilawa suka yi wa Musa da Haruna gunaguni cikin jejin, suka ce musu,
3 “Da ma mun mutu ta ikon Ubangiji a ƙasar Masar lokacin da muka zauna kusa da tukwanen nama, muka ci abinci muka ƙoshi. Ga shi, kun fito da mu zuwa cikin jeji don ku kashe dukan wannan taro da yunwa.”
4 Ubangiji kuwa ya ce wa Musa, “Ga shi, zan sauko muku da abinci daga sama. A kowace rana jama’a za su fita su tattara abin da zai ishe su a yini, da haka zan gwada su, ko za su kiyaye maganata, ko babu.
5 A kan rana ta shida, sai su ninka abin da suka saba tattarawa na kowace rana, su shirya shi.”
6 Musa da Haruna kuwa suka ce wa Isra’ilawa, “Da yamma za ku sani Ubangiji ne ya fisshe ku daga ƙasar Masar.
7 Da safe za ku ga ɗaukakar Ubangiji, gama ya ji gunagunin da kuka yi a kansa, gama wane, mu, da za ku yi gunaguni a kanmu?”
8 Musa ya kuma ce, “Da yamma Ubangiji zai ba ku nama ku ci, da safe kuwa zai ƙosar da ku da abinci, gama Ubangiji ya riga ya ji irin gunagunin da kuka yi a kansa. Ai, gunagunin ba a kanmu yake ba, wane mu? A kan Ubangiji ne kuka yi.”
9 Musa ya ce wa Haruna, “Faɗa wa taron jama’ar Isra’ila, su matso nan a gaban Ubangiji, gama ya ji gunaguninsu.”
10 Sa’ad da Haruna yake magana da taron jama’ar, suka duba wajen jeji, sai ga ɗaukakar Ubangiji ta bayyana a cikin girgije.
11 Ubangiji kuwa ya yi magana da Musa ya ce,
12 “Na ji gunagunin Isra’ilawa, amma ka faɗa musu cewa, ‘A tsakanin faɗuwar rana da almuru, za ku ci nama, da safe za ku kuma ƙoshi da abinci. Sa’an nan za ku sani, ni Ubangiji Allahnku ne.”’
13 Da maraice makware suka zo suka rufe zangon, da safe kuma raɓa ta kewaye zangon.
14 Sa’ad da raɓar ta kaɗe, sai ga wani abu tsaki-tsaki mai laushi, fari, kamar hazo a ƙasa.
15 Sa’ad da Isra’ilawa suka gan shi, suka ce wa junansu, “Manna,” wato “Mece ce wannan?” Gama ba su san irinta ba.
Musa kuwa ya ce musu, “Wannan ita ce abincin da Ubangiji ya ba ku, ku ci.
16 Abin da Ubangiji ya umarta ke nan, kowannenku ya tattara wadda ta ishe shi ci, kowa ya sami mudu daidai bisa ga yawan mutanen da yake cikin kowace alfarwa.”
17 Isra’ilawa suka yi haka nan, suka tattara, waɗansu suka zarce, waɗansu kuma ba su kai ba.
18 Amma da aka auna da mudu, ta waɗanda suka zarce ba ta yi saura ba, ta waɗanda ba su kai ba, ba ta gaza ba. Kowane mutum ya tattara daidai cinsa.
19 Musa ya ce musu, “Kada wani ya ci, ya bar saura har safiya.”
20 Amma waɗansu ba su kasa kunne ga Musa ba, suka bar saura, har ta kwana, kashegari kuwa ta yi tsutsotsi, ta ruɓe, sai Musa ya yi fushi da su.
21 Kowace safiya sukan tattara ta, kowa gwargwadon cinsa, amma da rana ta yi zafi sai manna ɗin ta narke.
22 A kan rana ta shida suka tattara biyu ɗin abin da suka saba, kowane mutum mudu biyu biyu. Sai shugabannin taron suka zo suka faɗa wa Musa.
23 Shi kuwa ya ce, “Ga abin da Ubangiji ya umarta, ‘Gobe ranar hutawa ce ta saduda, Asabar ce, tsattsarka ga Ubangiji. Ku toya abin da za ku toya, ku kuma dafa abin da za ku dafa. Abin da kuka ci kuka rage, ku ajiye don gobe.”’
24 Suka ajiye har gobe kamar yadda Musa ya umarta, amma ba ta yi ɗoyi ba, ba ta kuwa yi tsutsotsi ba.
25 Sai Musa ya ce, “Ita za ku ci yau, gama yau Asabar ce ga Ubangiji. Yau ba za ku same ta a saura ba.
26 Kwana shida za ku tattara ta, amma a rana ta bakwai wadda take asabar, ba za a iske kome ba.”
27 Amma a rana ta bakwai ɗin waɗansu mutane suka tafi don su tattara, ba su kuwa sami kome ba.
28 Sai Ubangiji ya ce wa Musa, “Har yaushe za ku ƙi kiyaye dokokina da umarnaina?
29 Lura fa, Ubangiji ne ya ba ku ranar Asabar, domin haka a rana ta shida yakan ba ku abinci na kwana biyu. Kowanne ya yi zamansa a inda yake. Kada kowa ya bar inda yake a rana ta bakwai ɗin.”
30 Sai jama’a suka huta a rana ta bakwai.
31 Isra’ilawa kuwa suka sa wa wannan abinci suna, Manna. Manna wata irin tsaba ce kamar farin riɗi. Ɗanɗanarta kuwa kamar waina ce da aka yi da zuma.
32 Sai Musa ya ce, “Ubangiji ya umarta a cika mudu da ita, a adana ta dukan zamananku domin kowane zamani a ga irin abincin da ya ciyar da ku cikin jeji lokacin da ya fito da ku daga ƙasar Masar.”
33 Sai Musa ya ce wa Haruna, “Ɗauki tukunya, ka zuba mudu guda na manna a ciki, ka ajiye a gaban Ubangiji, a adana har dukan zamananku.”
34 Kamar yadda Ubangiji ya umarci Musa, haka Haruna ya ajiye ta a gaban akwatin alkawari domin kiyayewa.
35 Shekara arba’in Isra’ilawa suka yi suna cin manna, har suka kai ƙasar da take da mutane, suka ci manna, har zuwa kan iyakar ƙasar Kan’ana.
36 Mudu ɗaya humushin garwa ɗaya ta gari.