FIT 7

1 Ubangiji ya ce wa Musa, “Duba, zan maishe ka kamar Allah ga Fir’auna. Ɗan’uwanka, Haruna kuwa, zai zama manzonka.

2 Kai za ka faɗa wa Haruna, ɗan’uwanka, dukan abin da na umarce ka, shi kuwa zai faɗa wa Fir’auna ya bar Isra’ilawa su fita ƙasa tasa.

3 Amma zan taurare zuciyar Fir’auna don in aikata alamu da mu’ujizai cikin ƙasar Masar.

4 Amma Fir’auna ba zai kasa kunne gare ku ba, don haka zan miƙa hannuna a bisa Masar, zan fitar da rundunar jama’ata, wato Isra’ilawa, daga ƙasar Masar ta wurin hukuntaina masu iko.

5 Masarawa kuma za su sani ni ne Ubangiji sa’ad da na miƙa hannuna gāba da Masar, don in fito da Isra’ilawa daga tsakiyarsu.”

6 Musa da Haruna suka yi yadda Ubangiji ya umarce su.

7 Musa yana da shekara tamanin, Haruna kuwa yana da shekara tamanin da uku sa’ad da suka yi magana da Fir’auna.

Sandan Haruna

8 Sai Ubangiji ya ce wa Musa da Haruna,

9 “Idan Fir’auna ya ce muku, ‘Aikata waɗansu al’ajabai don ku nuna isarku,’ sai ka faɗa wa Haruna ya ɗauki sandansa, ya jefa shi ƙasa a gaban Fir’auna. Sandan kuwa zai zama maciji.”

10 Sai Musa da Haruna suka tafi wurin Fir’auna, suka yi yadda Ubangiji ya umarce su. Haruna ya jefa sandansa a gaban Fir’auna. Da sandan ya fāɗi, sai ya zama maciji.

11 Fir’auna kuwa ya kirawo shahararrun malamai, da masu sihiri, su kuma su yi haka ta wurin sihirinsu na Masarawa.

12 Kowannensu ya jefa sandansa ƙasa, sai sandunan suka zama macizai. Amma sandan Haruna ya haɗiye sandunansu.

13 Duk da haka zuciyar Fir’auna ta taurare kamar yadda Ubangiji ya riga ya faɗa.

Annobar Jini

14 Sai Ubangiji ya ce wa Musa, “Fir’auna yana da taurin zuciya, ga shi, ya ƙi sakin jama’ar.

15 Ka tafi wurinsa da safe daidai lokacin da ya fita zai tafi Kogin Nilu. Ka jira don ka sadu da shi a bakin Nilu. Ka kuma ɗauki sandan nan wanda ya juye ya zama maciji.

16 Za ka faɗa wa Fir’auna cewa, ‘Ubangiji Allah na Ibraniyawa ya aike ni gare ka da cewa ka saki jama’ar Ubangiji domin su yi masa hidima a jeji. Amma ga shi, har yanzu ba ka yi biyayya ba.

17 Ubangiji ya ce, za ka sani shi ne Ubangiji ta wurin abin da zan aikata. Zan bugi ruwan Nilu da sandan da yake hannuna, ruwan kuwa zai rikiɗe ya zama jini.

18 Kifayen da suke cikin Nilu za su mutu. Nilu kuwa zai yi ɗoyi, har da Masarawa ba za su iya shan ruwansa ba.”’

19 Ubangiji kuma ya ce wa Musa ya faɗa wa Haruna ya ɗauki sandansa ya miƙa shi a bisa ruwayen Masar, da kogunansu, da rafuffukansu, da fadamunsu, da dukan tafkunansu don ruwansu ya zama jini. Jini zai kasance ko’ina a ƙasar Masar, i, har ma cikin randuna.

20 Musa da Haruna kuwa suka yi daidai kamar yadda Ubangiji ya umarta. Sai Haruna ya ta da sandansa sama ya bugi ruwan Nilu a gaban Fir’auna da fādawansa. Dukan ruwan Nilu kuwa ya rikiɗe jini.

21 Kifayen da suke cikin Nilu suka mutu. Nilu kuwa ya yi ɗoyi, har Masarawa ba su iya shan ruwansa ba. Ko’ina kuma a ƙasar Masar akwai jini.

22 Masu sihiri kuma na Masar suka yi haka, su ma, ta wurin sihirinsu, don haka zuciyar Fir’auna ta daɗa taurarewa, ya kuwa ƙi jin Musa da Haruna kamar yadda Ubangiji ya riga ya faɗa.

23 Sai ya juya, ya koma fādarsa, bai ko kula da abin da aka yi ba.

24 Dukan Masarawa suka tattone ramummuka a bakin Nilu, suna neman ruwan sha, gama ba su iya shan ruwan Nilu ba.

25 Kwana bakwai suka cika bayan da Ubangiji ya bugi Kogin Nilu.