Tashin Almasihu daga Matattu
1 A yanzu kuma, ‘yan’uwa, zan tuna muku da bisharar da na sanar da ku, wadda kuka karɓa, wadda kuke bi,
2 wadda kuma ake cetonku da ita, muddin kun riƙe maganar da na sanar da ku da kyau, in ba sama sama ne kuka gaskata ba.
3 Jawabi mafi muhimmanci da na sanar da ku, shi ne wanda na karɓo, cewa, Almasihu ya mutu domin zunubanmu, kamar yadda Littattafai suka faɗa,
4 cewa an binne shi, an ta da shi a rana ta uku, kamar yadda Littattafai suka faɗa,
5 ya kuma bayyana ga Kefas, sa’an nan ga sha biyun.
6 Sa’an nan ya bayyana ga ‘yan’uwa fiye da ɗari biyar a lokaci guda, yawancinsu kuwa suna nan har zuwa yanzu, amma waɗansu sun yi barci.
7 Sa’an nan ya bayyana ga Yakubu, sa’an nan ga dukan manzanni.
8 Daga ƙarshen duka ya bayyana a gare ni, ni ma da nake kasasshe, marar cancanta.
9 Don ni ne mafi ƙanƙanta a cikin manzanni, ban ma isa a ce da ni manzo ba, saboda na tsananta wa Ikkilisiyar Allah.
10 Amma saboda alherin Allah na zama yadda nake, alherin da ya yi mini kuwa ba a banza yake ba. Har ma na fi kowannensu aiki, ba kuwa ni ba, alherin Allah ne da yake zuciyata.
11 To, ko ni ne dai, ko kuma su ne, haka muke wa’azi, ta haka kuma kuka gaskata.
Tashin Matattu
12 To, da yake ana wa’azin Almasihu a kan an tashe shi daga matattu, ƙaƙa waɗansunku suke cewa, babu tashin matattu?
13 In dai babu tashin matattu, ashe, ba a ta da Almasihu ba ke nan.
14 In kuwa ba a ta da Almasihu ba, to, ashe, wa’azinmu a banza ne, bangaskiyarku kuma banza ce.
15 Sai ma ya zamana mun yi wa Allah shaidar zur ke nan, domin mun shaida Allah, cewa ya ta da Almasihu, wanda kuwa bai tasar ba, in da gaskiya ne ba a ta da matattu.
16 Don kuwa in ba a ta da matattu, ashe, Almasihu ma ba a ta da shi ba ke nan.
17 In kuwa ba a ta da Almasihu ba, ashe, bangaskiyarku banza ce, har yanzu kuma kuna tare da zunubanku.
18 Ashe, waɗanda suka yi barci a kan su na Almasihu, sun hallaka ke nan.
19 Da begenmu ga Almasihu domin wannan rai ne kaɗai, ai, da mun fi kowa zama abin tausayi.
20 Amma ga hakika an ta da Almasihu daga matattu, shi ne ma nunan fari na waɗanda suka yi barci.
21 Tun da yake mutuwa ta wurin mutum ta faru, haka kuma tashin matattu ta wurin Mutum yake.
22 Kamar yadda duk ake mutuwa saboda Adamu, haka duk za a rayar da su saboda Almasihu.
23 Amma kowanne bi da bi, Almasihu ne nunan fari, sa’an nan a ranar komowarsa, waɗanda suke na Almasihu.
24 Sa’an nan sai ƙarshen, sa’ad da zai mayar wa Allah Uba mulki, bayan ya shafe dukkan sarauta da mulki da iko.
25 Domin kuwa lalle ne ya yi mulki, har ya take dukkan maƙiyansa.
26 Magabciyar ƙarshe da za a shafe, ita ce mutuwa.
27 “Gama Allah ya sarayar da kome a ƙarƙashin ikonsa.” Amma da aka ce, “An sarayar da kome karƙashin ikonsa” a fili yake shi wannan da ya sarayar da kome a ƙarƙashin ikonsa ɗin, a keɓe yake.
28 Sa’ad da kuma aka sarayar da kome a ƙarƙashin ikonsa ɗin, sa’an nan ne Ɗan da kansa shi ma zai sarayar da kansa ga wannan da ya sarayar da kome a ƙarƙashin ikonsa, domin Allah yă tabbata shi ne kome da kome.
29 In ba haka ba, mene ne nufin waɗanda ake yi wa baftisma saboda matattu? In ba a ta da matattu sam, don me ake yi wa waɗansu baftisma saboda su?
30 Don me kuma nake a cikin hatsari a kowane lokaci?
31 Na hakikance ‘yan’uwa, saboda taƙama da ku da nake yi a cikin Almasihu Yesu Ubangijinmu, a kowace rana sai na sallama raina ga mutuwa!
32 Idan bisa ga ra’ayin mutum ne, na yi kokawa da namomin jeji a Afisa, mece ce ribata in dai har ba a ta da matattu? “Ba sai mu yi ta ci da sha ba, da yake gobe za mu mutu?”
33 Kada fa a yaudare ku! “Zama da mugaye yakan ɓata halayen kirki.”
34 Ku farka daga magagi, ku kama aikin adalci, ku daina yin zunubi. Waɗansu kam, ba su da sanin Allah. Na faɗi wannan ne don ku kunyata.
Tashin Jiki
35 Watakila wani zai yi tambaya, “Ta yaya ake ta da matattu? Da wace irin kama kuma suke fitowa?”
36 Kai, marar azanci! Abin da ka shuka, ai, ba zai tsiro ba sai ya mutu.
37 Abin da ka shuka kuma, ba shi ne ainihin abin da zai kasance ba, ƙwaya ce ƙawai, ko ta alkama ce, ko kuma, wata iri dabam.
38 Amma Allah yakan ba ta kama, yadda ya nufa, kowace ƙwaya da irin tata kama.
39 Don ba dukan tsoka ce iri ɗaya ba, mutane da irin tasu, dabbobi ma da irin tasu, tsuntsaye da irin tasu, kifaye kuma da irin tasu.
40 Akwai halitta irin ta Sama, akwai kuma irin ta ƙasa. Amma ɗaukakar irin ta Sama dabam, ɗaukakar irin ta ƙasa kuma dabam.
41 Ɗaukakar rana dabam, ta wata dabam, ta taurari kuma dabam. Wani tauraro kuwa yakan bambanta da wani a wajen ɗaukaka.
42 Haka kuma yake ga tashin matattu. Akan shuka su da halin ruɓa, akan kuma ta da su da halin rashin ruɓa.
43 Akan shuka da wulakanci, akan tasa da ɗaukaka, akan shuka da rashin ƙarfi, akan tasa da ƙarfi.
44 Akan shuka da jikin mutuntaka, akan tasa da jiki na ruhu. Da yake akwai jiki na mutuntaka, lalle kuma akwai jiki na ruhu.
45 Haka kuma yake a rubuce, “Mutumin farko, Adamu, ya zama rayayyen taliki,” Adamun ƙarshe kuwa Ruhu ne mai rayarwa.
46 Amma ba shi na Ruhun nan ne ya fara bayyana ba, na mutuntaka ne, daga baya kuma sai na Ruhu.
47 Mutumin farko daga ƙasa yake, na turɓaya ne. Na biyun kuwa daga Sama yake.
48 Kamar yadda shi na turɓayar nan yake, haka kuma waɗanda suke na turɓaya suke. Kamar yadda shi na Saman nan yake, haka kuma waɗanda suke na Sama suke.
49 Kamar yadda muka ɗauki siffar na turɓayar nan, haka kuma za mu ɗauki siffar na Saman nan.
50 Ina dai gaya muku wannan ‘yan’uwa, ba shi yiwuwa jiki mai tsoka da jini ya sami gādo a Mulkin Allah, haka kuma mai ruɓa ba ya gādon marar ruɓa.
51 Ga shi, zan sanar da ku wani asiri! Ba dukanmu ne za mu yi barci ba, amma dukanmu za a sauya kamanninmu,
52 farat ɗaya da ƙyiftawar ido, da jin busar ƙaho na ƙarshe, domin za a busa ƙaho, za a kuma ta da matattu da halin rashin ruɓa, za a kuma sauya kamanninmu.
53 Domin lalle ne, marar ruɓa ya maye mai ruɓar nan, marar mutuwa kuma ya maye mai mutuwar nan.
54 Sa’ad da kuma marar ruɓa ya maye mai ruɓar nan, marar mutuwa kuma ya maye mai mutuwar nan, a sa’an nan ne fa maganar nan da take a rubuce za a cika ta, cewa,
“An shafe mutuwa da aka ci nasararta.”
55 “Ke mutuwa, ina nasararki?
Ke mutuwa, ina ƙarinki?”
56 Ai, zunubi shi ne ƙarin mutuwa, Shari’a kuwa ita ce sanadin ƙarfin zunubi.
57 Godiya tā tabbata ga Allah wanda yake ba mu nasara ta wurin Ubangijinmu Yesu Almasihu.
58 Don haka, ya ‘yan’uwana, ƙaunatattu, ku tsaya a kafe, kullum kuna himmantuwa ga aikin Ubangiji, domin kuwa kun san famar da kuke yi saboda Ubangiji ba a banza take ba.