FAR 50

1 Yusufu kuwa ya fāɗa a kan mahaifinsa, ya yi kuka a kansa, ya sumbace shi.

2 Sai Yusufu ya umarci barorinsa masu magani, su shafe gawar mahaifinsa da maganin hana ruɓa. Saboda haka masu maganin suka shafe Isra’ila da maganin hana ruɓa.

3 Suka ɗauki kwana arba’in cif suna yin wannan, gama kwanakin da ake bukata ke nan don shafewa da maganin hana ruɓa. Masarawa kuwa suka yi masa makoki na kwana saba’in.

4 Sa’ad da kwanakin makokin suka wuce, Yusufu ya yi magana da iyalin gidan Fir’auna, ya ce, “Idan fa yanzu na sami tagomashi a wurinku, ku yi magana, ina roƙonku a gaban Fir’auna, ku ce masa,

5 ‘Sa’ad da mahaifina yake bakin mutuwa, ya sa ni in yi masa alkawari, cewa zan binne shi a kabarin da ya haƙa wa kansa a ƙasar Kan’ana.’ Don haka in ya yarda ya bar ni in je in binne mahaifina, sa’an nan in komo.”

6 Fir’auna ya amsa, ya ce, “Ka haura ka binne mahaifinka, kamar yadda ya rantsar da kai.”

7 Saboda haka, Yusufu ya haura ya binne mahaifinsa, tare da shi kuma dukan barorin Fir’auna suka haura, da dattawan gidan Fir’auna, da dukan dattawan ƙasar Masar,

8 da kuma dukan iyalin gidan Yusufu, da ‘yan’uwansa, da iyalin gidan mahaifinsa. Sai ‘yan ƙananansu, da garkunan awaki da na tumaki, da garkunan shanunsu, aka bari a ƙasar Goshen.

9 Da karusai da mahayan dawakai kuma suka tafi tare da shi. Babbar ƙungiya ce ƙwarai.

10 Sa’ad da suka kai farfajiyar masussukar Atad, wanda yake wajen Urdun, a nan ne fa suka yi makoki, da babban makoki da baƙin ciki mai zafi. Aka kuwa yi kwana bakwai ana makokin mahaifinsa.

11 Sa’ad da Ka’aniyawa mazaunan ƙasar, suka ga makokin da aka yi a farfajiyar masussukar Atad, sai suka ce, “Wannan makoki mai zafi ne ga Masarawa.” Don haka aka sa wa wurin suna Abel-mizrayim, wanda yake wajen Urdun.

12 Haka ‘ya’yansa suka yi masa kamar yadda ya umarta,

13 gama ‘ya’yansa suka ɗauke shi zuwa ƙasar Kan’ana, suka kuwa binne shi a kogon da yake saurar Makfela a gabashin Mamre, wanda Ibrahim ya saya, duk da saurar, daga wurin Efron Bahitte, ya zama mallakarsa don makabarta.

14 Bayan da Yusufu ya binne mahaifinsa, ya koma Masar tare da ‘yan’uwansa da dukan waɗanda suka tafi tare da shi don jana’izar mahaifinsa.

Yusufu ya Tabbatar wa ‘Yan’uwansa ba zai Rama Ba

15 Sa’ad da ‘yan’uwan Yusufu suka ga mahaifinsu ya rasu, suka ce, “Mai yiwuwa ne Yusufu zai ƙi jininmu, ya sāka mana dukan muguntar da muka yi masa.”

16 Saboda haka suka aika wa Yusufu da jawabi, suka ce, “Mahaifinka ya ba da wannan umarni kafin rasuwarsa,

17 ya ce, ‘Ku faɗa wa Yusufu, ina roƙonsa, ya gafarta laifin ‘yan’uwansa da zunubansu, gama sun yi masa mugunta.’ Yanzu fa, muna roƙonka, ka gafarta laifofin bayin Allah na mahaifinka.” Yusufu ya yi kuka sa’ad da suka yi magana da shi.

18 ‘Yan’uwansa kuma suka zo suka fāɗi a gabansa, suka ce, “Ga shi, mu barorinka ne.”

19 Amma Yusufu ya ce musu, “Kada ku ji tsoro, ni ba a matsayin Allah nake ba.

20 A nufinku mugunta ce kuka yi mini, amma Allah ya maishe ta alheri, don a rayar da jama’a masu yawa waɗanda suke da rai a yau.

21 Don haka kada ku ji tsoro, zan tanada muku, ku da ƙanananku.” Ta haka ya ta’azantar da su, ya yi musu magana ta kwantar da zuciya.

Rasuwar Yusufu

22 Haka fa Yusufu ya zauna a Masar, shi da iyalin gidan mahaifinsa. Yusufu kuwa ya yi shekara ɗari da goma a duniya.

23 Yusufu fa ya ga ‘ya’yan Ifraimu har tsara ta uku, aka kuma haifi ‘ya’yan Makir ɗan Manassa, aka karɓe su cikin iyalin Yusufu.

24 Yusufu kuwa ya ce wa ‘yan’uwansa, “Ina gab da mutuwa, amma lalle Allah zai ziyarce ku, zai kuwa haurar da ku daga wannan ƙasa zuwa ƙasar da ya rantse wa Ibrahim, da Ishaku, da Yakubu.”

25 Sa’an nan Yusufu ya rantse wa ‘ya’yan Isra’ila da cewa, “Hakika Allah zai ziyarce ku, ku kuma sai ku haura da ƙasusuwana daga nan.”

26 Yusufu ya rasu yana da shekara ɗari da goma. Sai suka shafe shi da maganin hana ruɓa. Aka kuwa sa shi a akwatin gawa cikin Masar.