FAR 48

Yakubu Ya Sa wa Ifraimu da Manassa Albarka

1 Ya zama fa bayan waɗannan al’amura, aka faɗa wa Yusufu, “Ga mahaifinka yana ciwo.” Sai ya ɗauki ‘ya’yansa biyu maza, Manassa da Ifraimu ya tafi ya gai da mahaifinsa.

2 Sa’ad da aka ce wa Yakubu, “Ɗanka Yusufu ya zo wurinka,” sai Yakubu ya ƙoƙarta ya tashi zaune a kan gadon.

3 Yakubu ya ce wa Yusufu, “Allah Maɗaukaki ya bayyana gare ni a Luz a ƙasar Kan’ana ya sa mini albarka,

4 ya ce mini, ‘Ga shi, zan sa ka hayayyafa, in riɓaɓɓanya ka, zan maishe ka ƙungiyar al’ummai, zan kuwa ba da wannan ƙasa ga zuriyarka a bayanka ta zama madawwamiyar mallaka.’

5 Yanzu fa, a kan waɗannan ‘ya’yanka maza biyu da aka haifa a Masar kafin zuwana, su nawa ne, Ifraimu da Manassa za su zama nawa, kamar yadda su Ra’ubainu da Saminu suke.

6 ‘Ya’ya waɗanda za a haifa a bayansu za su zama naka, za a kira su da sunan ‘yan’uwansu cikin gādonsu.

7 Sa’ad da nake zuwa daga Mesofotamiya, sai Rahila ta rasu a hannuna a ƙasar Kan’ana a kan hanya, ga shi kuwa, da sauran tazara kafin a kai Efrata. Na kuwa binne ta a Efrata,” wato Baitalami.

8 Sa’ad da Isra’ila ya ga ‘ya’yan Yusufu, maza, ya ce, “Su wane ne waɗannan?”

9 Sai Yusufu ya ce wa mahaifinsa, “’Ya’yana ne maza waɗanda Allah ya ba ni a nan.”

Sai ya ce, “Kawo su gare ni, ina roƙonka, domin in sa musu albarka.”

10 Yanzu fa, idanun Isra’ila sun dushe saboda yawan shekaru, har ba ya iya gani. Sai Yusufu ya kawo su kusa da shi, ya sumbace su ya rungume su.

11 Isra’ila ya ce wa Yusufu, “Ban yi zaton zan ga fuskarka ba, ga shi kuwa, Allah ya sa na gani har da na ‘ya’yanka.”

12 Yusufu ya kawar da su daga gwiwoyin Isra’ila, ya sunkuyar da fuskarsa har ƙasa a gabansa.

13 Yusufu ya ɗauki su biyu ɗin, Ifraimu a hannunsa na dama zuwa hannun hagun Isra’ila, Manassa kuma a hannunsa na hagu zuwa dama na Isra’ila, ya kawo su kusa da shi.

14 Isra’ila ya miƙa hannunsa na dama, ya ɗora bisa kan Ifraimu wanda yake ƙarami, hannunsa na hagu kuma bisa kan Manassa, yana harɗe da hannuwansa, gama Manassa shi ne ɗan fari.

15 Sai ya sa wa Yusufu albarka, ya ce,

“Allah na Ibrahim da Ishaku,

Iyayena da suka yi tafiyarsu a

gabansa,

Allah da ya bi da ni

Dukan raina har wa yau, ya sa musu

albarka.

16 Mala’ikan da ya fanshe ni

Daga dukan mugunta,

Ya sa wa samarin albarka,

Bari a dinga ambatarsu da sunana,

Da sunan Ibrahim da na Ishaku iyayena,

Bari kuma su riɓaɓɓanya, su zama

taron jama’a a tsakiyar duniya.”

17 Sa’ad da Yusufu ya ga mahaifinsa ya ɗora hannun damansa a bisa kan Ifraimu, ransa bai so ba, ya ɗauke hannun mahaifinsa, domin ya kawar da shi daga kan Ifraimu zuwa kan Manassa.

18 Sai Yusufu ya ce wa mahaifinsa, “Ba haka ba ne baba, gama wannan ne ɗan fari. Sa hannunka na dama a bisa kansa.”

19 Amma mahaifinsa ya ƙi, ya ce, “Na sani, ɗana, na sani, shi ma zai zama al’umma, zai ƙasaita, duk da haka ƙanensa zai fi shi ƙasaita, zuriyarsa kuwa za ta zama taron al’ummai.”

20 Ya sa musu albarka a wannan rana, yana cewa,

“Ta gare ku Isra’ila za su sa albarka

da cewa,

‘Allah ya maishe ku kamar Ifraimu

da Manassa.’ ”

Da haka ya sa Ifraimu gaba da Manassa.

21 Isra’ila ya ce wa Yusufu, “Ga shi, ina bakin mutuwa, amma Allah zai kasance tare da kai, zai kuma sāke komar da kai ƙasar kakanninka.

22 Ni ne nake ba ka Shekem, kashi ɗaya fiye da ‘yan’uwanka, wanda na ƙwace da takobina da bakana daga hannun Amoriyawa.”