1 Yakubu ya zauna a ƙasar Kan’ana inda mahaifinsa ya yi baƙunci.
2 Wannan shi ne tarihin zuriyar Yakubu.
Yusufu da ‘Yan’uwansa
Yusufu yana da shekara goma sha bakwai sa’ad da ya zama makiyayin garke tare da ‘yan’uwansa, ɗan ƙanƙanen yaro ne a tsakanin ‘ya’ya maza na Bilha da Zilfa matan mahaifinsa. Sai Yusufu ya kawo labarin munanan abubuwa da ‘yan’uwansa suke yi a wurin mahaifinsa,
3 Isra’ila kuwa ya fi ƙaunar Yusufu da kowannensu, domin shi ɗan tsufansa ne. Sai ya yi masa riga mai ado.
4 Amma sa’ad da ‘yan’uwansa suka gane mahaifinsu yana ƙaunarsa fiye da dukansu, suka ƙi jininsa, ba su iya maganar alheri da shi.
5 Yusufu ya yi mafarki. Sa’ad da ya faɗa wa ‘yan’uwansa, suka ƙara ƙin jininsa.
6 Ya ce musu, “Ku ji irin mafarkin da na yi.
7 Ga shi, muna ɗaurin dammuna cikin gona, ga kuwa damina ya tashi tsaye kyam, ga kuma dammunanku suka taru kewaye da shi, suka sunkuya wa damina.”
8 ‘Yan’uwansa suka ce masa, “Ashe, lalle ne kai za ka sarauce mu? Ko kuwa, ashe lalle ne kai za ka mallake mu?” Sai suka daɗa ƙin jininsa domin mafarkansa da maganganunsa.
9 Shi kuwa sai ya sāke yin wani mafarki, ya faɗa wa ‘yan’uwansa, ya ce, “Ga shi kuma na sāke yin wani mafarki, na ga rana, da wata, da taurari goma sha ɗaya suna sunkuya mini.”
10 Amma sa’ad da ya faɗa wa mahaifinsa da ‘yan’uwansa, sai mahaifinsa ya tsauta masa, ya ce, “Wane irin mafarki ne wannan da ka yi? Lalle ne, da ni da mahaifiyarka da ‘yan’uwanka za mu sunkuya a gabanka har ƙasa?”
11 ‘Yan’uwansa suka ji kishinsa, amma mahaifinsa ya riƙe al’amarin cikin zuciyarsa.
An Sayar da Yusufu zuwa Masar
12 Wata rana, da ‘yan’uwansa suka tafi kiwon garken mahaifinsu a Shekem,
13 Isra’ila ya ce wa Yusufu, “Ashe, ba ‘yan’uwanka suna kiwon garken a Shekem ba? Zo in aike ka wurinsu.”
Sai ya ce masa, “Ga ni.”
14 Mahaifinsa ya ce, “Tafi yanzu, ka dubo lafiyar ‘yan’uwanka da ta garken, ka kawo mini labarinsu.” Saboda haka, ya aike shi daga kwarin Hebron.
Da Yusufu ya isa Shekem,
15 wani mutum ya same shi yana hange-hange cikin karkara. Sai mutumin ya tambaye shi ya ce, “Me kake nema?”
16 Yusufu ya ce, “Ina neman ‘yan’uwana ne. Ina roƙonka ka faɗa mini idan ka san inda suke kiwon garkuna.”
17 Mutumin ya ce, “Sun riga sun tashi daga nan, gama na ji sun ce, ‘Bari mu tafi Dotan.’ ” Saboda haka, Yusufu ya bi sawun ‘yan’uwansa, ya kuwa same su a Dotan.
18 Da suka hango shi daga nesa, kafin ya zo kusa da su, sai suka ƙulla su kashe shi.
19 Suka ce wa juna, “Ga mai mafarkin nan can yana zuwa.
20 Ku zo mu kashe shi yanzu, mu jefa shi cikin ɗaya daga cikin rijiyoyin nan, sa’an nan mu ce, wata muguwar dabbar jeji ce ta kashe shi, sa’an nan mu ga yadda mafarkinsa zai zama.”
21 Amma sa’ad da Ra’ubainu ya ji, ya yi ƙoƙari ya cece shi daga hannunsu, yana cewa, “Kada mu raba shi da ransa.
22 Kada mu kashe shi, mu dai jefa shi cikin rijiyan nan a jeji, amma kada mu yi masa lahani.” Ya yi haka da nufin ya cece shi daga hannunsu, ya mayar da shi ga mahaifinsu.
23 Don haka, sa’ad da Yusufu ya zo wurin ‘yan’uwansa, suka tuɓe masa rigarsa, rigan nan mai ado wadda take wuyansa.
24 Suka ɗauke shi suka jefa shi cikin rijiyar. Rijiyar kuwa wofi ce, ba ruwa a ciki.
25 Suka zauna su ci abinci, da suka ɗaga ido suka duba, sai ga ayarin Isma’ilawa suna zuwa daga Gileyad, da raƙumansu ɗauke da ƙāro, da man ƙanshi na wartsakewa, da mur, suna gangarawa kan hanyarsu zuwa Masar.
26 Yahuza ya ce wa ‘yan’uwansa, “Wace riba ke nan, in mun kashe ɗan’uwanmu, muka ɓoye jininsa?
27 Ku zo mu sayar da shi ga Isma’ilawa, kada mu bar hannunmu ya taɓa shi, gama shi ɗan’uwanmu ne, shi kuma jikinmu ne.” ‘Yan’uwansa suka yarda da shi.
28 Da Madayanawa, fatake, suna wucewa, sai suka jawo Yusufu suka fitar da shi daga cikin rijiyar suka sayar wa Isma’ilawa a bakin azurfa ashirin, aka kuwa tafi da Yusufu zuwa Masar.
29 Sa’ad da Ra’ubainu ya koma a wajen rijiya, da bai ga Yusufu a cikin rijiyar ba, sai ya kyakkece tufafinsa,
30 ya koma wurin ‘yan’uwansa, ya ce, “Saurayin ba ya nan, ni kuwa, ina zan sa kaina?”
31 Suka ɗauki rigar Yusufu, suka yanka akuya, suka tsoma rigar cikin jinin.
32 Suka kuma ɗauki rigan nan mai ado, suka kawo ta ga mahaifinsu, suka ce, “Ga abar da muka samu, duba ka gani, ta ɗanka ce, ko kuwa?”
33 Da ya gane ita ce, ya ce, “Rigar ɗana ce, wani mugun naman jeji ne ya cinye shi, ba shakka an yayyage Yusufu.”
34 Sai Yakubu ya kyakkece rigunansa, ya yi ɗamara da majayi, ya yi kukan ɗansa har kwanaki masu yawa.
35 Dukan ‘ya’yansa mata da maza suka tashi domin su ta’azantar da shi, amma ya ƙi ta’azantuwa, yana cewa, “A’a, a Lahira zan tafi wurin ɗana, ina baƙin ciki.” Haka mahaifinsu ya yi kuka dominsa.
36 A lokacin kuwa, ashe, Madayanawa sun riga sun sayar da shi a Masar ga Fotifar, sarkin yaƙin Fir’auna, shugaba na masu tsaron fādar Fir’auna.