FAR 33

Yakubu ya Sadu da Isuwa

1 Yakubu ya ɗaga ido ya duba ke nan, sai ga Isuwa na zuwa da mutum arbaminya tare da shi. Sai ya raba wa Lai’atu da Rahila ‘ya’yan, tare da kuyangin nan biyu.

2 Ya sa kuyangin da ‘ya’yansu a gaba, sa’an nan Lai’atu sa’an nan Rahila da Yusufu a ƙarshen duka.

3 Shi kansa ya wuce gabansu, ya yi ta sunkuyar da kansa ƙasa sau bakwai, har sa’ad da ya kai kusa da ɗan’uwansa.

4 Amma Isuwa ya sheƙa ya tarye shi, ya rungume shi, ya faɗa a wuyansa, ya sumbace shi, suka kuwa yi kuka.

5 Sa’ad da Isuwa ya ta da idonsa ya ga mata da ‘ya’ya, ya ce, “Su wane ne waɗannan tare da kai?”

Yakubu ya ce, “Su ne ‘ya’ya waɗanda Allah cikin alherinsa ya ba baranka.”

6 Sai kuyangin suka matso kusa, su da ‘ya’yansu, suka sunkuya ƙasa.

7 Haka nan kuma Lai’atu da ‘ya’yanta suka matso, suka sunkuya ƙasa, a ƙarewa Yusufu da Rahila suka matso kusa, su kuma suka sunkuya ƙasa.

8 Isuwa kuwa ya ce, “Ina manufarka da duk waɗannan ƙungiyoyi da na gamu da su?”

Yakubu ya amsa, ya ce, “Ina neman tagomashi ne a idon shugabana.”

9 Amma Isuwa ya ce, “Ina da abin da ya ishe ni, ɗan’uwana, riƙe abin da kake da shi don kanka.”

10 Yakubu ya ce, “A’a, ina roƙonka, in dai na sami tagomashi a idonka, to, sai ka karɓi kyautar da yake hannuna, gama hakika ganin fuskarka, kamar ganin fuskar Allah ne, bisa ga yadda ka karɓe ni.

11 Ina roƙonka, ka karɓi kyautar da na kawo maka, gama Allah ya yi mini alheri matuƙa, gama ina da abin da ya ishe ni.” Da haka Yakubu ya i masa, Isuwa kuwa ya karɓa.

12 Sa’an nan Isuwa ya ce, “Bari mu ci gaba da tafiyarmu, ni kuwa in wuce gabanka.”

13 Amma Yakubu ya ce masa, “Shugabana, ai, ka sani ‘ya’yan ba su da ƙarfi, ga kuma bisashe da shanun tatsa, ina jin tausayinsu ƙwarai da gaske. Idan kuwa aka tsananta korarsu kwana ɗaya, garkunan za su mutu duka.

14 Bari shugabana ya wuce gaban baransa, ni zan biyo a hankali bisa ga saurin shanun da yake gabana, da kuma bisa ga saurin yaran, har in isa wurin shugaba a Seyir.”

15 Sai Isuwa ya ce, “Bari in bar waɗansu daga cikin mutanen da suke tare da ni, a wurinka.”

Amma Yakubu ya ce, “Ka kyauta ƙwarai, amma ba na bukatar haka, ya shugaba.”

16 A ran nan Isuwa ya koma a kan hanyarsa zuwa Seyir.

17 Yakubu ya kama hanya zuwa Sukkot, ya kuwa gina wa kansa gida, ya yi wa shanunsa garke. Saboda haka aka sa wa wurin suna Sukkot.

18 Yakubu kuwa ya kai birnin Shalem wanda yake ƙasar Kan’ana lafiya, a kan hanyarsa daga Fadan-aram, ya kuwa yi zango a ƙofar birnin.

19 Ya kuma sayi yankin saura inda ya kafa alfarwarsa daga ‘ya’yan Hamor, mahaifin Shekem, a bakin azurfa ɗari.

20 A wurin ya gina bagade ya sa masa suna El-Elohe-Isra-el.