Aka Auro wa Ishaku Mata
1 Yanzu Ibrahim ya tsufa, ya kuwa kwana biyu. Ubangiji kuma ya sa wa Ibrahim albarka a cikin abu duka.
2 Ibrahim ya ce wa baransa, daɗaɗɗen gidansa wanda yake hukunta dukan abin da yake da shi, “Sa hannunka a ƙarƙashin cinyata,
3 ka rantse da Ubangiji na sama da duniya, cewa ba za ka auro wa ɗana mata daga ‘yan matan Kan’aniyawa waɗanda nake zaune a tsakaninsu ba.
4 Amma za ka tafi ƙasata, daga cikin dangina ka auro wa ɗana Ishaku mata.”
5 Sai baransa ya ce masa, “Watakila matar ba za ta yarda ta biyo ni zuwa wannan ƙasa ba, tilas ke nan, in koma da ɗanka ƙasar da ka fito?”
6 Ibrahim ya ce masa, “Ka kiyaye wannan fa, kada ka kuskura ka koma da ɗana can.
7 Ubangiji Allah na Sama wanda ya ɗauke ni daga gidan mahaifina daga ƙasar haihuwata, wanda ya yi magana da ni ya kuma rantse mini, ‘Ga zuriyarka zan ba da wannan ƙasa,’ shi zai aiki mala’ikansa a gabanka. Za ka kuwa auro wa ɗana mata daga can.
8 Amma idan matar ba ta yarda ta biyo ka ba, ka kuɓuta daga rantsuwan nan tawa. Kai dai kada ka koma da ɗana can.”
9 Sai baran ya sa hannunsa a ƙarƙashin cinyar Ibrahim maigidansa, ya kuwa rantse masa zai yi.
10 Baran ya ɗibi raƙuma goma daga cikin raƙuman maigidansa. Ya tashi, yana ɗauke da tsaraba ta kowane irin abu mai kyau na maigidansa a hannunsa. Ya kama hanyar Mesofotamiya zuwa birnin Nahor.
11 Ya durƙusar da raƙumansa a bayan birnin, kusa da bakin rijiyar ruwa da maraice, wato lokacin da mata sukan tafi ɗebo ruwa.
12 Sai ya ce, “Ya Ubangiji Allah na maigidana Ibrahim.
13 Ga shi kuwa, ina tsaye a bakin rijiyar ruwa, ga kuma ‘yan matan mutanen birnin suna fitowa garin ɗibar ruwa.
14 Bari budurwar da zan ce wa, ‘Ina roƙo, ki sauke tulunki domin in sha,’ wadda za ta ce, ‘Sha, zan kuma shayar da raƙumanka,’ bari ta zama ita ce wadda ka zaɓa wa baranka Ishaku. Ta haka zan sani ka nuna madawwamiyar ƙaunarka ga maigidana.”
15 Kafin ya rufe baki, sai ga Rifkatu wadda aka haifa wa Betuwel ɗan Milka, matar Nahor ɗan’uwan Ibrahim, ta fito da tulun ruwanta a bisa kafaɗarta.
16 Budurwa mai kyan tsari ce. Tana da kyan gani ƙwarai, budurwa ce, ba wanda ya taɓa saninta. Ta gangara zuwa rijiyar ta cika tulunta, ta hauro.
17 Sai baran ya tarye ta a guje, ya ce, “Roƙo nake, ki ba ni ruwa kaɗan daga cikin tulunki in sha.”
18 Ta ce, “Sha, ya shugabana.” Nan da nan ta sauke tulunta ta riƙe a hannunta, ta ba shi ya sha.
19 Sa’ad da ta gama shayar da shi, ta ce, “Zan ɗebo wa raƙumanka kuma, har su gama sha.”
20 Sai nan da nan ta bulbule tulunta a cikin kwami, ta sāke sheƙawa a guje zuwa rijiyar, ta kuwa ɗebo wa raƙumansa duka.
21 Mutumin kuwa ya zura mata ido, shiru, yana so ya sani ko Allah ya arzuta tafiyarsa, ko kuwa babu?
22 Sa’ad da raƙuman suka gama sha, mutumin ya ɗauki zoben zinariya mai nauyin rabin shekel, ya sa mata a hanci. Ya kuma ɗauki mundaye biyu na shekel goma na zinariya ya sa a hannuwanta,
23 ya ce, “Ki faɗa mini ke ‘yar gidan wace ce? Akwai masauki a gidan mahaifinki inda za mu sauka?”
24 Sai ta ce masa, “Ni ‘yar Betuwel ce ɗan Milka wanda ta haifa wa Nahor.”
25 Ta ƙara da cewa, “Muna da isasshen baro da harawa duka, da kuma masauki.”
26 Mutumin ya yi ruku’u ya yi wa Ubangiji sujada,
27 ya ce, “Yabo ya tabbata ga Ubangiji na maigidana Ibrahim, wanda bai daina nuna madawwamiyar ƙaunarsa da amincinsa ga maigidana ba. Ubangiji ya bi da ni har zuwa gidan ɗan’uwan maigidana.”
28 Budurwar ta sheƙa a guje zuwa gida wurin mahaifiyarta ta faɗi waɗannan abubuwa.
29 Rifkatu kuwa tana da ɗan’uwa sunansa Laban. Sai Laban ya sheƙo zuwa wurin mutumin a bakin rijiya.
30 Sa’ad da ya ga zoben da mundaye da suke hannuwan ‘yar’uwarsa, sa’ad da kuma ya ji maganar Rifkatu ‘yar’uwarsa cewa, “Ga abin da mutumin ya faɗa mini,” sai ya je wurin. Ya kuwa same shi yana tsaye wajen raƙuma kusa da rijiyar.
31 Ya ce masa, “Shigo, ya mai albarka na Ubangiji, don me kake tsaye a waje? Gama na shirya gida da wuri domin raƙuma.”
32 Mutumin ya shiga gidan, Laban kuwa ya sauke raƙuman, ya ba shi baro da harawa domin raƙuma, da ruwa ya wanke ƙafafunsa da ƙafafun waɗanda suke tare da shi.
33 Aka sa abinci a gabansa domin ya ci, amma ya ce, “Ba zan ci ba, sai na faɗi abin da yake tafe da ni.”
Laban ya ce, “Faɗi maganarka.”
34 Ya ce, “Ni baran Ibrahim ne.
35 Ubangiji ya sa wa maigidana albarka ƙwarai, ya kuwa zama babba, ya ba shi garkunan tumaki da na shanu, da azurfa da zinariya, da barori mata da maza, da raƙuma da jakai.
36 Saratu ta haifa wa maigidana ɗa cikin tsufanta, a gare shi kuma ya ba da dukan abin da yake da shi.
37 Maigidana ya rantsar da ni da cewa, ‘Ba za ka auro wa ɗana mace daga cikin ‘ya’yan Kan’aniyawa waɗanda nake zaune a ƙasarsu ba,
38 amma ka tafi gidan mahaifina da dangina, ka auro wa ɗana mace.’
39 Sai na ce wa maigidana, ‘Watakila matar ba za ta biyo ni ba.’
40 Amma ya amsa mini ya ce, ‘Ubangiji wanda nake tafiya a gabansa zai aiki mala’ikansa tare da kai, ya arzuta hanyarka, za ka kuwa auro wa ɗana mace daga cikin dangina daga gidan mahaifina.
41 Sa’an nan za ka kuɓuta daga rantsuwata. Sa’ad da ka zo wurin dangina, idan kuwa ba su ba ka ita ba, za ka kuɓuta daga rantsuwata.’
42 “Yau kuwa da na iso bakin rijiyar, sai na ce a raina, ‘Ya Ubangiji, Allah na shugabana Ibrahim, in nufinka ne ka arzuta tafiyata.
43 Ga ni, ina tsaye a bakin rijiyar kuwa, bari budurwar da za ta fito ɗibar ruwa, wadda in na ce mata, “Roƙo nake, ba ni ruwa kaɗan daga ruwan tulunki in sha,”
44 in ta amsa mini, “To, sha, zan ɗebo wa raƙumanka kuma,” bari ta zama ita ce wadda Ubangiji ya zaɓar wa ɗan maigidana.’
45 Kafin in gama tunani a zuciyata, sai ga Rifkatu ta fito ɗauke da tulun ruwa a kafaɗarta, ta gangara zuwa rijiya ta ɗebo. Na ce mata, ‘Roƙo nake, ki ba ni, in sha.’
46 Nan da nan ta sauke tulunta daga kafaɗarta, ta ce, ‘To, sha, zan kuma shayar da raƙumanka.’ Na sha, ta kuma shayar da raƙuman.
47 Na kuwa tambaye ta, ‘’Yar gidan wane ne ke?’ Ta ce, ‘Ni ‘yar Betuwel ɗan Nahor, wanda Milka ta haifa masa.’ Sai na sa mata zobe a hanci, mundaye kuma a hannu.
48 Sa’an nan na yi ruku’u, na yi wa Ubangiji sujada, na yabi Ubangiji Allah na maigidana, Ibrahim, wanda ya bishe ni a hanya sosai, in auro wa ɗansa ‘yar danginsa.
49 Yanzu fa, idan za ku amince ku gaskata da maigidana, ku faɗa mini, in ba haka ba, sai ku faɗa mini, domin in san abin yi, in juya dama ko hagu.”
50 Laban da Betuwel suka amsa suka ce, “Wannan al’amari daga Ubangiji ne, ba mu da iko mu ce maka i, ko a’a.
51 Ga Rifkatu nan gabanka, ka ɗauke ta ku tafi, ta zama matar ɗan maigidanka, bisa ga faɗar Ubangiji.”
52 Sa’ad da baran Ibrahim ya ji wannan, ya sunkuyar da kansa ƙasa, ya yi sujada a gaban Ubangiji.
53 Sai baran ya kawo kayan ado na azurfa, da na zinariya, da tufafi, ya bai wa Rifkatu, ya kuma ba ɗan’uwanta da mahaifiyarta kayan ado masu tsada.
54 Shi da mutanen da suke tare da shi suka ci suka sha, suka kwana wurin. Da suka tashi da safe, sai ya ce, “A sallame ni, in koma wurin maigidana.”
55 Ɗan’uwanta da mahaifiyarta suka ce, “Ka bar budurwar tare da mu har ɗan lokaci, kada ya gaza kwana goma, bayan wannan ta tafi.”
56 Amma ya ce musu, “Kada ku makarar da ni, tun da yake Allah ya arzuta tafiyata, a sallame ni domin in koma wurin maigidana.”
57 Suka ce, “Za mu kira budurwar mu tambaye ta.”
58 Suka kirawo Rifkatu suka ce mata, “Za ki tafi tare da wannan mutum?”
Sai ta ce, “Zan tafi.”
59 Suka kuwa sallami Rifkatu ‘yar’uwarsu da uwar goyonta, da baran Ibrahim da mutanensa.
60 Suka sa wa Rifkatu albarka, suka ce mata,
“’Yar’uwarmu, ki zama mahaifiyar
dubbai,
Har dubbai goma,
Bari zuriyarki kuma su gāji ƙofofin
maƙiyansu!”
61 Sai Rifkatu da kuyanginta suka tashi suka hau raƙuman, suka bi mutumin. Haka nan kuwa baran ya ɗauki Rifkatu ya koma.
62 A lokacin kuwa Ishaku ya riga ya zo daga Biyer-lahai-royi yana zaune a Negeb.
63 A gabatowar maraice, sai Ishaku ya fita saura ya yi tunani, ya ɗaga idanunsa ya duba, ya ga raƙuma suna zuwa.
64 Da Rifkatu ta ɗaga idanunta, ta hangi Ishaku, sai ta sauka daga raƙumi,
65 ta ce wa baran, “Wane ne mutumin can da yake zuwa daga saura garin ya tarye mu?”
Sai baran ya ce, “Ai, maigidana ne.” Ta ɗauki mayafinta ta yi lulluɓi.
66 Sai baran ya faɗa wa Ishaku dukan abin da ya yi.
67 Ishaku kuwa ya shiga da ita cikin alfarwarsa ya ɗauki Rifkatu ta zama matarsa, ya kuwa ƙaunace ta. Ta haka Ishaku ya ta’azantu bayan rasuwar mahaifiyarsa.