Bayebaye na Ruhu
1 A yanzu kuma ‘yan’uwa, a game da baye-baye na ruhu, ba na so ku rasa sani.
2 Kun sani fa a sa’ad da kuke bin al’ummai, an juyar da ku ga bin gumakan nan marasa baki yadda aka ga dama.
3 Don haka nake sanar da ku, cewa ba mai magana ta wurin ikon Ruhun Allah sa’an nan ya ce, “Yesu la’ananne ne!” Haka kuma ba mai iya cewa, “Yesu Ubangiji ne,” sai ta wurin ikon Ruhu Mai Tsarki.
4 To, akwai baiwa iri iri, amma Ruhu ɗaya ne.
5 Akwai fanni iri iri na ibada, amma Ubangiji ɗaya ne.
6 Akwai kuma aiki iri iri, amma Allah ɗaya yake iza kowa ga yin kowannensu.
7 An yi wa kowanne baiwa da wani buɗi na Ruhu, don kyautata wa duka.
8 Wani an yi masa baiwa da koyar da hikima ta wurin Ruhu, wani kuma da koyar da sani ta wurin wannan Ruhu.
9 Wani kuwa an yi masa baiwa da bangaskiya ta wurin Ruhun nan, wani kuma baiwar warkarwa ta wurin Ruhun nan,
10 wani kuma yin mu’ujizai, wani kuma annabci, wani kuma baiwar rarrabe ruhu da aljani, wani kuma iya harshe iri iri, wani kuma fassara harsuna.
11 Dukan waɗannan Ruhu ɗaya ne da yake iza su, yake kuma rarraba wa ko wannensu yadda ya nufa.
Dukkanmu Gaɓoɓin Jiki Guda Ne
12 Wato, kamar yadda jiki yake guda, yake kuma da gaɓoɓi da yawa su gaɓoɓin kuwa ko da yake suna da yawa, jiki guda ne, to, haka ga Almasihu.
13 Dukanmu an yi mana baftisma ta wurin Ruhu guda, mu zama jiki guda, Yahudawa ko al’ummai, bayi ko ‘ya’ya, dukanmu kuwa an shayar da mu Ruhu guda.
14 Jiki ba gaba ɗaya ba ne, gaɓoɓi ne da yawa.
15 Da ƙafa za ta ce, “Da yake ni ba hannu ba ce, ai, ni ba gaɓar jiki ba ce,” faɗar haka ba za ta raba ta da zama gaɓar jikin ba.
16 Da kuma kunne zai ce, “Da yake ni ba ido ba ne, ai, ni ba gaɓar jiki ba ne,” faɗar haka ba za ta raba shi da zama gaɓar jikin ba.
17 Da dukan jiki ido ne, da me za a ji? Da dukan jiki kunne ne, da me za a sansana?
18 Amma ga shi, Allah ya shirya gaɓoɓin jiki, kowaccensu yadda ya nufa.
19 Da dukan jikin gaɓa ɗaya ne, da ina sauran jikin?
20 Amma ga shi, akwai gaɓoɓi da yawa, jiki kuwa ɗaya.
21 Ba dama ido yă ce wa hannu, “Ba ruwana da kai,” ko kuwa kai yă ce wa ƙafafu, “Ba ruwana da ku.”
22 Ba haka yake ba, sai ma gaɓoɓin da ake gani kamar raunana, su ne wajibi,
23 gaɓoɓin jiki kuma da ake gani kamar sun kasa sauran daraja, mukan fi ba su martaba. Ta haka gaɓoɓinmu marasa kyan gani, akan ƙara kyautata ganinsu.
24 Gaɓoɓinmu masu kyan gani kuwa ba sai an yi musu kome ba. Amma Allah ya harhaɗa jiki, yana ba da mafificiyar martaba ga ƙasƙantacciyar gaɓa,
25 kada rashin haɗa kai ya kasance ga jiki, sai dai gaɓoɓin su kula da juna, kula iri ɗaya.
26 Ta haka, in wata gaɓa ta ji ciwo, duk sai su ji ciwo tare, in kuwa an yabi wata, duk sai su yi farin ciki tare.
27 To, ku jikin Almasihu ne, kowannenku kuwa gaɓarsa ne.
28 A cikin ikkilisiya, Allah ya sa waɗansu su zama, na farko manzanni, na biyu annabawa, na uku masu koyarwa, sa’an nan sai masu yin mu’ujizai, sai masu baiwar warkarwa, da mataimaka, da masu tafiyar da Ikkilisiya, da kuma masu magana da harsuna iri iri.
29 Shin, duka manzanni ne? Ko duka annabawa ne? Ko duk masu koyarwa ne? Su duka masu yin mu’ujizai ne?
30 Duka ne suke da baiwar warkarwa? Duka ne suke magana da waɗansu harsuna? Ko kuwa duka ne suke fassara?
31 Sai dai ku himmantu ga neman mafafitan bayebaye.
Har ma zan nuna muku wata hanya mafificiya nesa.