Zunubin Sadumawa ya Haɓaka
1 Mala’ikun nan biyu kuwa suka isa Saduma da maraice, Lutu kuwa yana zaune a ƙofar Saduma. Sa’ad da Lutu ya gan su sai ya miƙe ya tarye su. Sai ya yi ruku’u a gabansu.
2 ya ce, “Iyayengijina, ina roƙonku ku ratse zuwa gidan baranku, ku kwana, ku wanke ƙafafunku, da sassafe kuma sai ku kama hanyarku.”
Suka ce, “A’a, a titi za mu kwana.”
3 Amma ya nace musu ƙwarai, sai suka ratse suka shiga gidansa, ya shirya musu liyafa, ya toya musu abinci marar yisti, suka ci.
4 Amma kafin su shiga barci, mutanen birnin Saduma, samari da tsofaffi, dukan mutane gaba ɗaya suka kewaye gidan.
5 Suka kira Lutu suka ce, “Ina mutanen da suka zo wurinka da daren nan? Fito mana da su waje, don mu yi luɗu da su.”
6 Lutu ya fita daga cikin gida ya rufe ƙofar a bayansa ya je wurin mutane,
7 ya ce, “Ina roƙonku ‘yan’uwana, kada ku aikata mugunta haka.
8 Ga shi, ina da ‘ya’ya mata biyu waɗanda ba su san namiji ba, bari in fito muku da su waje, ku yi yadda kuka ga dama da su, sai dai kada ku taɓa mutanen nan ko kaɗan, gama sun shiga ƙarƙashin inuwata.”
9 Amma suka ce, “Ba mu wuri!” Suka kuma ce, “Wannan mutum ya zo baƙunci ne, yanzu kuma zai zama alƙali! Yanzu za mu yi maka fiye da yadda za mu yi musu.” Sai suka tutture Lutu suka matsa kusa don su fasa ƙofar.
10 Amma baƙin suka miƙa hannunsu, suka shigar da Lutu cikin gida inda suke, suka rufe ƙofa.
11 Sai suka bugi mutanen da suke ƙofar gidan da makanta, ƙanana da manya duka, har suka gajiyar da kansu suna laluba inda ƙofa take.
Lutu ya Bar Saduma
12 Mutanen suka ce wa Lutu, “Kana da wani naka a nan? Ko surukai, ko ‘ya’ya mata da maza, ko dai kome naka da yake cikin birnin? Fito da su daga wurin,
13 gama muna gab da hallaka wurin nan, domin kukan da ake yi a kan mutanen ya yi yawa a gaban Ubangiji. Ubangiji kuwa ya aiko mu, mu hallaka birnin.”
14 Sai Lutu ya fita ya faɗa wa surukansa waɗanda za su auri ‘ya’yansa mata, “Tashi, ku fita daga wannan wuri, gama Ubangiji yana gab da hallaka birnin.” Amma sai surukansa suka aza wasa yake yi.
15 Sa’ad da safiya ta gabato, mala’ikun suka hanzarta Lutu, suna cewa, “Tashi, ka ɗauki matarka da ‘ya’yanka biyu mata da suke nan, don kada a shafe ku saboda zunubin birnin.”
16 Amma da ya yi ta ja musu rai, sai mutanen suka kama hannunsa, da na matarsa, da na ‘ya’yansa biyu mata, saboda jinƙan da Ubangiji ya yi masa, suka fitar da shi suka kai shi a bayan birnin.
17 Sa’ad da suka fitar da shi, suka ce, “Ka gudu domin ranka, kada ka waiwaya baya, ko ka tsaya ko’ina cikin kwari, gudu zuwa tuddai domin kada a hallaka ka.”
18 Sai Lutu ya ce musu, “A’a, ba haka ba ne iyayengijina,
19 ga shi, baranka ya sami tagomashi a idonka, ka kuwa nuna mini babban alheri da ka ceci raina, amma ba zan iya in kai tuddan ba, kada hatsarin ya same ni a hanya, in mutu.
20 Ga ɗan gari can ya fi kusa inda zan gudu in fake. Bari in gudu zuwa can, in tsirar da raina.”
21 Sai ya ce masa, “Na yarda da abin da ka ce, ba zan hallakar da garin da ka ambata ba.
22 Gaggauta, ka gudu zuwa can, ba zan yi kome ba sai ka isa wurin.” Domin haka aka kira sunan garin Zowar.
Halakar Saduma da Gwamrata
23 Da hantsi Lutu ya isa Zowar.
24 Sai Ubangiji ya yi ta zuba wa Saduma da Gwamrata wutar kibritu daga sama,
25 ya hallakar da waɗannan birane, da dukan kwarin, da dukan mazaunan biranen, da tsire-tsire.
26 Amma matar Lutu da take bin bayansa ta waiwaya, sai ta zama surin gishiri.
27 Da sassafe kuwa sai Ibrahim ya tafi wurin da dā ya tsaya a gaban Ubangiji,
28 ya duba wajen Saduma da Gwamrata, da wajen dukan ƙasar kwari, sai ya hangi, hayaƙi yana tashi kamar hayaƙin da yake fitowa daga matoya a bisa ƙasar.
29 Amma sa’ad da Allah ya hallaka biranen kwarin, ya tuna da Ibrahim, ya fid da Lutu daga halakar.
Asalin Mowabawa da Ammonawa
30 Lutu ya fita daga Zowar, ya zauna cikin tuddai da ‘ya’yansa biyu mata, gama yana jin tsoro ya zauna a Zowar. Ya zauna a cikin kogo da ‘ya’yansa biyu mata.
31 Sai ‘yar farin ta ce wa ƙaramar, “Mahaifinmu ya tsufa, ba wanda zai aure mu yadda aka saba yi ko’ina a duniya.
32 Zo dai, mu sa mahaifinmu ya sha ruwan inabi, sa’an nan sai mu kwana da shi, domin kada zuriyar mahaifinmu ta ƙare.”
33 Sai suka sa mahaifinsu ya sha ruwan inabi. Da daren nan kuwa ‘yar farin ta shiga ta kwana da mahaifinta, shi kuwa bai san da kwanciyarta ba balle fa tashinta.
34 Kashegari kuma, ‘yar farin ta ce wa ƙaramar, “Ga shi, daren jiya na kwana da mahaifina, bari daren yau kuma, mu sa shi ya sha ruwan inabi, ke ma sai ki shiga ki kwana da shi, domin kada zuriyar mahaifinmu ta ƙare.”
35 Saboda haka suka sa shi ya bugu da ruwan inabi a wannan dare kuma, ƙaramar ta shiga ta kwana da shi. Shi kuwa bai san da kwanciyarta ba balle fa tashinta.
36 Haka nan kuwa, ‘ya’yan Lutu biyu ɗin nan suka sami ciki daga mahaifinsu.
37 Ta farin, ta haifi ɗa namiji, ta sa masa suna Mowab. Shi ne asalin Mowabawa har yau.
38 Ƙaramar kuma ta haifi ɗa namiji, ta sa masa suna Benammi, shi ne asalin Ammonawa har yau.