Kaciya ita ce Shaidar Alkawarin
1 A lokacin da Abram yake da shekara tasa’in da tara Ubangiji ya bayyana gare shi, ya ce masa, “Ni ne Allah Mai Iko Dukka. Ka yi mini biyayya, ka zama kamili.
2 Zan yi maka alkawari, in ba ka zuriya mai yawa.”
3 Sai Abram ya yi ruku’u, Allah kuwa ya ce masa,
4 “Wannan shi ne alkawarin da zan yi maka, za ka zama uba ga al’ummai masu ɗumbun yawa.
5 Ba za a ƙara kiran sunanka Abram ba, amma sunanka zai zama Ibrahim, gama na sa ka, ka zama uba ga al’ummai masu ɗumbun yawa.
6 Zan arzuta ka ainun, daga gare ka zan yi al’ummai, daga gare ka kuma sarakuna za su fito.
7 “Zan kafa alkawarina da kai, da zuriyarka a bayanka cikin dukan tsararrakinsu, madawwamin alkawari ke nan, in zama Allahnka da na zuriyarka a bayanka.
8 Zan ba ka, kai da zuriyarka a bayanka, ƙasar baƙuncinka, wato dukan ƙasar Kan’ana ta zama mallakarka har abada, ni kuwa zan zama Allahnsu.”
9 Allah kuma ya ce wa Ibrahim, “Kai fa, sai ka kiyaye alkawarina, da kai da zuriyarka a bayanka cikin dukan tsararrakinsu.
10 Wannan shi ne alkawarina da za ka kiyaye, da kai da zuriyarka a bayanka. Sai a yi wa kowane ɗa namiji kaciya.
11 Loɓarku za ku yanke, don alamar alkawari a tsakanina da ku.
12 Daga yanzu duk namijin da aka haifa a cikinku za a yi masa kaciya a rana ta takwas har dukan tsararrakinku, ko haifaffen gida ne, ko sayayye da kuɗi daga kowane baƙo wanda ba na zuriyarku ba.
13 Duka biyu, da wanda aka haifa daga gidanka, da wanda ka saya da kuɗi, za a yi musu kaciya. Da haka alkawarina zai kasance cikin jikinku, madawwamin alkawari ke nan.
14 Kowane ɗa namiji da bai yi kaciya ba, wato wanda bai yi kaciyar loɓarsa ba, za a fitar da shi daga jama’arsa, don ya ta da alkawarina.”
15 Allah ya ce wa Ibrahim, “Ga zancen matarka Saraya, ba za ka kira sunanta Saraya ba, amma Saratu ne sunanta.
16 Zan sa mata albarka, banda haka kuma zan ba ka ɗa ta wurinta, zan sa mata albarka, za ta kuwa zama mahaifiyar al’ummai, sarakunan jama’a za su fito daga gare ta.”
17 Sai Ibrahim ya yi ruku’u, ya yi dariya a zuciyarsa, ya ce wa kansa, “Za a haifa wa mai shekara ɗari ɗa? Zai yiwu Saratu mai shekara tasa’in ta haifi ɗa?”
18 Sai Ibrahim ya ce wa Allah, “Da ma dai a bar Isma’ilu kawai ya rayu a gabanka.”
19 Allah ya ce, “A’a, matarka Saratu ita ce za ta haifa maka ɗa, za ka raɗa masa suna Ishaku. A gare shi zan tsai da alkawarina madawwami, da kuma ga zuriyarsa a bayansa.
20 Ga zancen Isma’ilu kuwa, na ji, ga shi, zan sa masa albarka in kuma riɓaɓɓanya shi ainun. Zai zama mahaifin ‘ya’yan sarakuna goma sha biyu, zan maishe shi al’umma mai girma.
21 Amma ga Ishaku ne zan tsai da alkawarina, wato wanda Saratu za ta haifa maka a baɗi war haka.”
22 Sa’ad da Allah ya gama magana da Ibrahim, sai ya tafi ya bar Ibrahim.
23 Ibrahim kuwa ya ɗauki Isma’ilu ɗansa, da dukan bayi, haifaffun gidansa, da waɗanda aka sayo su da kuɗinsa, ya kuwa yi wa kowane namiji na jama’ar gidansa kaciyar loɓarsa a wannan rana bisa ga faɗar Allah.
24 Ibrahim na da shekara tasa’in da tara sa’ad da aka yi masa kaciyar loɓarsa.
25 Isma’ilu ɗansa yana ɗan shekara goma sha uku sa’ad da aka yi masa kaciya.
26 A wannan rana, Ibrahim da ɗansa Isma’ilu aka yi musu kaciya,
27 da mazajen gidansa duka, da waɗanda suke haifaffun gidan da waɗanda aka sayo da kuɗi daga baƙi, aka yi musu kaciya tare da shi.