Hajaratu da Isma’ilu
1 Saraya matar Abram ba ta taɓa haihuwa ba, amma tana da baranya Bamasariya, sunanta Hajaratu.
2 Sai Saraya ta ce wa Abram, “To, ga shi, Ubangiji ya hana mini haihuwar ‘ya’ya. Shiga wurin baranyata, mai yiwuwa ne in sami ‘ya’ya daga gare ta.” Abram kuwa ya saurari murya matarsa Saraya.
3 A lokacin nan kuwa Abram yana da shekara goma da zama a ƙasar Kan’ana sa’ad da Saraya matar Abram ta ɗauki Hajaratu Bamasariya, baranyarta, ta bai wa Abram mijinta ta zama matarsa.
4 Abram kuwa ya shiga wurin Hajaratu, ta kuwa yi ciki. Da ta ga ta sami ciki sai ta dubi uwargijiyarta a raine.
5 Sai Saraya ta ce wa Abram, “Bari cutar da aka cuce ni da ita ta koma kanka! Na ba da baranyata a ƙirjinka, amma da ta ga ta sami ciki, sai tana dubana a raine. Ubangiji ya shara’anta tsakanina da kai.”
6 Amma Abram ya ce wa Saraya, “Ga shi, baranyarki tana cikin ikonki, yi yadda kika ga dama da ita.” Saraya ta ƙanƙanta ta, sai Hajaratu ta gudu daga gare ta.
7 Mala’ikan Ubangiji kuwa ya sami Hajaratu a gefen wata maɓuɓɓugar ruwa a jeji, wato maɓuɓɓugar da take kan hanyar Shur.
8 Sai ya ce, “Ke Hajaratu, baranyar Saraya, ina kika fito, ina kuma za ki?”
Ta ce, “Gudu nake yi daga uwargijiyata Saraya.”
9 Mala’ikan Ubangiji ya ce mata, “Koma wurin uwargijiyarki, ki yi mata ladabi.”
10 Mala’ikan Ubangiji kuma ya ce mata, “Zan riɓaɓɓanya zuriyarki ainun har da ba za a iya lasafta su ba saboda yawansu.”
11 Mala’ikan Ubangiji kuma ya ƙara ce mata, “Ga shi, kina da ciki, za ki haifi ɗa, za ki kira sunansa Isma’ilu, domin Ubangiji ya lura da wahalarki.
12 Zai zama mutum ne mai halin jakin jeji, hannunsa zai yi gāba da kowane mutum, hannun kowane mutum kuma zai yi gāba da shi. Zai yi zaman magabtaka tsakaninsa da ‘yan’uwansa duka.”
13 Sai ta kira sunan Ubangiji wanda ya yi magana da ita, “Kai Allah ne mai gani,” gama ta ce, “Ni! Har na iya ganin Allah in rayu?”
14 Domin haka aka kira sunan rijiyar, Biyer-lahai-royi, tana nan tsakanin Kadesh da Bered.
15 Hajaratu ta haifa wa Abram ɗa, Abram kuwa ya sa wa ɗa da Hajaratu ta haifa suna, Isma’ilu.
16 Abram yana da shekara tamanin da shida sa’ad da Hajaratu ta haifa masa Isma’ilu.