Kashedi a kan Bautar Gumaka
1 To, ina so ku sani, ‘yan’uwa, dukan kakanninmu an kāre su ne a ƙarƙashin gajimare, dukansu kuma sun ratsa ta cikin bahar.
2 Dukansu kuwa an yi musu baftisma ga bin Musa a cikin gajimaren, da kuma bahar ɗin.
3 Duka kuwa sun ci abincin nan na ruhu,
4 duk kuma sun sha ruwan nan na ruhu. Domin sun sha ruwa daga Dutsen nan na ruhu, wanda ya yi tafiya tare da su. Dutsen nan kuwa Almasihu ne.
5 Duk da haka Allah bai yi murna da yawancinsu ba, har aka karkashe su a jeji.
6 To, ai, waɗannan abubuwa gargaɗi ne a gare mu, kada mu yi marmarin mugayen abubuwa, kamar yadda suka yi.
7 Kada fa ku zama matsafa kamar yadda waɗansunsu suke. A rubuce yake cewa, “Jama’a sun zauna garin ci da sha, suka kuma tashi suka yi ta rawa.”
8 Kada fa mu yi fasikanci yadda waɗansunsu suka yi, har mutum dubu ashirin da uku suka zuba a rana ɗaya tak.
9 Kada kuma mu gwada Ubangiji yadda waɗansu suka yi, har macizai suka hallaka su.
10 Kada kuma mu yi gunaguni yadda waɗansu suka yi, har mai hallakarwa ya hallaka su.
11 To, duk wannan ya same su ne a kan misali, an kuma rubuta shi ne don a gargaɗe mu, mu da ƙarshen zamani ya zo mana.
12 Don haka duk wanda yake tsammani ya kahu, ya mai da hankali kada ya fāɗi.
13 Ba wani gwajin da ya taɓa samunku, wanda ba a saba yi wa ɗan adam ba. Allah mai alkawari ne, ba zai kuwa yarda a gwada ku fin ƙarfinku ba, amma a game da gwajin sai ya ba da mafita, yadda za ku iya jure shi.
14 Saboda haka, ya ƙaunatattuna, ku guji bautar gumaka.
15 Ina magana da ku a kan ku mahankalta ne fa, ku duba da kanku ku ga abin da nake faɗa.
16 Ƙoƙon nan na yin godiya, wanda muke gode wa Allah saboda shi, ashe, ba tarayya ne ga jinin Almasihu ba? Gurasar nan da muke gutsuttsurawa kuma, ashe, ba tarayya ce ga jikin Almasihu ba?
17 Da yake gurasar nan ɗaya ce, ashe kuwa, mu da muke da yawa jiki ɗaya ne, gama mu duk gurasa ɗaya muke ci.
18 Ku dubi ɗabi’ar Isra’ila. Ashe, waɗanda suke ci daga hadayu, ba tarayya suke yi da bagadin hadaya ba?
19 Me nake nufi ke nan? Abin da aka yanka wa gumakan ne ainihin wani abu, ko kuwa gunkin ne ainihin wani abu?
20 A’a! Na nuna ne kawai cewa abin da al’ummai suke yankawa, ga aljannu suke yanka wa, ba Allah ba. Ba na fa so ku zama abokan tarayya da aljannu.
21 Ba dama ku sha a ƙoƙon Ubangiji, ku kuma sha a na aljannu. Ba dama ku ci abinci a teburin Ubangiji, ku kuma ci a na aljannu.
22 Ashe, har mā tsokani Ubangiji ya yi kishi? Mun fi shi ƙarfi ne?
Yi Kome saboda Ɗaukakar Allah
23 “Dukan abubuwa halal ne,” amma ba dukan abubuwa ne masu amfani ba. “Dukan abubuwa halal ne,” amma ba dukan abubuwa ne suke ingantawa ba.
24 Kada kowa ya nemi ya kyautata wa kansa, sai dai ya kyautata wa ɗan’uwansa.
25 Ku ci kowane irin abu da ake sayarwa a mahauta, ba tare da tambaya ba saboda lamiri.
26 Don an rubuta, “Duniya ta Ubangiji ce, da duk abin da yake cikinta.”
27 In wani a cikin marasa ba da gaskiya ya kira ku cin abinci, kuka kuwa yarda ku tafi, sai ku ci duk irin da aka sa a gabanku, ba tare da tambaya ba saboda lamiri.
28 In kuwa wani ya ce muku, “An yanka wannan saboda gunki ne fa,” to, kada ku ci, saboda duban mutuncin wannan mai gaya muku, da kuma saboda lamiri,
29 nasa lamiri fa na ce, ba naka ba. Don me fa lamirin wani zai soki ‘yancina?
30 In na yi godiya ga Allah a kan abincina, saboda me za a zarge ni a kan abin da na ci da godiya ga Allah?
31 To, duk abin da kuke yi, ko ci, ko sha, ku yi kome saboda ɗaukakar Allah.
32 Kada ku zama abin tuntuɓe ga Yahudawa ko al’ummai ko ikkilisiyar Allah,
33 kamar dai yadda nake ƙoƙarin kyautata wa dukan mutane a cikin duk abin da nake yi, ba nema wa kaina amfani nake yi ba, sai dai in amfani mutane da yawa, don su sami ceto.