Abincin da aka Miƙa wa Gumaka
1 To, yanzu a game da abubuwan da aka yanka wa gumaka, mun sani dukanmu muna da ilimi. Ilimi yakan kumbura mutum, ƙauna kuwa takan inganta shi.
2 Duk mai gani ya san wani abu, ai, har a yanzu, bai san yadda ya kamata ya sani ba.
3 In kuwa wani na ƙaunar Allah, to, Allah ya san shi.
4 A game da cin abin da aka yanka wa gumaka kuwa, mun sani, duk duniyar nan gunki yana a matsayin abin da babu ne, da kuma, babu wani Allah sai ɗaya.
5 Ko da yake, akwai waɗanda ake kira alloli a sama ko a ƙasa, don kuwa akwai “alloli” da “iyayengiji” da yawa,
6 duk da haka dai, a gare mu kam, Allah ɗaya ne, wato Uba, wanda dukkan abubuwa suke daga gare shi, wanda mu kuma zamansa muke yi, Ubangiji kuma ɗaya ta gare shi muka kasance.
7 Amma dai ba kowa ne yake da wannan sani ba. Amma waɗansu ta wurin sabawarsu da al’amuran gunki har yanzu, sukan ci naman da suka ɗauka kamar an yanka wa gunki ne. Saboda haka lamirinsu, da yake rarrauna ne, ya ƙazantu.
8 Abinci ba zai ƙare mu a game da Allah ba. In mun ci, ba mu ƙaru ba, in kuma ba mu ci ba, ba mu ragu ba.
9 Sai dai ku lura, kada ‘yancin nan naku ya zama abin sa tuntuɓe ga waɗanda ba su tsai da zuciyarsu ba.
10 Amma in wani mutum, wanda yake da rarraunan lamiri, ya gan ka, kai da kake da sani, kana ci a ɗakin gunki, ashe, wannan ba zai ƙarfafa lamirinsa har ya ci abincin da aka miƙa wa gunki ba?
11 Wato, ta sanin nan naka, sai a rushe rarraunan nan, ɗan’uwa ne kuwa wanda Almasihu ya mutu dominsa!
12 Ta haka ne kuke yi wa Almasihu laifi, wato ta wurin yi wa ‘yan’uwanku laifi, kuna rushe rarraunan lamirinsu.
13 Saboda haka in dai cin nama ya sa ɗan’uwana tuntuɓe, har abada ba zan ƙara cin nama ba, don kada in sa ɗan’uwana tuntuɓe.