Aikin Manzanni
1 Ta haka ya kamata a san mu da zama ma’aikatan Almasihu, masu riƙon amanar asirtattun al’amuran Allah.
2 Har wa yau dai, abin da ake bukata ga mai riƙon amana, a same shi amintacce.
3 A gare ni kam, sassauƙan abu ne a ce ku ne za ku gwada ni, ko kuwa a gwada ni a gaban kowace mahukunta ta mutane. Ni ma ba na gwada kaina.
4 Ban sani ina da wani laifi ba, amma ba don wannan na kuɓuta ba, ai, Ubangiji shi ne mai gwada ni.
5 Don haka, kada ku yanke wani hukunci tun lokaci bai yi ba, kafin komowar Ubangiji, wanda zai tone al’amuran da suke ɓoye a duhu, ya kuma bayyana nufin zukata. A sa’an nan ne, Allah zai yaɓa wa kowa daidai gwargwado.
6 To, ‘yan’uwa, ga zancen waɗannan abubuwa, na misalta su ne ga kaina, da kuma Afolos saboda ku, don ku yi koyi da mu, cewa, kada ku zarce abin da yake a rubuce, kada kuma waninku ya yi fahariya da wani a kan wani.
7 Wa ya fifita ka da sauran? Me kuma kake da shi, wanda ba karɓa ka yi ba? Da yake karɓa ka yi, don me kake fahariya, kamar ba karɓa ka yi ba?
8 Mhm, wato, har kun riga kun yi hamdala! Har kun wadata! Har ma kun yi sarauta ba tare da mu ba ma! Da ma a ce kun yi mulki mana, har mu ma mu yi tare da ku!
9 Don a ganina, Allah ya bayyana mu, mu manzanni, koma bayan duka ne, kamar waɗanda mutuwa yake jewa a kansu, don mun zama abin nuni ga duniya, da mala’iku duk da mutane.
10 An ɗauke mu marasa azanci saboda Almasihu, wato, ku kuwa masu azanci cikin Almasihu! Wato, mu raunana ne, ku kuwa ƙarfafa! Ku kam, ana ganinku da martaba, mu kuwa a wulakance!
11 Har a yanzu haka, yunwa muke ji, da ƙishirwa, muna huntanci, ana bugunmu, kuma yawo muke yi haka, ba mu da gida.
12 Guminmu muke ci. In an zage mu, mukan sa albarka. In an tsananta mana, mukan daure.
13 In an ci mutuncinmu, mukan ba da haƙuri. Mun zama, har a yanzu ma, mu ne kamar jujin duniya, abin ƙyamar kowa.
14 Ba don in kunyata ku na rubuta wannan ba, sai dai don in gargaɗe ku a kan cewa, ku ‘ya’yana ne, ƙaunatattu.
15 Ko da kuna da malamai masu ɗumbun yawa, amma ba ku da ubanni da yawa, don ni ne ubanku a cikin Almasihu ta wurin bishara.
16 Don haka, ina roƙon ku, ku yi koyi da ni.
17 Saboda haka, na aika muku da Timoti, wanda yake shi ne ɗana ƙaunatacce, amintacce kuma a cikin Ubangiji, zai kuwa tuna muku da ka’idodina na bin Almasihu, kamar yadda nake koyarwa a ko’ina, a kowace ikkilisiya.
18 Waɗansu har suna ɗaga kai, kamar ba zan zo wurinku ba.
19 Amma kuwa zan zo gare ku ba da daɗewa ba, in Ubangiji ya yarda, zan kuma bincika, in ga ƙarfin mutane masu ɗaga kan nan, ba maganganunsu ba.
20 Domin Mulkin Allah ba ga maganar baka yake ba, sai dai ga ƙarfi.
21 To, me kuka zaɓa, in zo muku da sanda, ko kuwa da fuskar ƙauna da lumana?